53

النجم

An-Najm

The Star

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ Da sunan Allah Mai rahama Mai jin kai
Ayoyi 62
Juzu'i 27
Shafi 526-528
Nau'i Makkiya
Tsarin Saukarwa 23
0:00 / 0:00
Aya: 1 / 62
1

وَٱلنَّجْمِ إِذَا هَوَىٰ

wal-najmi idhā hawā

Inã rantsuwa da taurãron, a lõkacin da ya faku.

2

مَا ضَلَّ صَاحِبُكُمْ وَمَا غَوَىٰ

mā ḍalla ṣāḥibukum wamā ghawā

Ma'abũcinku bai ɓata ba, kuma bai ƙẽtare haddi ba.

3

وَمَا يَنطِقُ عَنِ ٱلْهَوَىٰٓ

wamā yanṭiqu ʿani l-hawā

Kuma bã ya yin magana daga son zuciyarsa.

4

إِنْ هُوَ إِلَّا وَحْىٌۭ يُوحَىٰ

in huwa illā waḥyun yūḥā

(Maganarsa) ba ta zamo ba, fãce wahayi ne da ake aikõwa.

5

عَلَّمَهُۥ شَدِيدُ ٱلْقُوَىٰ

ʿallamahu shadīdu l-quwā

(Malã'ika) mai tsananin ƙarfi 1ya sanar da shi.

6

ذُو مِرَّةٍۢ فَٱسْتَوَىٰ

dhū mirratin fa-is'tawā

Ma'abũcin ƙarfi da kwarjini, sa'an nan ya daidaita.

7

وَهُوَ بِٱلْأُفُقِ ٱلْأَعْلَىٰ

wahuwa bil-ufuqi l-aʿlā

Alhãli kuwa yanã a sararin samã mafi daukaka.

8

ثُمَّ دَنَا فَتَدَلَّىٰ

thumma danā fatadallā

Sa'an nan ya kusanta, kuma ya matsa zurõwa.

9

فَكَانَ قَابَ قَوْسَيْنِ أَوْ أَدْنَىٰ

fakāna qāba qawsayni aw adnā

Har ya kasance gwargwadon zirã'i biyu, kõ kuma abin da ya fi kusa.

10

فَأَوْحَىٰٓ إِلَىٰ عَبْدِهِۦ مَآ أَوْحَىٰ

fa-awḥā ilā ʿabdihi mā awḥā

Sa'an nan ya yi wahayi zuwa ga bãwan Allah (Muhammadu) da abin da ya faɗa (masa).

11

مَا كَذَبَ ٱلْفُؤَادُ مَا رَأَىٰٓ

mā kadhaba l-fuādu mā raā

Zũciyar (Annabi) bata ƙaryata abin da ya gani ba.

12

أَفَتُمَـٰرُونَهُۥ عَلَىٰ مَا يَرَىٰ

afatumārūnahu ʿalā mā yarā

Shin, zã ku yi masa musu a kan abin da yake gani?

13

وَلَقَدْ رَءَاهُ نَزْلَةً أُخْرَىٰ

walaqad raāhu nazlatan ukh'rā

Kuma lalle ya gan shi, haƙĩƙatan, a wani lõkacin saukarsa.1

14

عِندَ سِدْرَةِ ٱلْمُنتَهَىٰ

ʿinda sid'rati l-muntahā

A wurin da magaryar tuƙẽwa take.

15

عِندَهَا جَنَّةُ ٱلْمَأْوَىٰٓ

ʿindahā jannatu l-mawā

A inda taken, nan Aljannar makoma take.

16

إِذْ يَغْشَى ٱلسِّدْرَةَ مَا يَغْشَىٰ

idh yaghshā l-sid'rata mā yaghshā

Lõkacin da abin da yake rufe magaryar tuƙẽwa ya rufe ta.

17

مَا زَاغَ ٱلْبَصَرُ وَمَا طَغَىٰ

mā zāgha l-baṣaru wamā ṭaghā

Ganinsa1 bai karkata ba, kuma bai ƙetare haddi ba.

