ق
Qaf
The Letter Qaf
قٓ ۚ وَٱلْقُرْءَانِ ٱلْمَجِيدِ
qaf wal-qur'āni l-majīdi
K. Inã rantsuwa da Alƙur'ãni Mai girma.
بَلْ عَجِبُوٓا۟ أَن جَآءَهُم مُّنذِرٌۭ مِّنْهُمْ فَقَالَ ٱلْكَـٰفِرُونَ هَـٰذَا شَىْءٌ عَجِيبٌ
bal ʿajibū an jāahum mundhirun min'hum faqāla l-kāfirūna hādhā shayon ʿajībun
Ã'a, sun yi mãmãki, cewa mai gargaɗi, daga gare su, yã zo musu, sai kãfirai suka ce: "Wannan wani abu ne mai ban mãmãki."
أَءِذَا مِتْنَا وَكُنَّا تُرَابًۭا ۖ ذَٰلِكَ رَجْعٌۢ بَعِيدٌۭ
a-idhā mit'nā wakunnā turāban dhālika rajʿun baʿīdun
"Shin idan muka mutu kuma muka kasance turɓãya (zã a kõmo da mu)? Waccan kõmowa ce mai nĩsa."
قَدْ عَلِمْنَا مَا تَنقُصُ ٱلْأَرْضُ مِنْهُمْ ۖ وَعِندَنَا كِتَـٰبٌ حَفِيظٌۢ
qad ʿalim'nā mā tanquṣu l-arḍu min'hum waʿindanā kitābun ḥafīẓun
Lalle ne Mun san abin da ƙasã ke ragẽwo daga gare su, kuma wurin Mu akwai wani littãfi mai tsarẽwa.
بَلْ كَذَّبُوا۟ بِٱلْحَقِّ لَمَّا جَآءَهُمْ فَهُمْ فِىٓ أَمْرٍۢ مَّرِيجٍ
bal kadhabū bil-ḥaqi lammā jāahum fahum fī amrin marījin
Ã'a, sun ƙaryata ne game da gaskiyar a lõkacin da ta je musu, sabõda haka sunã a cikin wani al'amari mai raurawa.
أَفَلَمْ يَنظُرُوٓا۟ إِلَى ٱلسَّمَآءِ فَوْقَهُمْ كَيْفَ بَنَيْنَـٰهَا وَزَيَّنَّـٰهَا وَمَا لَهَا مِن فُرُوجٍۢ
afalam yanẓurū ilā l-samāi fawqahum kayfa banaynāhā wazayyannāhā wamā lahā min furūjin
Shin, to, ba su yi dubi ba zuwa ga samã a bisa gare su, yadda Muka gĩna ta, kuma Muka ƙawãce ta, kuma bã ta da waɗansu tsãgogi?
وَٱلْأَرْضَ مَدَدْنَـٰهَا وَأَلْقَيْنَا فِيهَا رَوَٰسِىَ وَأَنۢبَتْنَا فِيهَا مِن كُلِّ زَوْجٍۭ بَهِيجٍۢ
wal-arḍa madadnāhā wa-alqaynā fīhā rawāsiya wa-anbatnā fīhā min kulli zawjin bahījin
Da ƙasã, Mun mĩƙe ta, kuma Mun jẽfa kafaffun duwãtsu a cikinta, kuma Mun tsirar, a cikinta daga kõwane ma'auri mai ban sha'awa?
تَبْصِرَةًۭ وَذِكْرَىٰ لِكُلِّ عَبْدٍۢ مُّنِيبٍۢ
tabṣiratan wadhik'rā likulli ʿabdin munībin
Dõmin wãyar da ido da tunãtarwa ga dukan bãwa mai tawakkali?
وَنَزَّلْنَا مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءًۭ مُّبَـٰرَكًۭا فَأَنۢبَتْنَا بِهِۦ جَنَّـٰتٍۢ وَحَبَّ ٱلْحَصِيدِ
wanazzalnā mina l-samāi māan mubārakan fa-anbatnā bihi jannātin waḥabba l-ḥaṣīdi
Kuma Mun sassakar, daga samã ruwa mai albarka sa'an nan Muka tsirar game da shi (itãcen) lambuna da ƙwãya abin girbẽwa.
