يوسف
Yusuf
Joseph
الٓر ۚ تِلْكَ ءَايَـٰتُ ٱلْكِتَـٰبِ ٱلْمُبِينِ
alif-lam-ra til'ka āyātu l-kitābi l-mubīni
A. L̃.R. Waɗancan ãyoyin Littãfi mai bayyanãwa ne.
إِنَّآ أَنزَلْنَـٰهُ قُرْءَٰنًا عَرَبِيًّۭا لَّعَلَّكُمْ تَعْقِلُونَ
innā anzalnāhu qur'ānan ʿarabiyyan laʿallakum taʿqilūna
Lalle ne Mũ, Mun saukar da shi, yanã abin karantãwa na Lãrabci; tsammãninkũ, kunã hankalta.
نَحْنُ نَقُصُّ عَلَيْكَ أَحْسَنَ ٱلْقَصَصِ بِمَآ أَوْحَيْنَآ إِلَيْكَ هَـٰذَا ٱلْقُرْءَانَ وَإِن كُنتَ مِن قَبْلِهِۦ لَمِنَ ٱلْغَـٰفِلِينَ
naḥnu naquṣṣu ʿalayka aḥsana l-qaṣaṣi bimā awḥaynā ilayka hādhā l-qur'āna wa-in kunta min qablihi lamina l-ghāfilīna
Mũ, Munã bãyar da lãbãri a gare ka, mafi kyãwon lãbãri ga abin da Muka yi wahayin wannan Alƙur'ãni zuwa gare ka. Kuma lalle ne kã kasance a gabãninsa, haƙĩƙa, daga gafalallu.
إِذْ قَالَ يُوسُفُ لِأَبِيهِ يَـٰٓأَبَتِ إِنِّى رَأَيْتُ أَحَدَ عَشَرَ كَوْكَبًۭا وَٱلشَّمْسَ وَٱلْقَمَرَ رَأَيْتُهُمْ لِى سَـٰجِدِينَ
idh qāla yūsufu li-abīhi yāabati innī ra-aytu aḥada ʿashara kawkaban wal-shamsa wal-qamara ra-aytuhum lī sājidīna
A lõkacin da Yũsufu ya ce wa ubansa, "Yã bãba! Lalle ne nĩ, nã ga taurãri gõma shã ɗaya, da rãnã da watã. Na gan su sunã mãsu sujada a gare ni."
قَالَ يَـٰبُنَىَّ لَا تَقْصُصْ رُءْيَاكَ عَلَىٰٓ إِخْوَتِكَ فَيَكِيدُوا۟ لَكَ كَيْدًا ۖ إِنَّ ٱلشَّيْطَـٰنَ لِلْإِنسَـٰنِ عَدُوٌّۭ مُّبِينٌۭ
qāla yābunayya lā taqṣuṣ ru'yāka ʿalā ikh'watika fayakīdū laka kaydan inna l-shayṭāna lil'insāni ʿaduwwun mubīnun
Ya ce: "Ya ƙaramin ɗãna! Kada ka faɗi mafarkinka ga 'yan'uwanka, har su ƙulla maka wani kaidi. Lalle ne Shaidan ga mutum, haƙĩƙa, maƙiyi ne bayyanãnne.1
وَكَذَٰلِكَ يَجْتَبِيكَ رَبُّكَ وَيُعَلِّمُكَ مِن تَأْوِيلِ ٱلْأَحَادِيثِ وَيُتِمُّ نِعْمَتَهُۥ عَلَيْكَ وَعَلَىٰٓ ءَالِ يَعْقُوبَ كَمَآ أَتَمَّهَا عَلَىٰٓ أَبَوَيْكَ مِن قَبْلُ إِبْرَٰهِيمَ وَإِسْحَـٰقَ ۚ إِنَّ رَبَّكَ عَلِيمٌ حَكِيمٌۭ
wakadhālika yajtabīka rabbuka wayuʿallimuka min tawīli l-aḥādīthi wayutimmu niʿ'matahu ʿalayka waʿalā āli yaʿqūba kamā atammahā ʿalā abawayka min qablu ib'rāhīma wa-is'ḥāqa inna rabbaka ʿalīmun ḥakīmun
"Kuma kãmar wancan ne, Ubangijinka Yake zãɓen ka, kuma Ya sanar da kai daga fassarar lãbãrai, kuma ya cika ni'imõminSa a kanka, kuma a kan gidan Yãƙũba kãmar yadda ya cika su a kan ubanninka biyu, a gabãni, Ibrãhĩm da Is'hãƙa. Lalle Ubangijinka ne Masani, Mai hikima."
۞ لَّقَدْ كَانَ فِى يُوسُفَ وَإِخْوَتِهِۦٓ ءَايَـٰتٌۭ لِّلسَّآئِلِينَ
laqad kāna fī yūsufa wa-ikh'watihi āyātun lilssāilīna
Lalle ne, haƙĩƙa, ãyõyi1 sun kasance ga Yũsufu da 'yan'uwansa11 dõmin mãsu tambaya.
إِذْ قَالُوا۟ لَيُوسُفُ وَأَخُوهُ أَحَبُّ إِلَىٰٓ أَبِينَا مِنَّا وَنَحْنُ عُصْبَةٌ إِنَّ أَبَانَا لَفِى ضَلَـٰلٍۢ مُّبِينٍ
idh qālū layūsufu wa-akhūhu aḥabbu ilā abīnā minnā wanaḥnu ʿuṣ'batun inna abānā lafī ḍalālin mubīnin
A lõkacin da suka ce:1 lalle ne Yũsufu da ɗan'uwansa ne mafiya sõyuwa ga ubanmu daga gare mu, alhãli kuwa mũ jama'a guda ne. Lalle ubanmu, haƙĩƙa, yanã cikin ɓata bayyananniya.
ٱقْتُلُوا۟ يُوسُفَ أَوِ ٱطْرَحُوهُ أَرْضًۭا يَخْلُ لَكُمْ وَجْهُ أَبِيكُمْ وَتَكُونُوا۟ مِنۢ بَعْدِهِۦ قَوْمًۭا صَـٰلِحِينَ
uq'tulū yūsufa awi iṭ'raḥūhu arḍan yakhlu lakum wajhu abīkum watakūnū min baʿdihi qawman ṣāliḥīna
Ku kashe Yũsufu, kõ kuwa ku jẽfa shi a wata ƙasa, fuskar ubanku ta wõfinta sabõda ku, kuma ku kasance a bãyansa mutãne sãlihai.
قَالَ قَآئِلٌۭ مِّنْهُمْ لَا تَقْتُلُوا۟ يُوسُفَ وَأَلْقُوهُ فِى غَيَـٰبَتِ ٱلْجُبِّ يَلْتَقِطْهُ بَعْضُ ٱلسَّيَّارَةِ إِن كُنتُمْ فَـٰعِلِينَ
qāla qāilun min'hum lā taqtulū yūsufa wa-alqūhu fī ghayābati l-jubi yaltaqiṭ'hu baʿḍu l-sayārati in kuntum fāʿilīna
Wani mai magana daga cikinsu ya ce: "Kada ku kashe Yũsufu. Ku jẽfa shi a cikin duhun rĩjiya, wasu matafiya su tsince shi, idan kun kasance mãsu aikatãwa ne."
قَالُوا۟ يَـٰٓأَبَانَا مَا لَكَ لَا تَأْمَ۫نَّا عَلَىٰ يُوسُفَ وَإِنَّا لَهُۥ لَنَـٰصِحُونَ
qālū yāabānā mā laka lā tamannā ʿalā yūsufa wa-innā lahu lanāṣiḥūna
Suka ce: "Yã bãbanmu1! Mẽne ne a gare ka ba ka amince mana ba a kan Yũsufu, alhãlikuwa lalle ne mũ, haƙãƙa mãsu nashĩha muke a gare shi?"
أَرْسِلْهُ مَعَنَا غَدًۭا يَرْتَعْ وَيَلْعَبْ وَإِنَّا لَهُۥ لَحَـٰفِظُونَ
arsil'hu maʿanā ghadan yartaʿ wayalʿab wa-innā lahu laḥāfiẓūna
"Ka bar shi tãre da mu a gõbe, ya ji dãɗi, kuma ya yi wãsa. Kuma lalle ne mu, a gare shi, mãsu tsaro ne."
قَالَ إِنِّى لَيَحْزُنُنِىٓ أَن تَذْهَبُوا۟ بِهِۦ وَأَخَافُ أَن يَأْكُلَهُ ٱلذِّئْبُ وَأَنتُمْ عَنْهُ غَـٰفِلُونَ
qāla innī layaḥzununī an tadhhabū bihi wa-akhāfu an yakulahu l-dhi'bu wa-antum ʿanhu ghāfilūna
Ya ce: "Lalle ne ni, haƙãƙa yanã ɓãta mini rai ku tafii da shi, Kuma inã tsõron kerkẽci ya cinye shi, alhãli ku kuwa kunã mãsu shagala daga gare shi."
قَالُوا۟ لَئِنْ أَكَلَهُ ٱلذِّئْبُ وَنَحْنُ عُصْبَةٌ إِنَّآ إِذًۭا لَّخَـٰسِرُونَ
qālū la-in akalahu l-dhi'bu wanaḥnu ʿuṣ'batun innā idhan lakhāsirūna
Suka ce: "Haƙĩƙa idan kerkẽci ya cinye shi, alhãli kuwa munã dangin jũna, lalle ne mũ, a sa'an nan, hakĩka, mun zama mãsu hasãra."
فَلَمَّا ذَهَبُوا۟ بِهِۦ وَأَجْمَعُوٓا۟ أَن يَجْعَلُوهُ فِى غَيَـٰبَتِ ٱلْجُبِّ ۚ وَأَوْحَيْنَآ إِلَيْهِ لَتُنَبِّئَنَّهُم بِأَمْرِهِمْ هَـٰذَا وَهُمْ لَا يَشْعُرُونَ
falammā dhahabū bihi wa-ajmaʿū an yajʿalūhu fī ghayābati l-jubi wa-awḥaynā ilayhi latunabbi-annahum bi-amrihim hādhā wahum lā yashʿurūna
To, a lõkacin1 da suka tafi da shi, kuma suka yi niyyar su sanya shi a cikin duhun rĩjiya, Muka yi wahayi zuwa gare shi, "Lalle ne, kanã bã su lãbari game da wannan al'amari nãsu, kuma sũ ba su sani ba."
وَجَآءُوٓ أَبَاهُمْ عِشَآءًۭ يَبْكُونَ
wajāū abāhum ʿishāan yabkūna
Kuma suka je wa ubansu da dare sunã kũka.
