81

التكوير

At-Takwir

The Overthrowing

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ Da sunan Allah Mai rahama Mai jin kai
Ayoyi 29
Juzu'i 30
Shafi 586
Nau'i Makkiya
Tsarin Saukarwa 7
0:00 / 0:00
Aya: 1 / 29
1

إِذَا ٱلشَّمْسُ كُوِّرَتْ

idhā l-shamsu kuwwirat

Idan rãna aka shafe haskenta

2

وَإِذَا ٱلنُّجُومُ ٱنكَدَرَتْ

wa-idhā l-nujūmu inkadarat

Kuma idan taurãri suka gurɓãce (wani ya shiga a cikin wani).

3

وَإِذَا ٱلْجِبَالُ سُيِّرَتْ

wa-idhā l-jibālu suyyirat

Kuma idan duwãtsu aka tafiyar da su.

4

وَإِذَا ٱلْعِشَارُ عُطِّلَتْ

wa-idhā l-ʿishāru ʿuṭṭilat

Kuma idan rãƙuma mãsu cikunna1 aka sakẽ su wãwai, bã ga kõwa ba.

5

وَإِذَا ٱلْوُحُوشُ حُشِرَتْ

wa-idhā l-wuḥūshu ḥushirat

Kuma idan dabbõbin dãji aka tattara su.

6

وَإِذَا ٱلْبِحَارُ سُجِّرَتْ

wa-idhā l-biḥāru sujjirat

Kuma idan tẽkuna aka mayar da su wuta.

7

وَإِذَا ٱلنُّفُوسُ زُوِّجَتْ

wa-idhā l-nufūsu zuwwijat

Kuma idan rãyuka aka haɗa1 su da jikunkunansu.

8

وَإِذَا ٱلْمَوْءُۥدَةُ سُئِلَتْ

wa-idhā l-mawūdatu su-ilat

Kuma idan wadda aka turbuɗe1 ta da rai aka tambaye ta.

9

بِأَىِّ ذَنۢبٍۢ قُتِلَتْ

bi-ayyi dhanbin qutilat

"Sabõda wane laifi ne aka kashe ta?"

10

وَإِذَا ٱلصُّحُفُ نُشِرَتْ

wa-idhā l-ṣuḥufu nushirat

Idan takardun ayyuka aka wãtsa su (ga mãsu su).

11

وَإِذَا ٱلسَّمَآءُ كُشِطَتْ

wa-idhā l-samāu kushiṭat

Kuma idan sama aka fẽɗe ta.

12

وَإِذَا ٱلْجَحِيمُ سُعِّرَتْ

wa-idhā l-jaḥīmu suʿʿirat

Kuma idan Jahĩm aka hũra ta

13

وَإِذَا ٱلْجَنَّةُ أُزْلِفَتْ

wa-idhā l-janatu uz'lifat

Kuma idan Aljanna aka kusantar da ita.

14

عَلِمَتْ نَفْسٌۭ مَّآ أَحْضَرَتْ

ʿalimat nafsun mā aḥḍarat

Rai ya san abin da ya halartar (a rãnar nan).

15

فَلَآ أُقْسِمُ بِٱلْخُنَّسِ

falā uq'simu bil-khunasi

To, ba sai Na yi rantsuwa da taurãri matafã1 ba.

16

ٱلْجَوَارِ ٱلْكُنَّسِ

al-jawāri l-kunasi

Mãsu gudu suna ɓũya.

17

وَٱلَّيْلِ إِذَا عَسْعَسَ

wa-al-layli idhā ʿasʿasa

Da dare idan ya bãyar da bãya.

18

وَٱلصُّبْحِ إِذَا تَنَفَّسَ

wal-ṣub'ḥi idhā tanaffasa

Da sãfiya idan ta yi lumfashi.

19

إِنَّهُۥ لَقَوْلُ رَسُولٍۢ كَرِيمٍۢ

innahu laqawlu rasūlin karīmin

Lalle ne shi (Alƙur'ãni) haƙƙan, maganar wani manzon (Allah) ne mai girma ga Allah.

20

ذِى قُوَّةٍ عِندَ ذِى ٱلْعَرْشِ مَكِينٍۢ

dhī quwwatin ʿinda dhī l-ʿarshi makīnin

Mai ƙarfi, mai daraja a wurin Mai Al'arshi.

21

مُّطَاعٍۢ ثَمَّ أَمِينٍۢ

muṭāʿin thamma amīnin

Wanda ake yi wa ɗã'a (wato shugaban malã'iku) ne a can, amintacce.

22

وَمَا صَاحِبُكُم بِمَجْنُونٍۢ

wamā ṣāḥibukum bimajnūnin

Kuma abokinku ba mahaukaci ba ne.

23

وَلَقَدْ رَءَاهُ بِٱلْأُفُقِ ٱلْمُبِينِ

walaqad raāhu bil-ufuqi l-mubīni

Kuma lalle ne, yã gan shi1 a cikin sararin sama mabayyani.

24

وَمَا هُوَ عَلَى ٱلْغَيْبِ بِضَنِينٍۢ

wamā huwa ʿalā l-ghaybi biḍanīnin

Kuma shi, ga gaibi1 bã mai rowa ba ne.

25

وَمَا هُوَ بِقَوْلِ شَيْطَـٰنٍۢ رَّجِيمٍۢ

wamā huwa biqawli shayṭānin rajīmin

Kuma shi (Alƙur'ani) bã maganar shaiɗani, wanda aka la'ana, ba ce.

26

فَأَيْنَ تَذْهَبُونَ

fa-ayna tadhhabūna

Shin, a inã zã ku tafi?

27

إِنْ هُوَ إِلَّا ذِكْرٌۭ لِّلْعَـٰلَمِينَ

in huwa illā dhik'run lil'ʿālamīna

Lalle ne shi (Alƙur'ãni), bã kõme ba ne fãce gargaɗi ga talikai.

28

لِمَن شَآءَ مِنكُمْ أَن يَسْتَقِيمَ

liman shāa minkum an yastaqīma

Ga wanda ya so, daga cikinku, ya shiryu.

29

وَمَا تَشَآءُونَ إِلَّآ أَن يَشَآءَ ٱللَّهُ رَبُّ ٱلْعَـٰلَمِينَ

wamā tashāūna illā an yashāa l-lahu rabbu l-ʿālamīna

Kuma bã zã ku so ba sai idan Allah Ubangijin halitta Yã yarda.

Game da Wannan Sura