محمد
Muhammad
Muhammad
ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ وَصَدُّوا۟ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ أَضَلَّ أَعْمَـٰلَهُمْ
alladhīna kafarū waṣaddū ʿan sabīli l-lahi aḍalla aʿmālahum
Waɗanda suka kãfirta kuma suka kange mutãne daga tafarkin Allah, (Allah) Ya ɓatar da ayyukansu.
وَٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَعَمِلُوا۟ ٱلصَّـٰلِحَـٰتِ وَءَامَنُوا۟ بِمَا نُزِّلَ عَلَىٰ مُحَمَّدٍۢ وَهُوَ ٱلْحَقُّ مِن رَّبِّهِمْ ۙ كَفَّرَ عَنْهُمْ سَيِّـَٔاتِهِمْ وَأَصْلَحَ بَالَهُمْ
wa-alladhīna āmanū waʿamilū l-ṣāliḥāti waāmanū bimā nuzzila ʿalā muḥammadin wahuwa l-ḥaqu min rabbihim kaffara ʿanhum sayyiātihim wa-aṣlaḥa bālahum
Kuma waɗanda suka yi ĩmani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma suka yi ĩmani da abinda aka sassaukar ga Muhammadu, alhãli kuwa shĩ ne gaskiya daga Ubangijinsu, (Allah) Yã karkare musu miyãgun ayyukansu, kuma Yã kyautata hãlãyensu.
ذَٰلِكَ بِأَنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ ٱتَّبَعُوا۟ ٱلْبَـٰطِلَ وَأَنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ ٱتَّبَعُوا۟ ٱلْحَقَّ مِن رَّبِّهِمْ ۚ كَذَٰلِكَ يَضْرِبُ ٱللَّهُ لِلنَّاسِ أَمْثَـٰلَهُمْ
dhālika bi-anna alladhīna kafarū ittabaʿū l-bāṭila wa-anna alladhīna āmanū ittabaʿū l-ḥaqa min rabbihim kadhālika yaḍribu l-lahu lilnnāsi amthālahum
Wannan kuwa sabõda lalle, waɗanda suka kãfirta sun bi ƙarya, kumar lalle waɗanda suka yi ĩmãni, sun bi gaskiya daga Ubangijinsu. Kamar wannan ne Allah Yake bayyana wa mutãne misãlansu.
فَإِذَا لَقِيتُمُ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ فَضَرْبَ ٱلرِّقَابِ حَتَّىٰٓ إِذَآ أَثْخَنتُمُوهُمْ فَشُدُّوا۟ ٱلْوَثَاقَ فَإِمَّا مَنًّۢا بَعْدُ وَإِمَّا فِدَآءً حَتَّىٰ تَضَعَ ٱلْحَرْبُ أَوْزَارَهَا ۚ ذَٰلِكَ وَلَوْ يَشَآءُ ٱللَّهُ لَٱنتَصَرَ مِنْهُمْ وَلَـٰكِن لِّيَبْلُوَا۟ بَعْضَكُم بِبَعْضٍۢ ۗ وَٱلَّذِينَ قُتِلُوا۟ فِى سَبِيلِ ٱللَّهِ فَلَن يُضِلَّ أَعْمَـٰلَهُمْ
fa-idhā laqītumu alladhīna kafarū faḍarba l-riqābi ḥattā idhā athkhantumūhum fashuddū l-wathāqa fa-immā mannan baʿdu wa-immā fidāan ḥattā taḍaʿa l-ḥarbu awzārahā dhālika walaw yashāu l-lahu la-intaṣara min'hum walākin liyabluwā baʿḍakum bibaʿḍin wa-alladhīna qutilū fī sabīli l-lahi falan yuḍilla aʿmālahum
Sabõda haka idan kun haɗu da waɗanda suka kãfirta, sai ku yi ta dũkan wuyõyinsu har a lõkacin da suka yawaita musu kisa, to, ku tsananta ɗaurinsu sa'an nan imma karimci a bãyan' haka kõ biyan fansa, har yãƙi ya saukar da kayansa mãsu nauyi. Wancan, dã Allah nã so da Ya ci nasara a kansu (ba tare da yaƙin ba) kuma amma (ya wajabta jihadi) dõmin Ya jarraba sãshenku da sãshe. Kuma waɗanda zaka kashe a cikin tafarkin Allah,1 to, bã ai ɓatar da ayyukansu ba.