قَالُوا۟ يَـٰٓأَبَانَآ إِنَّا ذَهَبْنَا نَسْتَبِقُ وَتَرَكْنَا يُوسُفَ عِندَ مَتَـٰعِنَا فَأَكَلَهُ ٱلذِّئْبُ ۖ وَمَآ أَنتَ بِمُؤْمِنٍۢ لَّنَا وَلَوْ كُنَّا صَـٰدِقِينَ
qālū yāabānā innā dhahabnā nastabiqu wataraknā yūsufa ʿinda matāʿinā fa-akalahu l-dhi'bu wamā anta bimu'minin lanā walaw kunnā ṣādiqīna
Suka ce: "Yã bãbanmu!1 Lalle ne, mun tafi munã tsẽre, kuma muka bar Yusufu a wurin kãyanmu, sai kerkẽci ya cinye shi, kuma kai, bã mai amincẽwa da mu ba ne, kuma kõ dã mun kasance mãsu gaskiya!"_
وَجَآءُو عَلَىٰ قَمِيصِهِۦ بِدَمٍۢ كَذِبٍۢ ۚ قَالَ بَلْ سَوَّلَتْ لَكُمْ أَنفُسُكُمْ أَمْرًۭا ۖ فَصَبْرٌۭ جَمِيلٌۭ ۖ وَٱللَّهُ ٱلْمُسْتَعَانُ عَلَىٰ مَا تَصِفُونَ
wajāū ʿalā qamīṣihi bidamin kadhibin qāla bal sawwalat lakum anfusukum amran faṣabrun jamīlun wal-lahu l-mus'taʿānu ʿalā mā taṣifūna
Kuma suka je, a jikin rigarsa akwai wani jinin ƙarya. Ya ce: "Ã'a, zukatanku suka ƙawãta muku wani al'amari. Sai haƙuri mai kyau! Kuma Allah ne wanda ake nẽman taimako (a gunSa) a kan abin da kuke siffantãwa."
وَجَآءَتْ سَيَّارَةٌۭ فَأَرْسَلُوا۟ وَارِدَهُمْ فَأَدْلَىٰ دَلْوَهُۥ ۖ قَالَ يَـٰبُشْرَىٰ هَـٰذَا غُلَـٰمٌۭ ۚ وَأَسَرُّوهُ بِضَـٰعَةًۭ ۚ وَٱللَّهُ عَلِيمٌۢ بِمَا يَعْمَلُونَ
wajāat sayyāratun fa-arsalū wāridahum fa-adlā dalwahu qāla yābush'rā hādhā ghulāmun wa-asarrūhu biḍāʿatan wal-lahu ʿalīmun bimā yaʿmalūna
Kuma wani ãyari1 ya je, sai suka aika mai nẽman musu rũwa, sai ya zura gugansa, ya ce: "Yã bushãrata! Wannan yãro ne." Kuma suka ɓõye shi yanã abin sayarwa. Kuma Allah ne Masani ga abin da suke aikatãwa.
وَشَرَوْهُ بِثَمَنٍۭ بَخْسٍۢ دَرَٰهِمَ مَعْدُودَةٍۢ وَكَانُوا۟ فِيهِ مِنَ ٱلزَّٰهِدِينَ
washarawhu bithamanin bakhsin darāhima maʿdūdatin wakānū fīhi mina l-zāhidīna
Kuma suka sayar1 da shi da 'yan kuɗi kaɗan, dirhamõmi ƙidãyayyu, Kuma sun kasance, a wurinsa, daga mãsu isuwa da abu kaɗan.
وَقَالَ ٱلَّذِى ٱشْتَرَىٰهُ مِن مِّصْرَ لِٱمْرَأَتِهِۦٓ أَكْرِمِى مَثْوَىٰهُ عَسَىٰٓ أَن يَنفَعَنَآ أَوْ نَتَّخِذَهُۥ وَلَدًۭا ۚ وَكَذَٰلِكَ مَكَّنَّا لِيُوسُفَ فِى ٱلْأَرْضِ وَلِنُعَلِّمَهُۥ مِن تَأْوِيلِ ٱلْأَحَادِيثِ ۚ وَٱللَّهُ غَالِبٌ عَلَىٰٓ أَمْرِهِۦ وَلَـٰكِنَّ أَكْثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَعْلَمُونَ
waqāla alladhī ish'tarāhu min miṣ'ra li-im'ra-atihi akrimī mathwāhu ʿasā an yanfaʿanā aw nattakhidhahu waladan wakadhālika makkannā liyūsufa fī l-arḍi walinuʿallimahu min tawīli l-aḥādīthi wal-lahu ghālibun ʿalā amrihi walākinna akthara l-nāsi lā yaʿlamūna
Kuma wanda ya saye shi daga Masar1 ya ce wa mãtarsa, "Ki girmama mazauninsa, akwai tsammãnin ya amfãne mu, kõ kuwa mu riƙe shi ɗã."Kuma kamar wancan ne Muka tabbatar ga Yũsufu, a cikin ƙasa kuma dõmin Mu sanar da shi daia fassarar lũbũru, kuma Allah ne Marinjãyi a kan al'amarinSa, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba."
وَلَمَّا بَلَغَ أَشُدَّهُۥٓ ءَاتَيْنَـٰهُ حُكْمًۭا وَعِلْمًۭا ۚ وَكَذَٰلِكَ نَجْزِى ٱلْمُحْسِنِينَ
walammā balagha ashuddahu ātaynāhu ḥuk'man waʿil'man wakadhālika najzī l-muḥ'sinīna
Kuma a lõkacin da ya isa mafi ƙarfinsa, Muka bã shi hukunci da ilmi. Kuma kamar wancan ne Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
وَرَٰوَدَتْهُ ٱلَّتِى هُوَ فِى بَيْتِهَا عَن نَّفْسِهِۦ وَغَلَّقَتِ ٱلْأَبْوَٰبَ وَقَالَتْ هَيْتَ لَكَ ۚ قَالَ مَعَاذَ ٱللَّهِ ۖ إِنَّهُۥ رَبِّىٓ أَحْسَنَ مَثْوَاىَ ۖ إِنَّهُۥ لَا يُفْلِحُ ٱلظَّـٰلِمُونَ
warāwadathu allatī huwa fī baytihā ʿan nafsihi waghallaqati l-abwāba waqālat hayta laka qāla maʿādha l-lahi innahu rabbī aḥsana mathwāya innahu lā yuf'liḥu l-ẓālimūna
Kuma wadda yake 1a cikin ɗãkinta, ta nẽme shi ga kansa, kuma ta kukkulle ƙõfõfi, kuma ta ce, "Yã rage a gare ka!" ya ce: "Ina neman tsarin Allah! Lalle shĩne Ubangijina. Yã kyautata mazaunina. Lalle ne shĩ, mãsu zãlunci ba su cin nasara!"
وَلَقَدْ هَمَّتْ بِهِۦ ۖ وَهَمَّ بِهَا لَوْلَآ أَن رَّءَا بُرْهَـٰنَ رَبِّهِۦ ۚ كَذَٰلِكَ لِنَصْرِفَ عَنْهُ ٱلسُّوٓءَ وَٱلْفَحْشَآءَ ۚ إِنَّهُۥ مِنْ عِبَادِنَا ٱلْمُخْلَصِينَ
walaqad hammat bihi wahamma bihā lawlā an raā bur'hāna rabbihi kadhālika linaṣrifa ʿanhu l-sūa wal-faḥshāa innahu min ʿibādinā l-mukh'laṣīna
Kuma lalle ne, tã himmantu da shi. Kuma yã himmantu da ita in bã dõmin ya ga dalĩlin Ubangijinsa ba. Kãmar haka dai, dõmin Mu karkatar da mummũnan aiki da alfãsha daga gare shi. Lalle ne shi, daga bãyinMu zaɓaɓɓu yake.
وَٱسْتَبَقَا ٱلْبَابَ وَقَدَّتْ قَمِيصَهُۥ مِن دُبُرٍۢ وَأَلْفَيَا سَيِّدَهَا لَدَا ٱلْبَابِ ۚ قَالَتْ مَا جَزَآءُ مَنْ أَرَادَ بِأَهْلِكَ سُوٓءًا إِلَّآ أَن يُسْجَنَ أَوْ عَذَابٌ أَلِيمٌۭ
wa-is'tabaqā l-bāba waqaddat qamīṣahu min duburin wa-alfayā sayyidahā ladā l-bābi qālat mā jazāu man arāda bi-ahlika sūan illā an yus'jana aw ʿadhābun alīmun
Kuma suka yi tsẽre1 zuwa ga ƙõfa. Sai ta tsãge rigarsa daga bãya, kuma suka iske mijinta a wurin ƙõfar. Ta ce: "Mẽnene sakamakon wanda ya yi nufin cũta game da iyãlinka? Fãce a ɗaure shi, ko kuwa a yi masa wata azãba mai raɗaɗi."
قَالَ هِىَ رَٰوَدَتْنِى عَن نَّفْسِى ۚ وَشَهِدَ شَاهِدٌۭ مِّنْ أَهْلِهَآ إِن كَانَ قَمِيصُهُۥ قُدَّ مِن قُبُلٍۢ فَصَدَقَتْ وَهُوَ مِنَ ٱلْكَـٰذِبِينَ
qāla hiya rāwadatnī ʿan nafsī washahida shāhidun min ahlihā in kāna qamīṣuhu qudda min qubulin faṣadaqat wahuwa mina l-kādhibīna
Ya ce: "Ita ce ta nẽme ni a kaina."Kuma wani mai shaida daga mutãnenta ya bãyar da shaida: 1"Idan rigarsa ta kasance an tsage ta daga gaba, to, tã yi gaskiya, kuma shĩ ne daga maƙaryata."
وَإِن كَانَ قَمِيصُهُۥ قُدَّ مِن دُبُرٍۢ فَكَذَبَتْ وَهُوَ مِنَ ٱلصَّـٰدِقِينَ
wa-in kāna qamīṣuhu qudda min duburin fakadhabat wahuwa mina l-ṣādiqīna
"Kuma idan rigarsa ta kasance an tsãge ta daga bãya, to, tã yi ƙarya, kuma shĩ ne daga mãsu gaskiya."
فَلَمَّا رَءَا قَمِيصَهُۥ قُدَّ مِن دُبُرٍۢ قَالَ إِنَّهُۥ مِن كَيْدِكُنَّ ۖ إِنَّ كَيْدَكُنَّ عَظِيمٌۭ
falammā raā qamīṣahu qudda min duburin qāla innahu min kaydikunna inna kaydakunna ʿaẓīmun
Sa'an nan a lõkacin da ya ga rĩgarsa an tsãge ta daga bãya, ya ce: "Lalle ne shi, daga kaidinku ne, mata! Lalle ne kaidinku mai girma ne!"
يُوسُفُ أَعْرِضْ عَنْ هَـٰذَا ۚ وَٱسْتَغْفِرِى لِذَنۢبِكِ ۖ إِنَّكِ كُنتِ مِنَ ٱلْخَاطِـِٔينَ
yūsufu aʿriḍ ʿan hādhā wa-is'taghfirī lidhanbiki innaki kunti mina l-khāṭiīna
"Yusufu! Ka kau da kai daga wannan. Kuma ki nẽmi gãfara1 dõmin laifinki. Lalle ne ke, kin kasance daga mãsu kuskure."
۞ وَقَالَ نِسْوَةٌۭ فِى ٱلْمَدِينَةِ ٱمْرَأَتُ ٱلْعَزِيزِ تُرَٰوِدُ فَتَىٰهَا عَن نَّفْسِهِۦ ۖ قَدْ شَغَفَهَا حُبًّا ۖ إِنَّا لَنَرَىٰهَا فِى ضَلَـٰلٍۢ مُّبِينٍۢ
waqāla nis'watun fī l-madīnati im'ra-atu l-ʿazīzi turāwidu fatāhā ʿan nafsihi qad shaghafahā ḥubban innā lanarāhā fī ḍalālin mubīnin
Kuma waɗansu mãtã1 a cikin Birnin suka ce: "Matar Azĩz tanã nẽman hãdiminta daga kansa! Haƙĩƙa, yã rufe zũciyarta da so. Lalle ne mũ, Munã ganin taa cikin ɓata bayyanãnna."