وَٱلنَّخْلَ بَاسِقَـٰتٍۢ لَّهَا طَلْعٌۭ نَّضِيدٌۭ
wal-nakhla bāsiqātin lahā ṭalʿun naḍīdun
Da itãcen dabĩno dõgãye, sunã da'ya'yan itãce gunda mãsu hauhawar jũna.
رِّزْقًۭا لِّلْعِبَادِ ۖ وَأَحْيَيْنَا بِهِۦ بَلْدَةًۭ مَّيْتًۭا ۚ كَذَٰلِكَ ٱلْخُرُوجُ
riz'qan lil'ʿibādi wa-aḥyaynā bihi baldatan maytan kadhālika l-khurūju
Dõmin arziki ga bãyi, kuma Muka rãyar da ƙasa matacciya game da shi. Kamar wannan ne fitar daga kabari kake.
كَذَّبَتْ قَبْلَهُمْ قَوْمُ نُوحٍۢ وَأَصْحَـٰبُ ٱلرَّسِّ وَثَمُودُ
kadhabat qablahum qawmu nūḥin wa-aṣḥābu l-rasi wathamūdu
Mutãnen Nũhu sun ƙaryata, a gabãninsu (mutãnen yanzu) da ma'abũta Rassi, 1da Samũdãwa.
وَعَادٌۭ وَفِرْعَوْنُ وَإِخْوَٰنُ لُوطٍۢ
waʿādun wafir'ʿawnu wa-ikh'wānu lūṭin
Da Ãdãwa da Fir'auna da 'yan'uwan Lũɗu.
وَأَصْحَـٰبُ ٱلْأَيْكَةِ وَقَوْمُ تُبَّعٍۢ ۚ كُلٌّۭ كَذَّبَ ٱلرُّسُلَ فَحَقَّ وَعِيدِ
wa-aṣḥābu l-aykati waqawmu tubbaʿin kullun kadhaba l-rusula faḥaqqa waʿīdi
Da ma'abũta ƙunci 1da mutãnen Tubba'u,11 kõwanensu ya ƙaryata Manzanni, sai ƙyacẽwaTa ta tabbata.
أَفَعَيِينَا بِٱلْخَلْقِ ٱلْأَوَّلِ ۚ بَلْ هُمْ فِى لَبْسٍۢ مِّنْ خَلْقٍۢ جَدِيدٍۢ
afaʿayīnā bil-khalqi l-awali bal hum fī labsin min khalqin jadīdin
Shin, to, Mun kãsa ne game da halittar farko? Ã'a, su sunã a cikin rikici daga halitta sãbuwa.
وَلَقَدْ خَلَقْنَا ٱلْإِنسَـٰنَ وَنَعْلَمُ مَا تُوَسْوِسُ بِهِۦ نَفْسُهُۥ ۖ وَنَحْنُ أَقْرَبُ إِلَيْهِ مِنْ حَبْلِ ٱلْوَرِيدِ
walaqad khalaqnā l-insāna wanaʿlamu mā tuwaswisu bihi nafsuhu wanaḥnu aqrabu ilayhi min ḥabli l-warīdi
Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun halitta mutum kuma Mun san abin da ransa ke yin waswãsi da shi, kuma Mũ ne mafi kusanta zuwa gare shi daga lakar hannayẽnsa.
إِذْ يَتَلَقَّى ٱلْمُتَلَقِّيَانِ عَنِ ٱلْيَمِينِ وَعَنِ ٱلشِّمَالِ قَعِيدٌۭ
idh yatalaqqā l-mutalaqiyāni ʿani l-yamīni waʿani l-shimāli qaʿīdun
A lõkacin da mãsu haɗuwa biyu suke haɗuwa daga dãma, kuma daga hagu akwai wani (malã'ika) zaunanne.