18

لَقَدْ رَأَىٰ مِنْ ءَايَـٰتِ رَبِّهِ ٱلْكُبْرَىٰٓ

laqad raā min āyāti rabbihi l-kub'rā

Lalle, tabbas, (Annabinku) ya ga waɗanda suka fi girma1 daga ãyõyin Ubangijinsa.

19

أَفَرَءَيْتُمُ ٱللَّـٰتَ وَٱلْعُزَّىٰ

afara-aytumu l-lāta wal-ʿuzā

Shin, kun ga Lãta da uzza?1

20

وَمَنَوٰةَ ٱلثَّالِثَةَ ٱلْأُخْرَىٰٓ

wamanata l-thālithata l-ukh'rā

Da (wani gunki wai shi) Manãta, na ukunsu?

21

أَلَكُمُ ٱلذَّكَرُ وَلَهُ ٱلْأُنثَىٰ

alakumu l-dhakaru walahu l-unthā

Ashe, kũ ne da ɗa namiji Shĩ (Allah) kuma da ɗiya mace?

22

تِلْكَ إِذًۭا قِسْمَةٌۭ ضِيزَىٰٓ

til'ka idhan qis'matun ḍīzā

Wannan fa ya zama rabo naƙasasshe.

23

إِنْ هِىَ إِلَّآ أَسْمَآءٌۭ سَمَّيْتُمُوهَآ أَنتُمْ وَءَابَآؤُكُم مَّآ أَنزَلَ ٱللَّهُ بِهَا مِن سُلْطَـٰنٍ ۚ إِن يَتَّبِعُونَ إِلَّا ٱلظَّنَّ وَمَا تَهْوَى ٱلْأَنفُسُ ۖ وَلَقَدْ جَآءَهُم مِّن رَّبِّهِمُ ٱلْهُدَىٰٓ

in hiya illā asmāon sammaytumūhā antum waābāukum mā anzala l-lahu bihā min sul'ṭānin in yattabiʿūna illā l-ẓana wamā tahwā l-anfusu walaqad jāahum min rabbihimu l-hudā

Waɗannan bã kõme ba ne fãce sũnãye, waɗanda kuka ambace su da su, kũ da uwãyenku. Allah bai saukar da wani dalĩli game da su ba. (Kãfirai) bã su biyar kõme fãce zato da abin da rãyukansu ke so, Alhãli kuwa shiriyar1 ta daga wajen Ubangijinsu, ta jẽ musu (sai suka bar ta suka kõma wa zaton).

24

أَمْ لِلْإِنسَـٰنِ مَا تَمَنَّىٰ

am lil'insāni mā tamannā

Ko (an fai cẽwa) mutum zai sãmi abin da yake gũri?

25

فَلِلَّهِ ٱلْـَٔاخِرَةُ وَٱلْأُولَىٰ

falillahi l-ākhiratu wal-ūlā

To, Lãhira da dũniya na Allah kawai ne (wanda ya nẽme su daga wani, yã yi kuskure).

26

۞ وَكَم مِّن مَّلَكٍۢ فِى ٱلسَّمَـٰوَٰتِ لَا تُغْنِى شَفَـٰعَتُهُمْ شَيْـًٔا إِلَّا مِنۢ بَعْدِ أَن يَأْذَنَ ٱللَّهُ لِمَن يَشَآءُ وَيَرْضَىٰٓ

wakam min malakin fī l-samāwāti lā tugh'nī shafāʿatuhum shayan illā min baʿdi an yadhana l-lahu liman yashāu wayarḍā

Akwai malã'iku da yawa a cikin sammai cẽtonsu bã ya wadãtar da kõme fãce bãyan Allah Yã yi izni (da shi) ga wanda Yake so, kuma Yake yarda.