فَلَمَّا سَمِعَتْ بِمَكْرِهِنَّ أَرْسَلَتْ إِلَيْهِنَّ وَأَعْتَدَتْ لَهُنَّ مُتَّكَـًۭٔا وَءَاتَتْ كُلَّ وَٰحِدَةٍۢ مِّنْهُنَّ سِكِّينًۭا وَقَالَتِ ٱخْرُجْ عَلَيْهِنَّ ۖ فَلَمَّا رَأَيْنَهُۥٓ أَكْبَرْنَهُۥ وَقَطَّعْنَ أَيْدِيَهُنَّ وَقُلْنَ حَـٰشَ لِلَّهِ مَا هَـٰذَا بَشَرًا إِنْ هَـٰذَآ إِلَّا مَلَكٌۭ كَرِيمٌۭ
falammā samiʿat bimakrihinna arsalat ilayhinna wa-aʿtadat lahunna muttaka-an waātat kulla wāḥidatin min'hunna sikkīnan waqālati ukh'ruj ʿalayhinna falammā ra-aynahu akbarnahu waqaṭṭaʿna aydiyahunna waqul'na ḥāsha lillahi mā hādhā basharan in hādhā illā malakun karīmun
Sa'an nan a lõkacin da ta ji lãbãri game da mãkircinsu, sai ta aika kiran liyafa zuwa gare su, kuma ta yi tattalin abincin da ake dõgara wajen cinsa, kuma ta bai wa kõwace ɗaya daga cikinsu wuƙa, kuma ta ce: "Ka fito a kansu." To, a lõkacin da, suka gan shi, suka girmamã shi, kuma suka yanyanke hannãyensu, kuma suka ce: "Tsarki yanã ga Allah! Wannan bã mutum ba ne! Wannan bai zama ba fãce Malã'ika ne mai daraja!"
قَالَتْ فَذَٰلِكُنَّ ٱلَّذِى لُمْتُنَّنِى فِيهِ ۖ وَلَقَدْ رَٰوَدتُّهُۥ عَن نَّفْسِهِۦ فَٱسْتَعْصَمَ ۖ وَلَئِن لَّمْ يَفْعَلْ مَآ ءَامُرُهُۥ لَيُسْجَنَنَّ وَلَيَكُونًۭا مِّنَ ٱلصَّـٰغِرِينَ
qālat fadhālikunna alladhī lum'tunnanī fīhi walaqad rāwadttuhu ʿan nafsihi fa-is'taʿṣama wala-in lam yafʿal mā āmuruhu layus'jananna walayakūnan mina l-ṣāghirīna
Ta ce: "To wannan ne fa wanda kuka, zarge1 ni a cikinsa! Kuma lalle ne, haƙẽƙa na nẽme shi daga kansa, sai ya tsare gida, kuma nĩ inã rantsuwa, idan bai aikata abin da nake umurnin sa ba, haƙẽƙa anã ɗaure shi. Haƙĩƙa, yanã kasan, cewa daga ƙasƙantattu."
قَالَ رَبِّ ٱلسِّجْنُ أَحَبُّ إِلَىَّ مِمَّا يَدْعُونَنِىٓ إِلَيْهِ ۖ وَإِلَّا تَصْرِفْ عَنِّى كَيْدَهُنَّ أَصْبُ إِلَيْهِنَّ وَأَكُن مِّنَ ٱلْجَـٰهِلِينَ
qāla rabbi l-sij'nu aḥabbu ilayya mimmā yadʿūnanī ilayhi wa-illā taṣrif ʿannī kaydahunna aṣbu ilayhinna wa-akun mina l-jāhilīna
Ya ce: "Yã Ubangijina! Kurkuku ne mafi sõyuwa a gare ni daga abin da suke kirã na zuwa gare shi. Kuma idan ba Ka karkatar da kaidinsu daga gare ni ba, zan karkata zuwa gare su, kuma in kasance daga jãhilai."
فَٱسْتَجَابَ لَهُۥ رَبُّهُۥ فَصَرَفَ عَنْهُ كَيْدَهُنَّ ۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلْعَلِيمُ
fa-is'tajāba lahu rabbuhu faṣarafa ʿanhu kaydahunna innahu huwa l-samīʿu l-ʿalīmu
Sai Ubangijinsa Ya karɓa masa sabõda haka Ya karkatar da kaidinsu daga gare shi. Lalle Shĩ ne Mai jĩ, Masani.
ثُمَّ بَدَا لَهُم مِّنۢ بَعْدِ مَا رَأَوُا۟ ٱلْـَٔايَـٰتِ لَيَسْجُنُنَّهُۥ حَتَّىٰ حِينٍۢ
thumma badā lahum min baʿdi mā ra-awū l-āyāti layasjununnahu ḥattā ḥīnin
Sa'an nan kuma ya bayyana a gare su a bãyan sun ga alãmõmin, lalle ne dai su ɗaure shi har zuwa wani lõkaci.
وَدَخَلَ مَعَهُ ٱلسِّجْنَ فَتَيَانِ ۖ قَالَ أَحَدُهُمَآ إِنِّىٓ أَرَىٰنِىٓ أَعْصِرُ خَمْرًۭا ۖ وَقَالَ ٱلْـَٔاخَرُ إِنِّىٓ أَرَىٰنِىٓ أَحْمِلُ فَوْقَ رَأْسِى خُبْزًۭا تَأْكُلُ ٱلطَّيْرُ مِنْهُ ۖ نَبِّئْنَا بِتَأْوِيلِهِۦٓ ۖ إِنَّا نَرَىٰكَ مِنَ ٱلْمُحْسِنِينَ
wadakhala maʿahu l-sij'na fatayāni qāla aḥaduhumā innī arānī aʿṣiru khamran waqāla l-ākharu innī arānī aḥmilu fawqa rasī khub'zan takulu l-ṭayru min'hu nabbi'nā bitawīlihi innā narāka mina l-muḥ'sinīna
Kuma waɗansu samãri biyu suka shiga kurkuku tãre da shi.1 ¦ayansu ya ce: "Lalle ne nĩ, nã yi mafarkin gã ni inã mãtsar giya." Kuma ɗayan ya ce: "Lalle ne nĩ, nã yi Mafarkin gã ni inã ɗauke da waina a bisa kaina, tsuntsãye sunã ci daga gare ta. Ka bã mu lãbãri game da fassararsu. Lalle ne mũ, Munã ganin ka daga mãsu kyautatãwa."
قَالَ لَا يَأْتِيكُمَا طَعَامٌۭ تُرْزَقَانِهِۦٓ إِلَّا نَبَّأْتُكُمَا بِتَأْوِيلِهِۦ قَبْلَ أَن يَأْتِيَكُمَا ۚ ذَٰلِكُمَا مِمَّا عَلَّمَنِى رَبِّىٓ ۚ إِنِّى تَرَكْتُ مِلَّةَ قَوْمٍۢ لَّا يُؤْمِنُونَ بِٱللَّهِ وَهُم بِٱلْـَٔاخِرَةِ هُمْ كَـٰفِرُونَ
qāla lā yatīkumā ṭaʿāmun tur'zaqānihi illā nabbatukumā bitawīlihi qabla an yatiyakumā dhālikumā mimmā ʿallamanī rabbī innī taraktu millata qawmin lā yu'minūna bil-lahi wahum bil-ākhirati hum kāfirūna
Ya ce: "Wani abinci bã zai zo muku ba wanda ake azurtã ku da shi fãce nã bã ku lãbãrin fassararsa,1 kãfin ya zo muku. Wannan kuwa yanã daga abin da Ubangijĩna Ya sanar da ni. Lalle ne nĩ nã bar addinin mutãne waɗanda ba su yi ĩmãni da Allah ba, kuma game da lãhira, sũ kãfirai ne."
وَٱتَّبَعْتُ مِلَّةَ ءَابَآءِىٓ إِبْرَٰهِيمَ وَإِسْحَـٰقَ وَيَعْقُوبَ ۚ مَا كَانَ لَنَآ أَن نُّشْرِكَ بِٱللَّهِ مِن شَىْءٍۢ ۚ ذَٰلِكَ مِن فَضْلِ ٱللَّهِ عَلَيْنَا وَعَلَى ٱلنَّاسِ وَلَـٰكِنَّ أَكْثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَشْكُرُونَ
wa-ittabaʿtu millata ābāī ib'rāhīma wa-is'ḥāqa wayaʿqūba mā kāna lanā an nush'rika bil-lahi min shayin dhālika min faḍli l-lahi ʿalaynā waʿalā l-nāsi walākinna akthara l-nāsi lā yashkurūna
"Kuma na bi addinin iyayẽna, Ibrãhĩm da Is'hãka da Yãƙũba. Bã ya yiwuwa a gare mu mu yi shirka da Allah da kõme. Wannan yana daga falalar Allah a kanmu da mutãne, amma mafi yawan mutãne bã su gõdewa."
يَـٰصَـٰحِبَىِ ٱلسِّجْنِ ءَأَرْبَابٌۭ مُّتَفَرِّقُونَ خَيْرٌ أَمِ ٱللَّهُ ٱلْوَٰحِدُ ٱلْقَهَّارُ
yāṣāḥibayi l-sij'ni a-arbābun mutafarriqūna khayrun ami l-lahu l-wāḥidu l-qahāru
"Yã abõkaina biyu na kurkuku! Shin iyãyen giji dabam-dabam ne mafiya alhẽri kõ kuwa Allah Makaɗaici Mai tanƙwasãwa?"
مَا تَعْبُدُونَ مِن دُونِهِۦٓ إِلَّآ أَسْمَآءًۭ سَمَّيْتُمُوهَآ أَنتُمْ وَءَابَآؤُكُم مَّآ أَنزَلَ ٱللَّهُ بِهَا مِن سُلْطَـٰنٍ ۚ إِنِ ٱلْحُكْمُ إِلَّا لِلَّهِ ۚ أَمَرَ أَلَّا تَعْبُدُوٓا۟ إِلَّآ إِيَّاهُ ۚ ذَٰلِكَ ٱلدِّينُ ٱلْقَيِّمُ وَلَـٰكِنَّ أَكْثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَعْلَمُونَ
mā taʿbudūna min dūnihi illā asmāan sammaytumūhā antum waābāukum mā anzala l-lahu bihā min sul'ṭānin ini l-ḥuk'mu illā lillahi amara allā taʿbudū illā iyyāhu dhālika l-dīnu l-qayimu walākinna akthara l-nāsi lā yaʿlamūna
"Ba ku bauta wa kõme, baicinSa, fãce waɗansu sũnãye waɗanda kuka ambace su, kũ da ubanninku. Allah bai saukar da wani dalĩli ba game da su. Bãbu hukunci fãce na Allah. Ya yi umurnin kada ku bauta wa kõwa fãce Shi. Wancan ne addini madaidaici, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba."
يَـٰصَـٰحِبَىِ ٱلسِّجْنِ أَمَّآ أَحَدُكُمَا فَيَسْقِى رَبَّهُۥ خَمْرًۭا ۖ وَأَمَّا ٱلْـَٔاخَرُ فَيُصْلَبُ فَتَأْكُلُ ٱلطَّيْرُ مِن رَّأْسِهِۦ ۚ قُضِىَ ٱلْأَمْرُ ٱلَّذِى فِيهِ تَسْتَفْتِيَانِ
yāṣāḥibayi l-sij'ni ammā aḥadukumā fayasqī rabbahu khamran wa-ammā l-ākharu fayuṣ'labu fatakulu l-ṭayru min rasihi quḍiya l-amru alladhī fīhi tastaftiyāni
"Yã abõkaina biyu, na kurkuku! Amma ɗayanku, to, zai shãyar da uban gidansa giya, kuma gudan, to, zã a tsĩrẽ shi, sa'an nan tsuntsãye su ci daga kansa. An hukunta al'amarin, wanda a cikinsa kuke yin fatawa."