مَّا يَلْفِظُ مِن قَوْلٍ إِلَّا لَدَيْهِ رَقِيبٌ عَتِيدٌۭ
mā yalfiẓu min qawlin illā ladayhi raqībun ʿatīdun
Bã ya lafazi da wata magana fãce a lĩƙe da shi akwai mai tsaro halartacce.
وَجَآءَتْ سَكْرَةُ ٱلْمَوْتِ بِٱلْحَقِّ ۖ ذَٰلِكَ مَا كُنتَ مِنْهُ تَحِيدُ
wajāat sakratu l-mawti bil-ḥaqi dhālika mā kunta min'hu taḥīdu
Kuma mãyen mutuwa ya jẽ da gaskiya. Wannan shĩ ne abin da ka kasance daga gare shi kanã bijirẽwa.
وَنُفِخَ فِى ٱلصُّورِ ۚ ذَٰلِكَ يَوْمُ ٱلْوَعِيدِ
wanufikha fī l-ṣūri dhālika yawmu l-waʿīdi
Kuma aka hũra a cikin ƙaho. Wancan yinin ƙyacẽwar ne fa.
وَجَآءَتْ كُلُّ نَفْسٍۢ مَّعَهَا سَآئِقٌۭ وَشَهِيدٌۭ
wajāat kullu nafsin maʿahā sāiqun washahīdun
Kuma kõwane rai ya zo, tãre da shi akwai mai kõra da mai shaida.
لَّقَدْ كُنتَ فِى غَفْلَةٍۢ مِّنْ هَـٰذَا فَكَشَفْنَا عَنكَ غِطَآءَكَ فَبَصَرُكَ ٱلْيَوْمَ حَدِيدٌۭ
laqad kunta fī ghaflatin min hādhā fakashafnā ʿanka ghiṭāaka fabaṣaruka l-yawma ḥadīdun
(Sai a ce masa): "Lalle ne, haƙĩƙa, ka kasance a cikin gafala daga wannan. To, Mun kuranye maka rufinka, sabõda haka ganinka a yau, mai kaifi ne."
وَقَالَ قَرِينُهُۥ هَـٰذَا مَا لَدَىَّ عَتِيدٌ
waqāla qarīnuhu hādhā mā ladayya ʿatīdun
Kuma abõkin haɗinsa1 ya ce: "Wannan shi ne abin da ke tãre da ni halarce."
أَلْقِيَا فِى جَهَنَّمَ كُلَّ كَفَّارٍ عَنِيدٍۢ
alqiyā fī jahannama kulla kaffārin ʿanīdin
(A ce wa Malã'iku), "Ku jẽfa, a cikin Jahannama, dukan mai yawan kãfirci, mai tsaurin rai."
مَّنَّاعٍۢ لِّلْخَيْرِ مُعْتَدٍۢ مُّرِيبٍ
mannāʿin lil'khayri muʿ'tadin murībin
"Mai yawan hanãwa ga alhẽri, mai zãlunci, mai shakka."
ٱلَّذِى جَعَلَ مَعَ ٱللَّهِ إِلَـٰهًا ءَاخَرَ فَأَلْقِيَاهُ فِى ٱلْعَذَابِ ٱلشَّدِيدِ
alladhī jaʿala maʿa l-lahi ilāhan ākhara fa-alqiyāhu fī l-ʿadhābi l-shadīdi
"Wanda ya sanya, tãre da Allah wani abin bautãwa na dabam, sabõda haka kujẽfa shi a cikin azãba mai tsanani."
۞ قَالَ قَرِينُهُۥ رَبَّنَا مَآ أَطْغَيْتُهُۥ وَلَـٰكِن كَانَ فِى ضَلَـٰلٍۭ بَعِيدٍۢ
qāla qarīnuhu rabbanā mā aṭghaytuhu walākin kāna fī ḍalālin baʿīdin
Abõkin haɗinsa1 ya ce: "Ya Ubangijinmu! Ban sanya shi girman kai ba, kuma amma ya kasance a cikin ɓata mai nĩsa."