سَيَهْدِيهِمْ وَيُصْلِحُ بَالَهُمْ
sayahdīhim wayuṣ'liḥu bālahum
Zai shiryar da su, kuma Ya kyautata hãlãyensu.
وَيُدْخِلُهُمُ ٱلْجَنَّةَ عَرَّفَهَا لَهُمْ
wayud'khiluhumu l-janata ʿarrafahā lahum
Kuma Ya shigarda su Aljanna (wadda) Ya siffanta ta a gare su.
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓا۟ إِن تَنصُرُوا۟ ٱللَّهَ يَنصُرْكُمْ وَيُثَبِّتْ أَقْدَامَكُمْ
yāayyuhā alladhīna āmanū in tanṣurū l-laha yanṣur'kum wayuthabbit aqdāmakum
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmani! Idan kun taimaki Allah, zai taimake ku, kuma Ya tabbatar da dugãduganku..1
وَٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ فَتَعْسًۭا لَّهُمْ وَأَضَلَّ أَعْمَـٰلَهُمْ
wa-alladhīna kafarū fataʿsan lahum wa-aḍalla aʿmālahum
Kuma waɗanda suka kãfirta, to, ruɓushi ya tabbata a gare su, kuma (Allah) Ya ɓatar da ayyukansu.
ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمْ كَرِهُوا۟ مَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ فَأَحْبَطَ أَعْمَـٰلَهُمْ
dhālika bi-annahum karihū mā anzala l-lahu fa-aḥbaṭa aʿmālahum
Wannan, sabõda lalle sũ, sun ƙi abin da Allah Ya saukar dõmin haka Ya ɓata ayyukansu.
۞ أَفَلَمْ يَسِيرُوا۟ فِى ٱلْأَرْضِ فَيَنظُرُوا۟ كَيْفَ كَانَ عَـٰقِبَةُ ٱلَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ ۚ دَمَّرَ ٱللَّهُ عَلَيْهِمْ ۖ وَلِلْكَـٰفِرِينَ أَمْثَـٰلُهَا
afalam yasīrū fī l-arḍi fayanẓurū kayfa kāna ʿāqibatu alladhīna min qablihim dammara l-lahu ʿalayhim walil'kāfirīna amthāluhā
Shin, ba su yi tafiya ba, a cikin ƙasa, dõmin su gani yadda ãƙibar waɗanda ke a gabãninsu ta kasance? Allah Ya darkãke a kansu. Kuma akwai misãlan wannan ãƙibar ga kãfirai (na kõwane zãmani).
ذَٰلِكَ بِأَنَّ ٱللَّهَ مَوْلَى ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَأَنَّ ٱلْكَـٰفِرِينَ لَا مَوْلَىٰ لَهُمْ
dhālika bi-anna l-laha mawlā alladhīna āmanū wa-anna l-kāfirīna lā mawlā lahum
Wancan! Sabõda lalle Allah ne Majiɓincin waɗanda suka yi ĩmãni, kuma lalle, kafirai bãbu wani majiɓinci a gare su.