وَقَالَ لِلَّذِى ظَنَّ أَنَّهُۥ نَاجٍۢ مِّنْهُمَا ٱذْكُرْنِى عِندَ رَبِّكَ فَأَنسَىٰهُ ٱلشَّيْطَـٰنُ ذِكْرَ رَبِّهِۦ فَلَبِثَ فِى ٱلسِّجْنِ بِضْعَ سِنِينَ
waqāla lilladhī ẓanna annahu nājin min'humā udh'kur'nī ʿinda rabbika fa-ansāhu l-shayṭānu dhik'ra rabbihi falabitha fī l-sij'ni biḍ'ʿa sinīna
Kuma ya ce da wanda ya tabbatar da cẽwa shi mai kuɓuta ne daga gare su, "Ka ambacẽ ni a wurin uban gidanka." Sai Shaiɗan ya mantar da shi tunãwar Ubangijinsa, sabõda haka ya zauna a cikin kurkuku 'yan shekaru.
وَقَالَ ٱلْمَلِكُ إِنِّىٓ أَرَىٰ سَبْعَ بَقَرَٰتٍۢ سِمَانٍۢ يَأْكُلُهُنَّ سَبْعٌ عِجَافٌۭ وَسَبْعَ سُنۢبُلَـٰتٍ خُضْرٍۢ وَأُخَرَ يَابِسَـٰتٍۢ ۖ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلْمَلَأُ أَفْتُونِى فِى رُءْيَـٰىَ إِن كُنتُمْ لِلرُّءْيَا تَعْبُرُونَ
waqāla l-maliku innī arā sabʿa baqarātin simānin yakuluhunna sabʿun ʿijāfun wasabʿa sunbulātin khuḍ'rin wa-ukhara yābisātin yāayyuhā l-mala-u aftūnī fī ru'yāya in kuntum lilrru'yā taʿburūna
Kuma sarki ya ce: "Lalle ne, nã yi mafarki1; nã ga shãnu bakwai mãsu ƙiba, waɗansu bakwai rãmammu, sunã cin su, da zangarku bakwai kõre-kõre da waɗansu ƙeƙasassu. Yã kũ jama'a! Ku yi mini fatawa a cikin mafarkĩna, idan kun kasance ga mafarki kunã fassarawa."
قَالُوٓا۟ أَضْغَـٰثُ أَحْلَـٰمٍۢ ۖ وَمَا نَحْنُ بِتَأْوِيلِ ٱلْأَحْلَـٰمِ بِعَـٰلِمِينَ
qālū aḍghāthu aḥlāmin wamā naḥnu bitawīli l-aḥlāmi biʿālimīna
Suka ce: "Yãye-yãyen mafarki ne, kuma ba mu zamo masana ga fassarar yãye-yãyen mafarki ba."
وَقَالَ ٱلَّذِى نَجَا مِنْهُمَا وَٱدَّكَرَ بَعْدَ أُمَّةٍ أَنَا۠ أُنَبِّئُكُم بِتَأْوِيلِهِۦ فَأَرْسِلُونِ
waqāla alladhī najā min'humā wa-iddakara baʿda ummatin anā unabbi-ukum bitawīlihi fa-arsilūni
Kuma wannan da ya kuɓuta daga cikinsu ya ce: a bãyan yã yi tunãni a lõkaci mai tsawo, "Nĩ, inã bã ku lãbãri game da fassararsa. Sai ku aike ni."
يُوسُفُ أَيُّهَا ٱلصِّدِّيقُ أَفْتِنَا فِى سَبْعِ بَقَرَٰتٍۢ سِمَانٍۢ يَأْكُلُهُنَّ سَبْعٌ عِجَافٌۭ وَسَبْعِ سُنۢبُلَـٰتٍ خُضْرٍۢ وَأُخَرَ يَابِسَـٰتٍۢ لَّعَلِّىٓ أَرْجِعُ إِلَى ٱلنَّاسِ لَعَلَّهُمْ يَعْلَمُونَ
yūsufu ayyuhā l-ṣidīqu aftinā fī sabʿi baqarātin simānin yakuluhunna sabʿun ʿijāfun wasabʿi sunbulātin khuḍ'rin wa-ukhara yābisātin laʿallī arjiʿu ilā l-nāsi laʿallahum yaʿlamūna
"Yã Yũsufu! Yã kai mai yawan gaskiya! Ka yi mana fatawa a cikin shãnu bakwai mãsu ƙiba, waɗansu bakwai rãmammu sunã cin su, da zangarku bakwai kõrãye da waɗansu ƙẽƙasassu, tsammãnĩna in kõma ga mutãne, tsammãninsu zã su sani."
قَالَ تَزْرَعُونَ سَبْعَ سِنِينَ دَأَبًۭا فَمَا حَصَدتُّمْ فَذَرُوهُ فِى سُنۢبُلِهِۦٓ إِلَّا قَلِيلًۭا مِّمَّا تَأْكُلُونَ
qāla tazraʿūna sabʿa sinīna da-aban famā ḥaṣadttum fadharūhu fī sunbulihi illā qalīlan mimmā takulūna
Ya ce: "Kunã shũka, shẽkara bakwai tutur, sa'an nan abin da kuka girbe, sai ku bar shi, a cikin zanganniyarsa,1 sai kaɗan daga abin da kuke ci."
ثُمَّ يَأْتِى مِنۢ بَعْدِ ذَٰلِكَ سَبْعٌۭ شِدَادٌۭ يَأْكُلْنَ مَا قَدَّمْتُمْ لَهُنَّ إِلَّا قَلِيلًۭا مِّمَّا تُحْصِنُونَ
thumma yatī min baʿdi dhālika sabʿun shidādun yakul'na mā qaddamtum lahunna illā qalīlan mimmā tuḥ'ṣinūna
"Sa'an nan kuma waɗansu bakwai mãsu tsanani su zo daga hãyan wancan, su cinye abin da kuka gabãtar dõminsu, fãce kaɗan daga abin da kuke ãdanãwa."
ثُمَّ يَأْتِى مِنۢ بَعْدِ ذَٰلِكَ عَامٌۭ فِيهِ يُغَاثُ ٱلنَّاسُ وَفِيهِ يَعْصِرُونَ
thumma yatī min baʿdi dhālika ʿāmun fīhi yughāthu l-nāsu wafīhi yaʿṣirūna
"Sa'an nan kuma wata shẽkara ta zo daga bãyan wancan, a cikinta ake yi wa mutãne ruwa mai albarka, kuma a cikinta suke mãtsar abin sha."
وَقَالَ ٱلْمَلِكُ ٱئْتُونِى بِهِۦ ۖ فَلَمَّا جَآءَهُ ٱلرَّسُولُ قَالَ ٱرْجِعْ إِلَىٰ رَبِّكَ فَسْـَٔلْهُ مَا بَالُ ٱلنِّسْوَةِ ٱلَّـٰتِى قَطَّعْنَ أَيْدِيَهُنَّ ۚ إِنَّ رَبِّى بِكَيْدِهِنَّ عَلِيمٌۭ
waqāla l-maliku i'tūnī bihi falammā jāahu l-rasūlu qāla ir'jiʿ ilā rabbika fasalhu mā bālu l-nis'wati allātī qaṭṭaʿna aydiyahunna inna rabbī bikaydihinna ʿalīmun
Kuma sarkin ya ce: "Ku zo mini da shi." To, a lõkacin da manzo ya je masa (Yũsufu), ya ce: "Ka kõma zuwa ga uban gidanka, sa' an nan ka tambaye shi; Mẽnene hãlin mãtãyen nan waɗanda suka yanyanke hannãyensu? Lalle ne Ubangijĩna ne Masani game da kaidin su."
قَالَ مَا خَطْبُكُنَّ إِذْ رَٰوَدتُّنَّ يُوسُفَ عَن نَّفْسِهِۦ ۚ قُلْنَ حَـٰشَ لِلَّهِ مَا عَلِمْنَا عَلَيْهِ مِن سُوٓءٍۢ ۚ قَالَتِ ٱمْرَأَتُ ٱلْعَزِيزِ ٱلْـَٔـٰنَ حَصْحَصَ ٱلْحَقُّ أَنَا۠ رَٰوَدتُّهُۥ عَن نَّفْسِهِۦ وَإِنَّهُۥ لَمِنَ ٱلصَّـٰدِقِينَ
qāla mā khaṭbukunna idh rāwadttunna yūsufa ʿan nafsihi qul'na ḥāsha lillahi mā ʿalim'nā ʿalayhi min sūin qālati im'ra-atu l-ʿazīzi l-āna ḥaṣḥaṣa l-ḥaqu anā rāwadttuhu ʿan nafsihi wa-innahu lamina l-ṣādiqīna
Ya ce: "Mẽne ne babban al'amarinku, a lõkacin da kaka nẽmi Yũsufu daga kansa?" Suka ce: "Tsarki ga Allah yake! Ba mu san wani mummũnan aiki a kansaba." Mãtar Azĩz ta ce: "Yanzu fagaskiya1 ta bayyana. Nĩ ce nã nẽme shi daga kansa. Kuma lalle ne shĩ, haƙĩƙa, yanã daga mãsu gaskiya.
ذَٰلِكَ لِيَعْلَمَ أَنِّى لَمْ أَخُنْهُ بِٱلْغَيْبِ وَأَنَّ ٱللَّهَ لَا يَهْدِى كَيْدَ ٱلْخَآئِنِينَ
dhālika liyaʿlama annī lam akhun'hu bil-ghaybi wa-anna l-laha lā yahdī kayda l-khāinīna
"Wancan ne, dõmin ya san cẽwa lalle ne ni ban yaudareshi ba a ɓõye, kuma lalle Allah bã Ya shiryar da kaidin mayaudara."
۞ وَمَآ أُبَرِّئُ نَفْسِىٓ ۚ إِنَّ ٱلنَّفْسَ لَأَمَّارَةٌۢ بِٱلسُّوٓءِ إِلَّا مَا رَحِمَ رَبِّىٓ ۚ إِنَّ رَبِّى غَفُورٌۭ رَّحِيمٌۭ
wamā ubarri-u nafsī inna l-nafsa la-ammāratun bil-sūi illā mā raḥima rabbī inna rabbī ghafūrun raḥīmun
"Kuma bã ni kuɓutar da kaina. Lalle ne rai, haƙĩƙa, mai yawan umurni ne da mummũnan aiki, fãce abin da Ubangjina Ya yi na; rahama. Lalle Ubangjina Mai gãfara ne, Mai jin ƙai."