قَالَ لَا تَخْتَصِمُوا۟ لَدَىَّ وَقَدْ قَدَّمْتُ إِلَيْكُم بِٱلْوَعِيدِ
qāla lā takhtaṣimū ladayya waqad qaddamtu ilaykum bil-waʿīdi
Ya ce: "Kada ku yi husũma a wur Nalhãli Na gabãtar da ƙyacewa zuwa gare ku."
مَا يُبَدَّلُ ٱلْقَوْلُ لَدَىَّ وَمَآ أَنَا۠ بِظَلَّـٰمٍۢ لِّلْعَبِيدِ
mā yubaddalu l-qawlu ladayya wamā anā biẓallāmin lil'ʿabīdi
"Ba a musanya magana a wuriNa, Kuma Ban zama Mai zãlunci ba ga bãyi Na."
يَوْمَ نَقُولُ لِجَهَنَّمَ هَلِ ٱمْتَلَأْتِ وَتَقُولُ هَلْ مِن مَّزِيدٍۢ
yawma naqūlu lijahannama hali im'talati wataqūlu hal min mazīdin
Rãnar da Muke cẽwa ga Jahannama "Shin, kin cika?" Kuma ta ce: "Ashe,1 akwai wani ƙãri?"
وَأُزْلِفَتِ ٱلْجَنَّةُ لِلْمُتَّقِينَ غَيْرَ بَعِيدٍ
wa-uz'lifati l-janatu lil'muttaqīna ghayra baʿīdin
Kuma a kusantar dã Aljanna ga mãsu taƙawa, ba da nĩsa ba.
هَـٰذَا مَا تُوعَدُونَ لِكُلِّ أَوَّابٍ حَفِيظٍۢ
hādhā mā tūʿadūna likulli awwābin ḥafīẓin
"Wannan shĩ ne abin da ake yi muku wa'adi da shi ga dukan mai yawan kõmawa ga Allah, mai tsarewar (umurninSa).
مَّنْ خَشِىَ ٱلرَّحْمَـٰنَ بِٱلْغَيْبِ وَجَآءَ بِقَلْبٍۢ مُّنِيبٍ
man khashiya l-raḥmāna bil-ghaybi wajāa biqalbin munībin
"Wanda ya ji tsõron Mai rahama a fake, 1kuma ya zo da wata irin zũciya mai tawakkali."
ٱدْخُلُوهَا بِسَلَـٰمٍۢ ۖ ذَٰلِكَ يَوْمُ ٱلْخُلُودِ
ud'khulūhā bisalāmin dhālika yawmu l-khulūdi
(A ce musu) "Ku shige ta da aminci, 1waccan ita ce rãnar dawwama."
لَهُم مَّا يَشَآءُونَ فِيهَا وَلَدَيْنَا مَزِيدٌۭ
lahum mā yashāūna fīhā waladaynā mazīdun
Sunã da abin da suke so a cikinta, kuma tãre da Mũ akwai ƙãrin ni'ima,
وَكَمْ أَهْلَكْنَا قَبْلَهُم مِّن قَرْنٍ هُمْ أَشَدُّ مِنْهُم بَطْشًۭا فَنَقَّبُوا۟ فِى ٱلْبِلَـٰدِ هَلْ مِن مَّحِيصٍ
wakam ahlaknā qablahum min qarnin hum ashaddu min'hum baṭshan fanaqqabū fī l-bilādi hal min maḥīṣin
Kuma da yawa Muka halakar, a gabãninsu, (mutãnen yanzu) ɗaga waɗansu al'ummomi, (waɗanda suke) sũ ne mafi ƙarfin damƙa daga gare su, sa'an nan suka yi bincike a cikin ƙasãshe: 'Kõ akwai wurin tsĩra'?1 (Babu).
إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَذِكْرَىٰ لِمَن كَانَ لَهُۥ قَلْبٌ أَوْ أَلْقَى ٱلسَّمْعَ وَهُوَ شَهِيدٌۭ
inna fī dhālika ladhik'rā liman kāna lahu qalbun aw alqā l-samʿa wahuwa shahīdun
Lalle ne, a cikin wancan, akwai tunãtarwa ga wanda zũciyarsa ta kasance gare shi, kõ kuwa ya jẽfa saurãro, alhãli kuwa yanã halarce (da hankalinsa).