إِنَّ ٱللَّهَ يُدْخِلُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَعَمِلُوا۟ ٱلصَّـٰلِحَـٰتِ جَنَّـٰتٍۢ تَجْرِى مِن تَحْتِهَا ٱلْأَنْهَـٰرُ ۖ وَٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ يَتَمَتَّعُونَ وَيَأْكُلُونَ كَمَا تَأْكُلُ ٱلْأَنْعَـٰمُ وَٱلنَّارُ مَثْوًۭى لَّهُمْ
inna l-laha yud'khilu alladhīna āmanū waʿamilū l-ṣāliḥāti jannātin tajrī min taḥtihā l-anhāru wa-alladhīna kafarū yatamattaʿūna wayakulūna kamā takulu l-anʿāmu wal-nāru mathwan lahum
Lalle ne, Allah nã shigar da waɗanda suka yi ĩmani kuma suka aikata ayyukan ƙwarai a gidãjen Aljanna, kõgunan ruwa na gudana daga ƙarƙashinsu, kuma waɗanda suka kãfirta sunã jin ɗan daɗi (adũniya) kuma sunã ci, kamar yadda dabbõbi ke ci, kuma wutã ita ce mazauni a gare su.
وَكَأَيِّن مِّن قَرْيَةٍ هِىَ أَشَدُّ قُوَّةًۭ مِّن قَرْيَتِكَ ٱلَّتِىٓ أَخْرَجَتْكَ أَهْلَكْنَـٰهُمْ فَلَا نَاصِرَ لَهُمْ
waka-ayyin min qaryatin hiya ashaddu quwwatan min qaryatika allatī akhrajatka ahlaknāhum falā nāṣira lahum
Kuma da yawa akwai alƙarya, ita ce mafi tsanani ga ƙarfi daga alƙaryarka wadda ta fitar da kai, Mun halaka ta, sa'an nan kuwa bãbu wani mai taimako a gare su.
أَفَمَن كَانَ عَلَىٰ بَيِّنَةٍۢ مِّن رَّبِّهِۦ كَمَن زُيِّنَ لَهُۥ سُوٓءُ عَمَلِهِۦ وَٱتَّبَعُوٓا۟ أَهْوَآءَهُم
afaman kāna ʿalā bayyinatin min rabbihi kaman zuyyina lahu sūu ʿamalihi wa-ittabaʿū ahwāahum
Shin, wanda ya kasance a kan wata hujja daga Ubangijinsa, zai zama kamar wanda aka ƙawãce masa mugun aikinsa, kuma suka bibbiyi son zũciyõyinsu?
مَّثَلُ ٱلْجَنَّةِ ٱلَّتِى وُعِدَ ٱلْمُتَّقُونَ ۖ فِيهَآ أَنْهَـٰرٌۭ مِّن مَّآءٍ غَيْرِ ءَاسِنٍۢ وَأَنْهَـٰرٌۭ مِّن لَّبَنٍۢ لَّمْ يَتَغَيَّرْ طَعْمُهُۥ وَأَنْهَـٰرٌۭ مِّنْ خَمْرٍۢ لَّذَّةٍۢ لِّلشَّـٰرِبِينَ وَأَنْهَـٰرٌۭ مِّنْ عَسَلٍۢ مُّصَفًّۭى ۖ وَلَهُمْ فِيهَا مِن كُلِّ ٱلثَّمَرَٰتِ وَمَغْفِرَةٌۭ مِّن رَّبِّهِمْ ۖ كَمَنْ هُوَ خَـٰلِدٌۭ فِى ٱلنَّارِ وَسُقُوا۟ مَآءً حَمِيمًۭا فَقَطَّعَ أَمْعَآءَهُمْ
mathalu l-janati allatī wuʿida l-mutaqūna fīhā anhārun min māin ghayri āsinin wa-anhārun min labanin lam yataghayyar ṭaʿmuhu wa-anhārun min khamrin ladhatin lilshāribīna wa-anhārun min ʿasalin muṣaffan walahum fīhā min kulli l-thamarāti wamaghfiratun min rabbihim kaman huwa khālidun fī l-nāri wasuqū māan ḥamīman faqaṭṭaʿa amʿāahum
Misãlin Aljanna, wadda aka yi wa'adinta ga mãsu taƙawa, a cikinta akwai waɗansu kõguna na ruwa ba mai sãkẽwa ba da waɗansu kõguna na madara wadda ɗanɗanonta bã ya canjãwa, da waɗansu kõguna na giya mai dãɗi ga mashãya, da waɗansu kõguna na zuma tãtacce kuma suna sãmu, a cikinta, daga kõwane irin 'ya'yan itãce, da wata gãfara daga Ubangijinsu. (Shin, mãsu wannan ni'ima nã daidaita) kamar wanda yake madawwami ne a cikin wutã kuma an shãyar da su wani ruwa mai zãfi har ya kakkãtse hanjinsu?