وَقَالَ ٱلْمَلِكُ ٱئْتُونِى بِهِۦٓ أَسْتَخْلِصْهُ لِنَفْسِى ۖ فَلَمَّا كَلَّمَهُۥ قَالَ إِنَّكَ ٱلْيَوْمَ لَدَيْنَا مَكِينٌ أَمِينٌۭ
waqāla l-maliku i'tūnī bihi astakhliṣ'hu linafsī falammā kallamahu qāla innaka l-yawma ladaynā makīnun amīnun
Kuma sarkin ya ce: "Ku zo mini da shi in kẽɓe shi ga kaina." To, a lõkacin da Yũsufu ya yi masa magana sai ya ce: "Lalle ne kai a yau, a gunmu, mai daraja ne, amintacce."1
قَالَ ٱجْعَلْنِى عَلَىٰ خَزَآئِنِ ٱلْأَرْضِ ۖ إِنِّى حَفِيظٌ عَلِيمٌۭ
qāla ij'ʿalnī ʿalā khazāini l-arḍi innī ḥafīẓun ʿalīmun
Ya ce: "Ka sanya ni a kan taskõkin ƙasa. Lalle ne nĩ, mai tsarẽwa ne, kuma masani."
وَكَذَٰلِكَ مَكَّنَّا لِيُوسُفَ فِى ٱلْأَرْضِ يَتَبَوَّأُ مِنْهَا حَيْثُ يَشَآءُ ۚ نُصِيبُ بِرَحْمَتِنَا مَن نَّشَآءُ ۖ وَلَا نُضِيعُ أَجْرَ ٱلْمُحْسِنِينَ
wakadhālika makkannā liyūsufa fī l-arḍi yatabawwa-u min'hā ḥaythu yashāu nuṣību biraḥmatinā man nashāu walā nuḍīʿu ajra l-muḥ'sinīna
Kuma kamar wancan ne Muka bãyar da ĩko ga Yũsufu a cikin ƙasa1 yanã sauka a inda duk yake so. Munã sãmun wanda Muke so da rahamar Mu, kuma bã Mu tõzartar da lãdar mãsu kyautatawa.
وَلَأَجْرُ ٱلْـَٔاخِرَةِ خَيْرٌۭ لِّلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَكَانُوا۟ يَتَّقُونَ
wala-ajru l-ākhirati khayrun lilladhīna āmanū wakānū yattaqūna
Kuma lalle lãdar Lãhira ce mafi alhẽri ga waɗandasuka yi ĩmãni, kuma suka kasance mãsu taƙawa.
وَجَآءَ إِخْوَةُ يُوسُفَ فَدَخَلُوا۟ عَلَيْهِ فَعَرَفَهُمْ وَهُمْ لَهُۥ مُنكِرُونَ
wajāa ikh'watu yūsufa fadakhalū ʿalayhi faʿarafahum wahum lahu munkirūna
Kuma 'yan'uwan1 Yũsufu suka jẽ, sa'an nan suka shiga a gare shi, sai ya gãne su, alhãli kuwa su, sunã mãsu musunsa.
وَلَمَّا جَهَّزَهُم بِجَهَازِهِمْ قَالَ ٱئْتُونِى بِأَخٍۢ لَّكُم مِّنْ أَبِيكُمْ ۚ أَلَا تَرَوْنَ أَنِّىٓ أُوفِى ٱلْكَيْلَ وَأَنَا۠ خَيْرُ ٱلْمُنزِلِينَ
walammā jahhazahum bijahāzihim qāla i'tūnī bi-akhin lakum min abīkum alā tarawna annī ūfī l-kayla wa-anā khayru l-munzilīna
Kuma a lõkacin da ya yi musu tattali da tattalinsu, ya ce: "Ku zo mini da wani ɗan'uwa nãku daga ubanku. Ba ku gani ba cẽwa lalle ne nĩ, inã cika ma'auni, kuma nĩ ne mafi alhẽrin mãsu saukarwa?"
فَإِن لَّمْ تَأْتُونِى بِهِۦ فَلَا كَيْلَ لَكُمْ عِندِى وَلَا تَقْرَبُونِ
fa-in lam tatūnī bihi falā kayla lakum ʿindī walā taqrabūni
"Sa'an nan idan ba ku zo mini da shĩ ba, to, bãbu awoa gare ku a wurĩna, kuma kada ku, kasance ni."
قَالُوا۟ سَنُرَٰوِدُ عَنْهُ أَبَاهُ وَإِنَّا لَفَـٰعِلُونَ
qālū sanurāwidu ʿanhu abāhu wa-innā lafāʿilūna
Suka ce: "Zã mu nẽme shi daga ubansa. Kuma lalle ne mũ, haƙĩƙa, mãsu aikatãwa ne."
وَقَالَ لِفِتْيَـٰنِهِ ٱجْعَلُوا۟ بِضَـٰعَتَهُمْ فِى رِحَالِهِمْ لَعَلَّهُمْ يَعْرِفُونَهَآ إِذَا ٱنقَلَبُوٓا۟ إِلَىٰٓ أَهْلِهِمْ لَعَلَّهُمْ يَرْجِعُونَ
waqāla lifit'yānihi ij'ʿalū biḍāʿatahum fī riḥālihim laʿallahum yaʿrifūnahā idhā inqalabū ilā ahlihim laʿallahum yarjiʿūna
Kuma ya ce wa yaransa, "Ku sanya hajjarsu a cikin kãyansu, tsammãninsu sunã gãne ta idan sun jũya zuwa ga mutãnensu, tsammã ninsu, zã su kõmo."
فَلَمَّا رَجَعُوٓا۟ إِلَىٰٓ أَبِيهِمْ قَالُوا۟ يَـٰٓأَبَانَا مُنِعَ مِنَّا ٱلْكَيْلُ فَأَرْسِلْ مَعَنَآ أَخَانَا نَكْتَلْ وَإِنَّا لَهُۥ لَحَـٰفِظُونَ
falammā rajaʿū ilā abīhim qālū yāabānā muniʿa minnā l-kaylu fa-arsil maʿanā akhānā naktal wa-innā lahu laḥāfiẓūna
To, a lõkacin da suka kõma zuwa ga ubansu, suka ce: "Yã bãbanmu! An hana mu awo sai ka aika ɗan'uwanmu tãre da mu. Zã mu yi awo. Kuma lalle ne, haƙĩƙa mũ, mãsu lũra da Shi ne."
قَالَ هَلْ ءَامَنُكُمْ عَلَيْهِ إِلَّا كَمَآ أَمِنتُكُمْ عَلَىٰٓ أَخِيهِ مِن قَبْلُ ۖ فَٱللَّهُ خَيْرٌ حَـٰفِظًۭا ۖ وَهُوَ أَرْحَمُ ٱلرَّٰحِمِينَ
qāla hal āmanukum ʿalayhi illā kamā amintukum ʿalā akhīhi min qablu fal-lahu khayrun ḥāfiẓan wahuwa arḥamu l-rāḥimīna
Ya ce: "Ashe, zã ni amince muku a kansa? Fãce dai kamar yadda na amince muku a kan ɗan'uwansa daga gabãni, sai dai Allah ne Mafĩfĩcin mãsu tsari, kuma Shĩ ne Mafi rahamar mãsu rahama."
وَلَمَّا فَتَحُوا۟ مَتَـٰعَهُمْ وَجَدُوا۟ بِضَـٰعَتَهُمْ رُدَّتْ إِلَيْهِمْ ۖ قَالُوا۟ يَـٰٓأَبَانَا مَا نَبْغِى ۖ هَـٰذِهِۦ بِضَـٰعَتُنَا رُدَّتْ إِلَيْنَا ۖ وَنَمِيرُ أَهْلَنَا وَنَحْفَظُ أَخَانَا وَنَزْدَادُ كَيْلَ بَعِيرٍۢ ۖ ذَٰلِكَ كَيْلٌۭ يَسِيرٌۭ
walammā fataḥū matāʿahum wajadū biḍāʿatahum ruddat ilayhim qālū yāabānā mā nabghī hādhihi biḍāʿatunā ruddat ilaynā wanamīru ahlanā wanaḥfaẓu akhānā wanazdādu kayla baʿīrin dhālika kaylun yasīrun
Kuma a lõkacin da suka bũɗe kãyansu, suka sãmi hajjarsu an mayar musu da ita, suka ce: "Yã bãbanmu! Ba mu zãlunci! Wannan hajjarmu ce an mayar mana da ita, kuma mu nẽmo wa iyalinmu abinci, kuma mu kiyãye ɗan'uwanmu, kuma mu ƙãra awon kãyan rãƙumi guda, wancan awo ne mai sauki."
قَالَ لَنْ أُرْسِلَهُۥ مَعَكُمْ حَتَّىٰ تُؤْتُونِ مَوْثِقًۭا مِّنَ ٱللَّهِ لَتَأْتُنَّنِى بِهِۦٓ إِلَّآ أَن يُحَاطَ بِكُمْ ۖ فَلَمَّآ ءَاتَوْهُ مَوْثِقَهُمْ قَالَ ٱللَّهُ عَلَىٰ مَا نَقُولُ وَكِيلٌۭ
qāla lan ur'silahu maʿakum ḥattā tu'tūni mawthiqan mina l-lahi latatunnanī bihi illā an yuḥāṭa bikum falammā ātawhu mawthiqahum qāla l-lahu ʿalā mā naqūlu wakīlun
Ya ce: "Bã zan sake shi tãre da kũ ba, sai kun kawo mini alkawarinku baga Allah, haƙĩƙa, kunã dawo mini da shi, sai fa idan an kẽwaye ku." To, a, lõkacinda suka yi mãsa alkawari, ya ce: "Allah ne wakĩli a kan abin da muke faɗa."
وَقَالَ يَـٰبَنِىَّ لَا تَدْخُلُوا۟ مِنۢ بَابٍۢ وَٰحِدٍۢ وَٱدْخُلُوا۟ مِنْ أَبْوَٰبٍۢ مُّتَفَرِّقَةٍۢ ۖ وَمَآ أُغْنِى عَنكُم مِّنَ ٱللَّهِ مِن شَىْءٍ ۖ إِنِ ٱلْحُكْمُ إِلَّا لِلَّهِ ۖ عَلَيْهِ تَوَكَّلْتُ ۖ وَعَلَيْهِ فَلْيَتَوَكَّلِ ٱلْمُتَوَكِّلُونَ
waqāla yābaniyya lā tadkhulū min bābin wāḥidin wa-ud'khulū min abwābin mutafarriqatin wamā ugh'nī ʿankum mina l-lahi min shayin ini l-ḥuk'mu illā lillahi ʿalayhi tawakkaltu waʿalayhi falyatawakkali l-mutawakilūna
Kuma ya ce: "Yã ɗiyana! Kada ku shiga ta ƙõfa guda, ku shiga ta ƙõfõfi dabam-dabam,1 kuma bã na wadãtar muku kõme daga Allah. Bãbu hukunci fãce daga Allah, a gare Shi na dõgara, kuma a gare Shi mãsu dõgara sai su dõgara."
وَلَمَّا دَخَلُوا۟ مِنْ حَيْثُ أَمَرَهُمْ أَبُوهُم مَّا كَانَ يُغْنِى عَنْهُم مِّنَ ٱللَّهِ مِن شَىْءٍ إِلَّا حَاجَةًۭ فِى نَفْسِ يَعْقُوبَ قَضَىٰهَا ۚ وَإِنَّهُۥ لَذُو عِلْمٍۢ لِّمَا عَلَّمْنَـٰهُ وَلَـٰكِنَّ أَكْثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَعْلَمُونَ
walammā dakhalū min ḥaythu amarahum abūhum mā kāna yugh'nī ʿanhum mina l-lahi min shayin illā ḥājatan fī nafsi yaʿqūba qaḍāhā wa-innahu ladhū ʿil'min limā ʿallamnāhu walākinna akthara l-nāsi lā yaʿlamūna
Kuma a lõkacin da suka shiga daga inda ubansu ya umurce su wani abu bai kasance yanã wadãtarwa ga barinsu daga Allah ba fãce wata bukata ce a ran Yãƙũbu, ya bayyana ta. Kuma lalle ne shĩ, haƙĩƙa, ma'abũcin wani ilmi ne ga abin da Muka sanar da shi, kuma mafi yawan mutãne ba su sani ba.