27

إِنَّ ٱلَّذِينَ لَا يُؤْمِنُونَ بِٱلْـَٔاخِرَةِ لَيُسَمُّونَ ٱلْمَلَـٰٓئِكَةَ تَسْمِيَةَ ٱلْأُنثَىٰ

inna alladhīna lā yu'minūna bil-ākhirati layusammūna l-malāikata tasmiyata l-unthā

Lalle waɗannan da bã su yin ĩmãni da Lãhira, haƙĩƙa sunã kiran malã'iku da sũnan mace.

28

وَمَا لَهُم بِهِۦ مِنْ عِلْمٍ ۖ إِن يَتَّبِعُونَ إِلَّا ٱلظَّنَّ ۖ وَإِنَّ ٱلظَّنَّ لَا يُغْنِى مِنَ ٱلْحَقِّ شَيْـًۭٔا

wamā lahum bihi min ʿil'min in yattabiʿūna illā l-ẓana wa-inna l-ẓana lā yugh'nī mina l-ḥaqi shayan

Kuma bã su da wani ilmi game da shi, bã su bin kõme fãce zato alhãli kuwa lalle zato bã ya amfãnar da kõme daga gaskiya.

29

فَأَعْرِضْ عَن مَّن تَوَلَّىٰ عَن ذِكْرِنَا وَلَمْ يُرِدْ إِلَّا ٱلْحَيَوٰةَ ٱلدُّنْيَا

fa-aʿriḍ ʿan man tawallā ʿan dhik'rinā walam yurid illā l-ḥayata l-dun'yā

Sabõda haka sai ka kau da kai daga wanda ya jũya bãya daga ambaton Mu kuma bai yi nufin kõme ba fãce rãyuwar kusa (dũniya).

30

ذَٰلِكَ مَبْلَغُهُم مِّنَ ٱلْعِلْمِ ۚ إِنَّ رَبَّكَ هُوَ أَعْلَمُ بِمَن ضَلَّ عَن سَبِيلِهِۦ وَهُوَ أَعْلَمُ بِمَنِ ٱهْتَدَىٰ

dhālika mablaghuhum mina l-ʿil'mi inna rabbaka huwa aʿlamu biman ḍalla ʿan sabīlihi wahuwa aʿlamu bimani ih'tadā

Wannan ita ce iyãkar abin da suke iya kai gare shi na ilmi. lalle Ubangijinka Shĩ ne Mafi sanin wanda ya ɓace daga hanyar Sa, kuma Shi ne Mafi sani ga wanda ya nẽmi shiriya.

31

وَلِلَّهِ مَا فِى ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَمَا فِى ٱلْأَرْضِ لِيَجْزِىَ ٱلَّذِينَ أَسَـٰٓـُٔوا۟ بِمَا عَمِلُوا۟ وَيَجْزِىَ ٱلَّذِينَ أَحْسَنُوا۟ بِٱلْحُسْنَى

walillahi mā fī l-samāwāti wamā fī l-arḍi liyajziya alladhīna asāū bimā ʿamilū wayajziya alladhīna aḥsanū bil-ḥus'nā

Kuma abin da ke cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasã na Allah kawai ne, dõmin Yã sãka wa waɗanda suka mũnana da abin da suka aikata, kuma Ya sãka wa waɗanda suki kyautata da sakamakon da ya fi kyau.

32

ٱلَّذِينَ يَجْتَنِبُونَ كَبَـٰٓئِرَ ٱلْإِثْمِ وَٱلْفَوَٰحِشَ إِلَّا ٱللَّمَمَ ۚ إِنَّ رَبَّكَ وَٰسِعُ ٱلْمَغْفِرَةِ ۚ هُوَ أَعْلَمُ بِكُمْ إِذْ أَنشَأَكُم مِّنَ ٱلْأَرْضِ وَإِذْ أَنتُمْ أَجِنَّةٌۭ فِى بُطُونِ أُمَّهَـٰتِكُمْ ۖ فَلَا تُزَكُّوٓا۟ أَنفُسَكُمْ ۖ هُوَ أَعْلَمُ بِمَنِ ٱتَّقَىٰٓ

alladhīna yajtanibūna kabāira l-ith'mi wal-fawāḥisha illā l-lamama inna rabbaka wāsiʿu l-maghfirati huwa aʿlamu bikum idh ansha-akum mina l-arḍi wa-idh antum ajinnatun fī buṭūni ummahātikum falā tuzakkū anfusakum huwa aʿlamu bimani ittaqā