وَلَقَدْ خَلَقْنَا ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضَ وَمَا بَيْنَهُمَا فِى سِتَّةِ أَيَّامٍۢ وَمَا مَسَّنَا مِن لُّغُوبٍۢ
walaqad khalaqnā l-samāwāti wal-arḍa wamā baynahumā fī sittati ayyāmin wamā massanā min lughūbin
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun halitta sammai da ƙasã da abin da ke a tsakãninsu, a cikin kwãnaki shida, alhãli wata'yar wahala ba ta shãfe Mu ba.
فَٱصْبِرْ عَلَىٰ مَا يَقُولُونَ وَسَبِّحْ بِحَمْدِ رَبِّكَ قَبْلَ طُلُوعِ ٱلشَّمْسِ وَقَبْلَ ٱلْغُرُوبِ
fa-iṣ'bir ʿalā mā yaqūlūna wasabbiḥ biḥamdi rabbika qabla ṭulūʿi l-shamsi waqabla l-ghurūbi
Sabõda haka, ka yi haƙuri a kan abin da suke fadã, kuma ka yi tasĩhi1 game da gõdẽ wa Ubangijinka (watau ka yi salla) a gabãnin fitõwar rãnã da gabãnin ɓacẽwarta.
وَمِنَ ٱلَّيْلِ فَسَبِّحْهُ وَأَدْبَـٰرَ ٱلسُّجُودِ
wamina al-layli fasabbiḥ'hu wa-adbāra l-sujūdi
Kuma daga dare, sai ka yi tasbĩhi a gare Shi da bãyan sujada.
وَٱسْتَمِعْ يَوْمَ يُنَادِ ٱلْمُنَادِ مِن مَّكَانٍۢ قَرِيبٍۢ
wa-is'tamiʿ yawma yunādi l-munādi min makānin qarībin
Kuma ka saurãra a rãnar da mai kira ke yin kira daga wuri 1makusanci.
يَوْمَ يَسْمَعُونَ ٱلصَّيْحَةَ بِٱلْحَقِّ ۚ ذَٰلِكَ يَوْمُ ٱلْخُرُوجِ
yawma yasmaʿūna l-ṣayḥata bil-ḥaqi dhālika yawmu l-khurūji
Rãnar da suke saurãron tsãwa da gaskiya. Wancan shĩ ne yinin fita (daga kabari).
إِنَّا نَحْنُ نُحْىِۦ وَنُمِيتُ وَإِلَيْنَا ٱلْمَصِيرُ
innā naḥnu nuḥ'yī wanumītu wa-ilaynā l-maṣīru
Lalle Mũ ne haƙĩƙa, Mu ne ke rãyarwa, kuma Mũ ne ke kashẽwa, kuma zuwa gare Mu kawai ne makõmar take.
يَوْمَ تَشَقَّقُ ٱلْأَرْضُ عَنْهُمْ سِرَاعًۭا ۚ ذَٰلِكَ حَشْرٌ عَلَيْنَا يَسِيرٌۭ
yawma tashaqqaqu l-arḍu ʿanhum sirāʿan dhālika ḥashrun ʿalaynā yasīrun
Rãnar da ƙasã ke tsattsãgẽwa daga gare su, sunã mãsu gaggãwa. Wancan tãrãwar mutãne ne, mai sauƙi a gare Mu.
نَّحْنُ أَعْلَمُ بِمَا يَقُولُونَ ۖ وَمَآ أَنتَ عَلَيْهِم بِجَبَّارٍۢ ۖ فَذَكِّرْ بِٱلْقُرْءَانِ مَن يَخَافُ وَعِيدِ
naḥnu aʿlamu bimā yaqūlūna wamā anta ʿalayhim bijabbārin fadhakkir bil-qur'āni man yakhāfu waʿīdi
Mũ ne mafi sani game da abin da suke faɗi, kuma bã zã ka zama mai tĩlasta su ba. Sabõda haka ka tunatar game da Alƙur'ani,1 ga wanda ke tsõron ƙyacewaTa.