وَلَمَّا دَخَلُوا۟ عَلَىٰ يُوسُفَ ءَاوَىٰٓ إِلَيْهِ أَخَاهُ ۖ قَالَ إِنِّىٓ أَنَا۠ أَخُوكَ فَلَا تَبْتَئِسْ بِمَا كَانُوا۟ يَعْمَلُونَ
walammā dakhalū ʿalā yūsufa āwā ilayhi akhāhu qāla innī anā akhūka falā tabta-is bimā kānū yaʿmalūna
Kuma a lõkacin da suka shiga wajen Yũsufu, ya tattara ɗan'uwansa zuwa gare shi, ya ce: "Lalle nĩ ne ɗan'uwanka, sabõda haka kada ka yi baƙin ciki da abin da suka kasance sunã aikatãwa."
فَلَمَّا جَهَّزَهُم بِجَهَازِهِمْ جَعَلَ ٱلسِّقَايَةَ فِى رَحْلِ أَخِيهِ ثُمَّ أَذَّنَ مُؤَذِّنٌ أَيَّتُهَا ٱلْعِيرُ إِنَّكُمْ لَسَـٰرِقُونَ
falammā jahhazahum bijahāzihim jaʿala l-siqāyata fī raḥli akhīhi thumma adhana mu-adhinun ayyatuhā l-ʿīru innakum lasāriqūna
Sa'an nan a lõkacin da ya yi musu tattali da tattalinsu, sai ya sanya ma'auni a cikin kãyan ɗan'uwansa sa'an nan kuma mai yẽkuwa ya yi yẽkuwa," Yã kũ ãyari! lalle ne, haƙĩƙa kũ ɓarãyi ne."
قَالُوا۟ وَأَقْبَلُوا۟ عَلَيْهِم مَّاذَا تَفْقِدُونَ
qālū wa-aqbalū ʿalayhim mādhā tafqidūna
Suka ce: kuma suka fuskanta zuwa gare su: "Mẽne ne kuke nẽma?"
قَالُوا۟ نَفْقِدُ صُوَاعَ ٱلْمَلِكِ وَلِمَن جَآءَ بِهِۦ حِمْلُ بَعِيرٍۢ وَأَنَا۠ بِهِۦ زَعِيمٌۭ
qālū nafqidu ṣuwāʿa l-maliki waliman jāa bihi ḥim'lu baʿīrin wa-anā bihi zaʿīmun
Suka ce: "Munã nẽman ma'aunin sarki. Kuma wanda ya zo da shi, yanã da kãyan rãkumi ɗaya, kuma ni ne lãmuni game da shi."
قَالُوا۟ تَٱللَّهِ لَقَدْ عَلِمْتُم مَّا جِئْنَا لِنُفْسِدَ فِى ٱلْأَرْضِ وَمَا كُنَّا سَـٰرِقِينَ
qālū tal-lahi laqad ʿalim'tum mā ji'nā linuf'sida fī l-arḍi wamā kunnā sāriqīna
Suka ce: "Tallahi! Lalle ne, haƙĩƙa, kun sani, ba mu zodon mu yi ɓarna a cikin ƙasa ba, kuma ba mu kasance ɓarãyi ba."
قَالُوا۟ فَمَا جَزَٰٓؤُهُۥٓ إِن كُنتُمْ كَـٰذِبِينَ
qālū famā jazāuhu in kuntum kādhibīna
Suka ce: "To mẽne ne sakamakonsa idan, kun kasance maƙaryata?"
قَالُوا۟ جَزَٰٓؤُهُۥ مَن وُجِدَ فِى رَحْلِهِۦ فَهُوَ جَزَٰٓؤُهُۥ ۚ كَذَٰلِكَ نَجْزِى ٱلظَّـٰلِمِينَ
qālū jazāuhu man wujida fī raḥlihi fahuwa jazāuhu kadhālika najzī l-ẓālimīna
Suka ce: "Sakamakonsa, wanda aka same shi a cikin kãyansa, to, shi ne sakamakonsa,1 kamar wancan ne muke sãka wa azzãlumai."
فَبَدَأَ بِأَوْعِيَتِهِمْ قَبْلَ وِعَآءِ أَخِيهِ ثُمَّ ٱسْتَخْرَجَهَا مِن وِعَآءِ أَخِيهِ ۚ كَذَٰلِكَ كِدْنَا لِيُوسُفَ ۖ مَا كَانَ لِيَأْخُذَ أَخَاهُ فِى دِينِ ٱلْمَلِكِ إِلَّآ أَن يَشَآءَ ٱللَّهُ ۚ نَرْفَعُ دَرَجَـٰتٍۢ مَّن نَّشَآءُ ۗ وَفَوْقَ كُلِّ ذِى عِلْمٍ عَلِيمٌۭ
fabada-a bi-awʿiyatihim qabla wiʿāi akhīhi thumma is'takhrajahā min wiʿāi akhīhi kadhālika kid'nā liyūsufa mā kāna liyakhudha akhāhu fī dīni l-maliki illā an yashāa l-lahu narfaʿu darajātin man nashāu wafawqa kulli dhī ʿil'min ʿalīmun
To, sai ya fãra (bincike) da jikunansu a gabãnin jakar ɗan'uwansa. Sa'an nan ya fitar da ita daga jakar ɗan'uwansa. Kamar wancan muka shirya wa Yũsufu. Bai kasance ya kãma ɗan'uwansa a cikin addinin (dõkõkin) sarki ba, fãce idan Allah Ya so. Munã ɗaukaka darajõji ga wanda Muka so, kuma a saman kõwane ma'abũcin ilmi akwai wani masani.
۞ قَالُوٓا۟ إِن يَسْرِقْ فَقَدْ سَرَقَ أَخٌۭ لَّهُۥ مِن قَبْلُ ۚ فَأَسَرَّهَا يُوسُفُ فِى نَفْسِهِۦ وَلَمْ يُبْدِهَا لَهُمْ ۚ قَالَ أَنتُمْ شَرٌّۭ مَّكَانًۭا ۖ وَٱللَّهُ أَعْلَمُ بِمَا تَصِفُونَ
qālū in yasriq faqad saraqa akhun lahu min qablu fa-asarrahā yūsufu fī nafsihi walam yub'dihā lahum qāla antum sharrun makānan wal-lahu aʿlamu bimā taṣifūna
Suka ce: "Idan ya yi sãta, to, lalle ne wani ɗan'uwansa yã taɓa yin sãta a gabãninsa." Sai Yũsufu ya bõye1 ta a cikin ransa. Kuma bai bayyana ta ba a gare su, ya ce: "Kũ ne mafi sharri ga wuri. Kuma Allah ne Mafi sani daga abin da kuke siffantãwa."
قَالُوا۟ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلْعَزِيزُ إِنَّ لَهُۥٓ أَبًۭا شَيْخًۭا كَبِيرًۭا فَخُذْ أَحَدَنَا مَكَانَهُۥٓ ۖ إِنَّا نَرَىٰكَ مِنَ ٱلْمُحْسِنِينَ
qālū yāayyuhā l-ʿazīzu inna lahu aban shaykhan kabīran fakhudh aḥadanā makānahu innā narāka mina l-muḥ'sinīna
Suka ce: "Yã kai Azĩzu! Lalle ne yanã da wani ubã, tsoho mai daraja, sabõda haka ka kãma ɗayanmu amatsayinsa. Lalle ne mũ, muna ganin ka daga mãsu kyautatãwa."
قَالَ مَعَاذَ ٱللَّهِ أَن نَّأْخُذَ إِلَّا مَن وَجَدْنَا مَتَـٰعَنَا عِندَهُۥٓ إِنَّآ إِذًۭا لَّظَـٰلِمُونَ
qāla maʿādha l-lahi an nakhudha illā man wajadnā matāʿanā ʿindahu innā idhan laẓālimūna
Ya ce: "Allah Ya tsare mu daga mu kãma wani fãce wanda muka sãmi kãyanmu a wurinsa. Lalle ne mũ, a lõkacin nan, haƙĩƙa, azzãlumai ne."
فَلَمَّا ٱسْتَيْـَٔسُوا۟ مِنْهُ خَلَصُوا۟ نَجِيًّۭا ۖ قَالَ كَبِيرُهُمْ أَلَمْ تَعْلَمُوٓا۟ أَنَّ أَبَاكُمْ قَدْ أَخَذَ عَلَيْكُم مَّوْثِقًۭا مِّنَ ٱللَّهِ وَمِن قَبْلُ مَا فَرَّطتُمْ فِى يُوسُفَ ۖ فَلَنْ أَبْرَحَ ٱلْأَرْضَ حَتَّىٰ يَأْذَنَ لِىٓ أَبِىٓ أَوْ يَحْكُمَ ٱللَّهُ لِى ۖ وَهُوَ خَيْرُ ٱلْحَـٰكِمِينَ
falammā is'tayasū min'hu khalaṣū najiyyan qāla kabīruhum alam taʿlamū anna abākum qad akhadha ʿalaykum mawthiqan mina l-lahi wamin qablu mā farraṭtum fī yūsufa falan abraḥa l-arḍa ḥattā yadhana lī abī aw yaḥkuma l-lahu lī wahuwa khayru l-ḥākimīna
Sabõda haka, a lõkacin da suka yanke tsammãni daga gare shi, sai suka fita sunã mãsu gãnãwa.1 Babbansu ya ce: "Shin, ba ku sani ba cẽwa lalle ne ubanku yariƙi alkawari daga Allah a kanku, kuma daga gabanin haka akwai abin da kuka yi na sakaci game da Yũsufu? Sabõda haka, bã zan gushe daga ƙasar nan ba fãce ubana yã yi mini izni, kõ kuwa Allah Ya yi hukunci a gare ni, kuma Shĩ ne Mafi alhẽrin mahukunta."
ٱرْجِعُوٓا۟ إِلَىٰٓ أَبِيكُمْ فَقُولُوا۟ يَـٰٓأَبَانَآ إِنَّ ٱبْنَكَ سَرَقَ وَمَا شَهِدْنَآ إِلَّا بِمَا عَلِمْنَا وَمَا كُنَّا لِلْغَيْبِ حَـٰفِظِينَ
ir'jiʿū ilā abīkum faqūlū yāabānā inna ib'naka saraqa wamā shahid'nā illā bimā ʿalim'nā wamā kunnā lil'ghaybi ḥāfiẓīna
"Ku kõma zuwa ga ubanku, ku gaya masa: Yã bãbanmu, lalle ne ɗanka yã yi sãta, kuma ba mu yi shaida ba fãce da abin da muka sani, kuma ba mu kasance mun san gaibu ba."