Waɗanda ke nĩsantar manyan zunubai da abũbuwan alfãsha, fãce ƙanãnan laifuffuka, lalle Ubangijinka Mai yalwatattar gãfara ne, Shĩ ne Ya fi sani ga abinda ke gare ku a lõkacin da Ya ƙãga halittarku daga ƙasa, kuma a lõkacin da kuke tãyuna a cikin cikannan uwãyenku. Sabõda haka, kada ku tsarkake1 kanku, Shĩ ne Mafi sani ga wanda ya yi taƙawa.

33

أَفَرَءَيْتَ ٱلَّذِى تَوَلَّىٰ

afara-ayta alladhī tawallā

Shin, ka ga wannan da ya jũya baya?

34

وَأَعْطَىٰ قَلِيلًۭا وَأَكْدَىٰٓ

wa-aʿṭā qalīlan wa-akdā

Ya yi kyauta kaɗan, kuma ya yi rowa?

35

أَعِندَهُۥ عِلْمُ ٱلْغَيْبِ فَهُوَ يَرَىٰٓ

aʿindahu ʿil'mu l-ghaybi fahuwa yarā

Shin, akwai ilmin gaibi a wurinsa, Sabõda haka yanã ganin gaibin?

36

أَمْ لَمْ يُنَبَّأْ بِمَا فِى صُحُفِ مُوسَىٰ

am lam yunabba bimā fī ṣuḥufi mūsā

Ko kuwa ba a ba shi lãbãri ba ga abin da yake a cikin Littafan Mũsã?

37

وَإِبْرَٰهِيمَ ٱلَّذِى وَفَّىٰٓ

wa-ib'rāhīma alladhī waffā

Da Ibrãhĩm wanda ya cika alkawari?

38

أَلَّا تَزِرُ وَازِرَةٌۭ وِزْرَ أُخْرَىٰ

allā taziru wāziratun wiz'ra ukh'rā

Cẽwa wani rai mai kãyan laifi bã ya ɗaukar kãyan laifin wani.

39

وَأَن لَّيْسَ لِلْإِنسَـٰنِ إِلَّا مَا سَعَىٰ

wa-an laysa lil'insāni illā mā saʿā

Kuma mutum bã shi da kõme fãce abin da ya aikata.

40

وَأَنَّ سَعْيَهُۥ سَوْفَ يُرَىٰ

wa-anna saʿyahu sawfa yurā

Kuma lalle, aikinsa zã a gan shi.

41

ثُمَّ يُجْزَىٰهُ ٱلْجَزَآءَ ٱلْأَوْفَىٰ

thumma yuj'zāhu l-jazāa l-awfā

Sa'an nan a sãka masa da sakamako wanda yake mafi cikar ma'auni?

42

وَأَنَّ إِلَىٰ رَبِّكَ ٱلْمُنتَهَىٰ

wa-anna ilā rabbika l-muntahā

Kuma lalle, makõmar zuwa Ubangijinka kawai take?

43

وَأَنَّهُۥ هُوَ أَضْحَكَ وَأَبْكَىٰ

wa-annahu huwa aḍḥaka wa-abkā

Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya sanya dariya, kuma Ya sanya kũka.

44

وَأَنَّهُۥ هُوَ أَمَاتَ وَأَحْيَا

wa-annahu huwa amāta wa-aḥyā

Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya kashe, kuma Ya rãyar.

45

وَأَنَّهُۥ خَلَقَ ٱلزَّوْجَيْنِ ٱلذَّكَرَ وَٱلْأُنثَىٰ

wa-annahu khalaqa l-zawjayni l-dhakara wal-unthā

Kuma lalle Shĩ ne Ya yi halitta nau'i-nau'i, namiji da mace.