وَسْـَٔلِ ٱلْقَرْيَةَ ٱلَّتِى كُنَّا فِيهَا وَٱلْعِيرَ ٱلَّتِىٓ أَقْبَلْنَا فِيهَا ۖ وَإِنَّا لَصَـٰدِقُونَ
wasali l-qaryata allatī kunnā fīhā wal-ʿīra allatī aqbalnā fīhā wa-innā laṣādiqūna
"Kuma ka tambayi alƙarya wadda muka kasance a cikinta da ãyari wanda muka gabãto acikinsa, kuma lalle ne haƙĩƙa, mũ mãsu gaskiya ne."
قَالَ بَلْ سَوَّلَتْ لَكُمْ أَنفُسُكُمْ أَمْرًۭا ۖ فَصَبْرٌۭ جَمِيلٌ ۖ عَسَى ٱللَّهُ أَن يَأْتِيَنِى بِهِمْ جَمِيعًا ۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلْعَلِيمُ ٱلْحَكِيمُ
qāla bal sawwalat lakum anfusukum amran faṣabrun jamīlun ʿasā l-lahu an yatiyanī bihim jamīʿan innahu huwa l-ʿalīmu l-ḥakīmu
Ya ce: "Ã'a, zukatanku sun ƙawãta wani al'amari a gare ku. Sai haƙuri mai kyãwo, akwai tsammãnin Allah Ya zo mini da su gabã ɗaya (Yũsufu da 'yan'uwansa). Lalle ne Shĩ ne Masani, Mai hikima."
وَتَوَلَّىٰ عَنْهُمْ وَقَالَ يَـٰٓأَسَفَىٰ عَلَىٰ يُوسُفَ وَٱبْيَضَّتْ عَيْنَاهُ مِنَ ٱلْحُزْنِ فَهُوَ كَظِيمٌۭ
watawallā ʿanhum waqāla yāasafā ʿalā yūsufa wa-ib'yaḍḍat ʿaynāhu mina l-ḥuz'ni fahuwa kaẓīmun
Kuma ya jũya daga gare su, kuma ya ce: "Yã baƙin cikina a kan Yũsufu!" Kuma idãnunsa suka yi fari sabõda huznu sa'an nan yanã ta haɗẽwar haushi.
قَالُوا۟ تَٱللَّهِ تَفْتَؤُا۟ تَذْكُرُ يُوسُفَ حَتَّىٰ تَكُونَ حَرَضًا أَوْ تَكُونَ مِنَ ٱلْهَـٰلِكِينَ
qālū tal-lahi tafta-u tadhkuru yūsufa ḥattā takūna ḥaraḍan aw takūna mina l-hālikīna
Suka ce: "Tallahi! Bã zã ka gushe ba, kanã ambaton Yũsufu,1 har ka kasance Mai rauni ƙwarai, kõ kuwa ka kasance daga mãsu halaka."
قَالَ إِنَّمَآ أَشْكُوا۟ بَثِّى وَحُزْنِىٓ إِلَى ٱللَّهِ وَأَعْلَمُ مِنَ ٱللَّهِ مَا لَا تَعْلَمُونَ
qāla innamā ashkū bathī waḥuz'nī ilā l-lahi wa-aʿlamu mina l-lahi mā lā taʿlamūna
Ya ce: "Abin sani kawai, inã kai ƙarar baƙin cikĩna da sunõna zuwa ga Allah, kuma na san abin da ba ku sani ba daga Allah."
يَـٰبَنِىَّ ٱذْهَبُوا۟ فَتَحَسَّسُوا۟ مِن يُوسُفَ وَأَخِيهِ وَلَا تَا۟يْـَٔسُوا۟ مِن رَّوْحِ ٱللَّهِ ۖ إِنَّهُۥ لَا يَا۟يْـَٔسُ مِن رَّوْحِ ٱللَّهِ إِلَّا ٱلْقَوْمُ ٱلْكَـٰفِرُونَ
yābaniyya idh'habū fataḥassasū min yūsufa wa-akhīhi walā tāy'asū min rawḥi l-lahi innahu lā yāy'asu min rawḥi l-lahi illā l-qawmu l-kāfirūna
"Yã ɗiyãna! Sai ku tafi ku nẽmo lãbãrin Yũsufu1 da ɗan'uwansa. Kada ku yanke tsammãni daga rahamar Allah. Lalle ne, bãbu Mai yanke tsammãni daga rahamar Allah fãce mutãne kãfirai."
فَلَمَّا دَخَلُوا۟ عَلَيْهِ قَالُوا۟ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلْعَزِيزُ مَسَّنَا وَأَهْلَنَا ٱلضُّرُّ وَجِئْنَا بِبِضَـٰعَةٍۢ مُّزْجَىٰةٍۢ فَأَوْفِ لَنَا ٱلْكَيْلَ وَتَصَدَّقْ عَلَيْنَآ ۖ إِنَّ ٱللَّهَ يَجْزِى ٱلْمُتَصَدِّقِينَ
falammā dakhalū ʿalayhi qālū yāayyuhā l-ʿazīzu massanā wa-ahlanā l-ḍuru waji'nā bibiḍāʿatin muz'jātin fa-awfi lanā l-kayla wataṣaddaq ʿalaynā inna l-laha yajzī l-mutaṣadiqīna
Sa'an nan a lõkacin da suka shiga gare shi suka ce: "Yã kai Azĩzu! Cũta ta shãfe mu, mũ da iyãlinmu, kuma mun zo da wata hãja maras kuma. Sai ka cika mana ma'auni, kuma ka yi sadaka a gare mu. Lalle ne Allah Yanã sãka wa mãsu yin sadaka. "1
قَالَ هَلْ عَلِمْتُم مَّا فَعَلْتُم بِيُوسُفَ وَأَخِيهِ إِذْ أَنتُمْ جَـٰهِلُونَ
qāla hal ʿalim'tum mā faʿaltum biyūsufa wa-akhīhi idh antum jāhilūna
Ya ce: "Shin, kan1 san abin da kuka aikata ga Yũsufu da ɗan'uwansa a lõkacin da kuke jãhilai?"
قَالُوٓا۟ أَءِنَّكَ لَأَنتَ يُوسُفُ ۖ قَالَ أَنَا۠ يُوسُفُ وَهَـٰذَآ أَخِى ۖ قَدْ مَنَّ ٱللَّهُ عَلَيْنَآ ۖ إِنَّهُۥ مَن يَتَّقِ وَيَصْبِرْ فَإِنَّ ٱللَّهَ لَا يُضِيعُ أَجْرَ ٱلْمُحْسِنِينَ
qālū a-innaka la-anta yūsufu qāla anā yūsufu wahādhā akhī qad manna l-lahu ʿalaynā innahu man yattaqi wayaṣbir fa-inna l-laha lā yuḍīʿu ajra l-muḥ'sinīna
Saka ce: "Shin kõ, lalle ne, kai ne Yũsufu?" Ya ce: "Nĩ ne Yũsufu, kuma wamian shĩ ne ɗan'uwãna. Hƙĩƙa Allah Yã yi falala a gare mu. Lalle ne, shi wanda ya bi Allah da taƙawa, kuma ya yi haƙuri, to, Lalle ne Allah bã Ya tõzarta lãdar mãsu kyautatãwa."
قَالُوا۟ تَٱللَّهِ لَقَدْ ءَاثَرَكَ ٱللَّهُ عَلَيْنَا وَإِن كُنَّا لَخَـٰطِـِٔينَ
qālū tal-lahi laqad ātharaka l-lahu ʿalaynā wa-in kunnā lakhāṭiīna
Suka ce: "Tallahi! Lalle ne haƙĩƙa, Allah Yã zãɓe ka akannmu, kuma lalle ne mun kasance, haƙĩƙa, mãsu kuskure."
قَالَ لَا تَثْرِيبَ عَلَيْكُمُ ٱلْيَوْمَ ۖ يَغْفِرُ ٱللَّهُ لَكُمْ ۖ وَهُوَ أَرْحَمُ ٱلرَّٰحِمِينَ
qāla lā tathrība ʿalaykumu l-yawma yaghfiru l-lahu lakum wahuwa arḥamu l-rāḥimīna
Ya ce: "Bãbu zargi akanku a yau, Allah Yanã gãfartã muku, kuma Shĩ ne Mafi rahamar mãsu rahama."
ٱذْهَبُوا۟ بِقَمِيصِى هَـٰذَا فَأَلْقُوهُ عَلَىٰ وَجْهِ أَبِى يَأْتِ بَصِيرًۭا وَأْتُونِى بِأَهْلِكُمْ أَجْمَعِينَ
idh'habū biqamīṣī hādhā fa-alqūhu ʿalā wajhi abī yati baṣīran watūnī bi-ahlikum ajmaʿīna
"Ku tafi da rĩgãta wannan, sa'an nan ku jẽfa ta a kan fuskar mahaifina, zai kõma mai gani. Kuma ku zo mini da iyãlinku bãki ɗaya."
وَلَمَّا فَصَلَتِ ٱلْعِيرُ قَالَ أَبُوهُمْ إِنِّى لَأَجِدُ رِيحَ يُوسُفَ ۖ لَوْلَآ أَن تُفَنِّدُونِ
walammā faṣalati l-ʿīru qāla abūhum innī la-ajidu rīḥa yūsufa lawlā an tufannidūni
Kuma, a lõkacin da ãyari1 ya bar (Masar) ubansa ya ce: "Lalle ne nĩ inã shãƙar iskar Yũsufu, bã dõmin kanã ƙaryata ni ba."
قَالُوا۟ تَٱللَّهِ إِنَّكَ لَفِى ضَلَـٰلِكَ ٱلْقَدِيمِ
qālū tal-lahi innaka lafī ḍalālika l-qadīmi
Suka ce: "Tallahi lalle ne, kai, haƙĩƙa, kanã a cikin ɓatarka daɗaɗɗa."
فَلَمَّآ أَن جَآءَ ٱلْبَشِيرُ أَلْقَىٰهُ عَلَىٰ وَجْهِهِۦ فَٱرْتَدَّ بَصِيرًۭا ۖ قَالَ أَلَمْ أَقُل لَّكُمْ إِنِّىٓ أَعْلَمُ مِنَ ٱللَّهِ مَا لَا تَعْلَمُونَ
falammā an jāa l-bashīru alqāhu ʿalā wajhihi fa-ir'tadda baṣīran qāla alam aqul lakum innī aʿlamu mina l-lahi mā lā taʿlamūna
Sa'an nan a lõkacin da mai bãyar da bushãra ya je, sai ya jẽfa ta a kan fuskarsa, sai ya kõma mai gani. Ya ce: "Shin, ban gaya muku ba, lalle ne, ni inã sanin abin da ba ku sani ba, daga Allah?"
قَالُوا۟ يَـٰٓأَبَانَا ٱسْتَغْفِرْ لَنَا ذُنُوبَنَآ إِنَّا كُنَّا خَـٰطِـِٔينَ
qālū yāabānā is'taghfir lanā dhunūbanā innā kunnā khāṭiīna
Suka ce: "Yã ubanmu!1 ka nẽma mana gãfara ga zunubanmu, lalle ne mũ, mun kasance mãsu kuskure."
قَالَ سَوْفَ أَسْتَغْفِرُ لَكُمْ رَبِّىٓ ۖ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلْغَفُورُ ٱلرَّحِيمُ
qāla sawfa astaghfiru lakum rabbī innahu huwa l-ghafūru l-raḥīmu
Ya ce: "Da sannu zã ni nẽma muku gãfara daga Ubangijina. Shi ne Mai gãfara, Mai jin ƙai."