46

مِن نُّطْفَةٍ إِذَا تُمْنَىٰ

min nuṭ'fatin idhā tum'nā

Daga wani ɗigon ruwa guda a lõkacin da ake jẽfa shi a cikin mahaifa.

47

وَأَنَّ عَلَيْهِ ٱلنَّشْأَةَ ٱلْأُخْرَىٰ

wa-anna ʿalayhi l-nashata l-ukh'rā

Kuma a kansa ne ƙãga halitta ta biyu take.

48

وَأَنَّهُۥ هُوَ أَغْنَىٰ وَأَقْنَىٰ

wa-annahu huwa aghnā wa-aqnā

Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya azurta, kuma Ya wadãtar.

49

وَأَنَّهُۥ هُوَ رَبُّ ٱلشِّعْرَىٰ

wa-annahu huwa rabbu l-shiʿ'rā

Kuma lalle, Shĩ, Shi ne Ubangijin Shi'ira.1

50

وَأَنَّهُۥٓ أَهْلَكَ عَادًا ٱلْأُولَىٰ

wa-annahu ahlaka ʿādan l-ūlā

Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya halaka Ãdãwa na farko.

51

وَثَمُودَا۟ فَمَآ أَبْقَىٰ

wathamūdā famā abqā

Da Samũdãwa, sa'an nan bai rage su ba.

52

وَقَوْمَ نُوحٍۢ مِّن قَبْلُ ۖ إِنَّهُمْ كَانُوا۟ هُمْ أَظْلَمَ وَأَطْغَىٰ

waqawma nūḥin min qablu innahum kānū hum aẓlama wa-aṭghā

Da mutãnen Nũhu a gabãnin haka, lalle sũ sun kasance mafi zãlunci kuma mafi girman kai.

53

وَٱلْمُؤْتَفِكَةَ أَهْوَىٰ

wal-mu'tafikata ahwā

Da waɗanda aka birkice 1ƙasarsu, Ya kãyar da su.

54

فَغَشَّىٰهَا مَا غَشَّىٰ

faghashāhā mā ghashā

Sa'an nan abin da ya rufe su, ya rufe su.

55

فَبِأَىِّ ءَالَآءِ رَبِّكَ تَتَمَارَىٰ

fabi-ayyi ālāi rabbika tatamārā

To, da wace daga ni'imõmin Ubangijinka kake 1yin shakka?

56

هَـٰذَا نَذِيرٌۭ مِّنَ ٱلنُّذُرِ ٱلْأُولَىٰٓ

hādhā nadhīrun mina l-nudhuri l-ūlā

wannan (Muhammadu) mai gargaɗi ne kamar irin mãsu gargaɗi na farko.

57

أَزِفَتِ ٱلْـَٔازِفَةُ

azifati l-āzifatu

Makusanciya1 fa, tã yi kusa.

58

لَيْسَ لَهَا مِن دُونِ ٱللَّهِ كَاشِفَةٌ

laysa lahā min dūni l-lahi kāshifatun

Bãbu wani rai, banda Allah, mai iya bãyani gare ta.

59

أَفَمِنْ هَـٰذَا ٱلْحَدِيثِ تَعْجَبُونَ

afamin hādhā l-ḥadīthi taʿjabūna

Shin, kuma daga wannan 1lãbãri kuke mãmãki?

60

وَتَضْحَكُونَ وَلَا تَبْكُونَ

wataḍḥakūna walā tabkūna

Kuma kunã yin dãriya, kuma bã ku yin kũka?

61

وَأَنتُمْ سَـٰمِدُونَ

wa-antum sāmidūna

Alhãli kunã mãsu wãsã?

62

فَٱسْجُدُوا۟ لِلَّهِ وَٱعْبُدُوا۟ ۩

fa-us'judū lillahi wa-uʿ'budū

To, ku yi tawãli'u 1ga Allah, kuma ku bauta (masa).

Sujada

Game da Wannan Sura