فَلَمَّا دَخَلُوا۟ عَلَىٰ يُوسُفَ ءَاوَىٰٓ إِلَيْهِ أَبَوَيْهِ وَقَالَ ٱدْخُلُوا۟ مِصْرَ إِن شَآءَ ٱللَّهُ ءَامِنِينَ
falammā dakhalū ʿalā yūsufa āwā ilayhi abawayhi waqāla ud'khulū miṣ'ra in shāa l-lahu āminīna
Sa'an nan a lõkacin1 da suka shiga gun Yũsufu, yã tattara mahaifansa biyu a gare shi, kuma ya ce: "Ku shiga Masar in Allah Ya so, kuna amintattu."
وَرَفَعَ أَبَوَيْهِ عَلَى ٱلْعَرْشِ وَخَرُّوا۟ لَهُۥ سُجَّدًۭا ۖ وَقَالَ يَـٰٓأَبَتِ هَـٰذَا تَأْوِيلُ رُءْيَـٰىَ مِن قَبْلُ قَدْ جَعَلَهَا رَبِّى حَقًّۭا ۖ وَقَدْ أَحْسَنَ بِىٓ إِذْ أَخْرَجَنِى مِنَ ٱلسِّجْنِ وَجَآءَ بِكُم مِّنَ ٱلْبَدْوِ مِنۢ بَعْدِ أَن نَّزَغَ ٱلشَّيْطَـٰنُ بَيْنِى وَبَيْنَ إِخْوَتِىٓ ۚ إِنَّ رَبِّى لَطِيفٌۭ لِّمَا يَشَآءُ ۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلْعَلِيمُ ٱلْحَكِيمُ
warafaʿa abawayhi ʿalā l-ʿarshi wakharrū lahu sujjadan waqāla yāabati hādhā tawīlu ru'yāya min qablu qad jaʿalahā rabbī ḥaqqan waqad aḥsana bī idh akhrajanī mina l-sij'ni wajāa bikum mina l-badwi min baʿdi an nazagha l-shayṭānu baynī wabayna ikh'watī inna rabbī laṭīfun limā yashāu innahu huwa l-ʿalīmu l-ḥakīmu
Kuma ya ɗaukaka iyãyensa biyu a kan karaga, sa'an nan suka fãɗi a gare shi, suna mãsu sujada.1 Kuma ya ce: "Ya bãbãna! Wannan ita ce fassarar mafarkin nan nãwa. Lalle ne Ubangijina Ya sanya shi ya tabbata sõsai, kuma lalle ne Ya kyautata game da ni a lõkacin da Ya fitar da ni daga kurkuku. Kuma Ya zo da ku daga ƙauye, a bãyan Shaiɗan yã yi fisgar ɓarna a tsakãnĩna da tsakãnin 'yan'uwana, Lalle ne Ubangijina Mai tausasawa ne ga abin da Yake so. Lalle ne Shĩ, Shĩ ne Masani, Mai hikima."
۞ رَبِّ قَدْ ءَاتَيْتَنِى مِنَ ٱلْمُلْكِ وَعَلَّمْتَنِى مِن تَأْوِيلِ ٱلْأَحَادِيثِ ۚ فَاطِرَ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ أَنتَ وَلِىِّۦ فِى ٱلدُّنْيَا وَٱلْـَٔاخِرَةِ ۖ تَوَفَّنِى مُسْلِمًۭا وَأَلْحِقْنِى بِٱلصَّـٰلِحِينَ
rabbi qad ātaytanī mina l-mul'ki waʿallamtanī min tawīli l-aḥādīthi fāṭira l-samāwāti wal-arḍi anta waliyyī fī l-dun'yā wal-ākhirati tawaffanī mus'liman wa-alḥiq'nī bil-ṣāliḥīna
"Yã Ubangijina1 lalle ne Kã bã ni daga mulki, kuma Kã sanar da ni daga fassarar lãbaru. Ya Mahaliccin sammai da ƙasa! Kai ne Majiɓincĩna a dũniya da Lãhira Ka karɓi raina inã Musulmi, kuma Ka riskar da ni ga sãlihai."
ذَٰلِكَ مِنْ أَنۢبَآءِ ٱلْغَيْبِ نُوحِيهِ إِلَيْكَ ۖ وَمَا كُنتَ لَدَيْهِمْ إِذْ أَجْمَعُوٓا۟ أَمْرَهُمْ وَهُمْ يَمْكُرُونَ
dhālika min anbāi l-ghaybi nūḥīhi ilayka wamā kunta ladayhim idh ajmaʿū amrahum wahum yamkurūna
Wannan daga1 lãbarun gaibi ne, Munã yin wahayinsa zuwa gare ka, kuma ba ka kasance a wurinsu ba a lõkacin da suke yin niyyar zartar da al'amarinsu, alhãli sunã yin mãkirci.
وَمَآ أَكْثَرُ ٱلنَّاسِ وَلَوْ حَرَصْتَ بِمُؤْمِنِينَ
wamā aktharu l-nāsi walaw ḥaraṣta bimu'minīna
Kuma mafi yawan mutãne ba su zama mãsu ĩmãni ba, kõ da kã yi kwaɗayin haka.
وَمَا تَسْـَٔلُهُمْ عَلَيْهِ مِنْ أَجْرٍ ۚ إِنْ هُوَ إِلَّا ذِكْرٌۭ لِّلْعَـٰلَمِينَ
wamā tasaluhum ʿalayhi min ajrin in huwa illā dhik'run lil'ʿālamīna
Kuma bã ka tambayar su wata lãdã a kansa. Shĩ bai zama ba fãce ambato dõmin halittu.
وَكَأَيِّن مِّنْ ءَايَةٍۢ فِى ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ يَمُرُّونَ عَلَيْهَا وَهُمْ عَنْهَا مُعْرِضُونَ
waka-ayyin min āyatin fī l-samāwāti wal-arḍi yamurrūna ʿalayhā wahum ʿanhā muʿ'riḍūna
Kuma da yawa, wata ãyã a cikin sammai da ƙasa sunã shũɗẽwa a kanta kuma sũ, sunã bijirẽwa daga gare ta.
وَمَا يُؤْمِنُ أَكْثَرُهُم بِٱللَّهِ إِلَّا وَهُم مُّشْرِكُونَ
wamā yu'minu aktharuhum bil-lahi illā wahum mush'rikūna
Kuma mafi yawansu ba su yin ĩmãni da Allah fãce kuma sunã mãsu shirki.
أَفَأَمِنُوٓا۟ أَن تَأْتِيَهُمْ غَـٰشِيَةٌۭ مِّنْ عَذَابِ ٱللَّهِ أَوْ تَأْتِيَهُمُ ٱلسَّاعَةُ بَغْتَةًۭ وَهُمْ لَا يَشْعُرُونَ
afa-aminū an tatiyahum ghāshiyatun min ʿadhābi l-lahi aw tatiyahumu l-sāʿatu baghtatan wahum lā yashʿurūna
Shin fa, sun amince cẽwa wata masĩfa daga azãbar Allah ta zo musu ko kuwa Tãshin ¡iyãma ta zo musu kwatsam, alhãli sũ ba su sani ba?
قُلْ هَـٰذِهِۦ سَبِيلِىٓ أَدْعُوٓا۟ إِلَى ٱللَّهِ ۚ عَلَىٰ بَصِيرَةٍ أَنَا۠ وَمَنِ ٱتَّبَعَنِى ۖ وَسُبْحَـٰنَ ٱللَّهِ وَمَآ أَنَا۠ مِنَ ٱلْمُشْرِكِينَ
qul hādhihi sabīlī adʿū ilā l-lahi ʿalā baṣīratin anā wamani ittabaʿanī wasub'ḥāna l-lahi wamā anā mina l-mush'rikīna
Ka ce: "Wannan ce hanyãta;1 inã kira zuwa ga Allah a kan basĩra, nĩ da waɗanda suka bĩ ni, kuma tsarki ya tabbata ga Allah! Nĩ kuma, ban zama daga mãsu shirki ba."
وَمَآ أَرْسَلْنَا مِن قَبْلِكَ إِلَّا رِجَالًۭا نُّوحِىٓ إِلَيْهِم مِّنْ أَهْلِ ٱلْقُرَىٰٓ ۗ أَفَلَمْ يَسِيرُوا۟ فِى ٱلْأَرْضِ فَيَنظُرُوا۟ كَيْفَ كَانَ عَـٰقِبَةُ ٱلَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ ۗ وَلَدَارُ ٱلْـَٔاخِرَةِ خَيْرٌۭ لِّلَّذِينَ ٱتَّقَوْا۟ ۗ أَفَلَا تَعْقِلُونَ
wamā arsalnā min qablika illā rijālan nūḥī ilayhim min ahli l-qurā afalam yasīrū fī l-arḍi fayanẓurū kayfa kāna ʿāqibatu alladhīna min qablihim waladāru l-ākhirati khayrun lilladhīna ittaqaw afalā taʿqilūna
Kuma ba Mu aika ba a gabãninka fãce mazãje, Munã wahayi zuwa gare su, daga mutãnen ƙauyuka. Shin fa, ba su yi tafiya a cikin ƙasa ba, dõmin su dũbayadda ãƙibar waɗanda suka kasance daga gabãninsu ta zama? Kuma lalle ne gidan Lãhira shĩ ne mafi alhẽri ga waɗanda suka yi taƙawa? Shin fa, bã ku hankalta?
حَتَّىٰٓ إِذَا ٱسْتَيْـَٔسَ ٱلرُّسُلُ وَظَنُّوٓا۟ أَنَّهُمْ قَدْ كُذِبُوا۟ جَآءَهُمْ نَصْرُنَا فَنُجِّىَ مَن نَّشَآءُ ۖ وَلَا يُرَدُّ بَأْسُنَا عَنِ ٱلْقَوْمِ ٱلْمُجْرِمِينَ
ḥattā idhā is'tayasa l-rusulu waẓannū annahum qad kudhibū jāahum naṣrunā fanujjiya man nashāu walā yuraddu basunā ʿani l-qawmi l-muj'rimīna
Har a lõkacin da Manzanni suka yanke tsammãni, kuma suka yi zaton cẽwa an jingina suga ƙarya, sai taimakonMu ya je masu, Sa'an nan Mu tsẽrar da wanda Muke so, kuma bã a mayar da azãbarMu daga mutãne mãsu laifi.
لَقَدْ كَانَ فِى قَصَصِهِمْ عِبْرَةٌۭ لِّأُو۟لِى ٱلْأَلْبَـٰبِ ۗ مَا كَانَ حَدِيثًۭا يُفْتَرَىٰ وَلَـٰكِن تَصْدِيقَ ٱلَّذِى بَيْنَ يَدَيْهِ وَتَفْصِيلَ كُلِّ شَىْءٍۢ وَهُدًۭى وَرَحْمَةًۭ لِّقَوْمٍۢ يُؤْمِنُونَ
laqad kāna fī qaṣaṣihim ʿib'ratun li-ulī l-albābi mā kāna ḥadīthan yuf'tarā walākin taṣdīqa alladhī bayna yadayhi watafṣīla kulli shayin wahudan waraḥmatan liqawmin yu'minūna
Lalle ne haƙĩƙa abin kula yã kasance a cikin ƙissoshinsu ga masu hankali. Bai kasance wani ƙirƙiran lãbãri ba kuma amma shi gaskatãwa ne ga, abin da yake a gaba gare shi, da rarrabẽwar dukan abũbuwa, da shiriya da rahama ga mutãne waɗanda suka yi ĩmãni.