وَمِنْهُم مَّن يَسْتَمِعُ إِلَيْكَ حَتَّىٰٓ إِذَا خَرَجُوا۟ مِنْ عِندِكَ قَالُوا۟ لِلَّذِينَ أُوتُوا۟ ٱلْعِلْمَ مَاذَا قَالَ ءَانِفًا ۚ أُو۟لَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ طَبَعَ ٱللَّهُ عَلَىٰ قُلُوبِهِمْ وَٱتَّبَعُوٓا۟ أَهْوَآءَهُمْ
wamin'hum man yastamiʿu ilayka ḥattā idhā kharajū min ʿindika qālū lilladhīna ūtū l-ʿil'ma mādhā qāla ānifan ulāika alladhīna ṭabaʿa l-lahu ʿalā qulūbihim wa-ittabaʿū ahwāahum
Kuma daga cikinsu akwai wanda ke saurare1 zuwa gare ka, har idan sun fita daga wurinka, su ce wa waɗanda aka bai wa ilmi "Mẽne ne (Muhammadu) ya fãɗa ɗazu?" Waɗannan ne waɗanda Allah Ya shãfe haske daga zukãtansu, kuma suka bi son zũciyõyinsu.
وَٱلَّذِينَ ٱهْتَدَوْا۟ زَادَهُمْ هُدًۭى وَءَاتَىٰهُمْ تَقْوَىٰهُمْ
wa-alladhīna ih'tadaw zādahum hudan waātāhum taqwāhum
Kuma waɗannan da suka nẽmi shiryuwa (Allah) Ya ƙara musu shiryuwarsu, kuma Yã bã su (sakamakon) taƙawarsu.1
فَهَلْ يَنظُرُونَ إِلَّا ٱلسَّاعَةَ أَن تَأْتِيَهُم بَغْتَةًۭ ۖ فَقَدْ جَآءَ أَشْرَاطُهَا ۚ فَأَنَّىٰ لَهُمْ إِذَا جَآءَتْهُمْ ذِكْرَىٰهُمْ
fahal yanẓurūna illā l-sāʿata an tatiyahum baghtatan faqad jāa ashrāṭuhā fa-annā lahum idhā jāathum dhik'rāhum
To shin sunã jiran (wani abu)? Fãce Sa'a ta jẽ musu bisa abku. dõmin lalle sharuɗɗanta sun zo. To, yãya tunãwarsu1 take, idan har ta jẽ musu?
فَٱعْلَمْ أَنَّهُۥ لَآ إِلَـٰهَ إِلَّا ٱللَّهُ وَٱسْتَغْفِرْ لِذَنۢبِكَ وَلِلْمُؤْمِنِينَ وَٱلْمُؤْمِنَـٰتِ ۗ وَٱللَّهُ يَعْلَمُ مُتَقَلَّبَكُمْ وَمَثْوَىٰكُمْ
fa-iʿ'lam annahu lā ilāha illā l-lahu wa-is'taghfir lidhanbika walil'mu'minīna wal-mu'mināti wal-lahu yaʿlamu mutaqallabakum wamathwākum
Sabõda hakaa ka sani, cẽwa bãbu abin bautãwa fãce Allah, kuma ka nẽmi gãfara ga zunubin, ka,1 (kuma sabõda mũminai maza da mũminai mãtã kuma Allah Ya san majũyaiku da mazauninku.
وَيَقُولُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ لَوْلَا نُزِّلَتْ سُورَةٌۭ ۖ فَإِذَآ أُنزِلَتْ سُورَةٌۭ مُّحْكَمَةٌۭ وَذُكِرَ فِيهَا ٱلْقِتَالُ ۙ رَأَيْتَ ٱلَّذِينَ فِى قُلُوبِهِم مَّرَضٌۭ يَنظُرُونَ إِلَيْكَ نَظَرَ ٱلْمَغْشِىِّ عَلَيْهِ مِنَ ٱلْمَوْتِ ۖ فَأَوْلَىٰ لَهُمْ
wayaqūlu alladhīna āmanū lawlā nuzzilat sūratun fa-idhā unzilat sūratun muḥ'kamatun wadhukira fīhā l-qitālu ra-ayta alladhīna fī qulūbihim maraḍun yanẓurūna ilayka naẓara l-maghshiyi ʿalayhi mina l-mawti fa-awlā lahum
Kuma waɗanda suka yi ĩmãni sunã cẽwa: "Don mẽne ne ba a saukar da wata sũra ba? "To idan aka saukar da wata sũra, bayyananna, kuma aka ambaci yãƙi a cikinta, zã ka ga waɗanda yake akwai wata cuta a cikin zukatansu sunã kallo zuwa gare ka, irin kallon wanda aka rufe da mãgãgi sabõda mutuwa. To, abin da yake mafĩfĩci a gare su:
طَاعَةٌۭ وَقَوْلٌۭ مَّعْرُوفٌۭ ۚ فَإِذَا عَزَمَ ٱلْأَمْرُ فَلَوْ صَدَقُوا۟ ٱللَّهَ لَكَانَ خَيْرًۭا لَّهُمْ
ṭāʿatun waqawlun maʿrūfun fa-idhā ʿazama l-amru falaw ṣadaqū l-laha lakāna khayran lahum
Yin ɗã'a da magana mai kyau. Sa'an nan idan al'marin ya ƙullu,1 to, dã sun yi wa Allah gaskiya, lalle dã ya kasance mafifi ci a gare su.
فَهَلْ عَسَيْتُمْ إِن تَوَلَّيْتُمْ أَن تُفْسِدُوا۟ فِى ٱلْأَرْضِ وَتُقَطِّعُوٓا۟ أَرْحَامَكُمْ
fahal ʿasaytum in tawallaytum an tuf'sidū fī l-arḍi watuqaṭṭiʿū arḥāmakum
To, shin, kunã fãtan idan kun jũya (daga umurnin) zã ku yi ɓarna a cikin ƙasã, kuma ku yan yanke1 zumuntarku?
أُو۟لَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ لَعَنَهُمُ ٱللَّهُ فَأَصَمَّهُمْ وَأَعْمَىٰٓ أَبْصَـٰرَهُمْ
ulāika alladhīna laʿanahumu l-lahu fa-aṣammahum wa-aʿmā abṣārahum
Waɗannan sũ ne waɗanda Allah Ya la'anẽ su, sa'an nan Ya kurumtar da su, kuma Ya makantar da ganinsu.
أَفَلَا يَتَدَبَّرُونَ ٱلْقُرْءَانَ أَمْ عَلَىٰ قُلُوبٍ أَقْفَالُهَآ
afalā yatadabbarūna l-qur'āna am ʿalā qulūbin aqfāluhā
Shin to, bã zã su, kula da Alƙur'ãni ba, kõ kuwa a bin zukã tansu akwai makullansu?
إِنَّ ٱلَّذِينَ ٱرْتَدُّوا۟ عَلَىٰٓ أَدْبَـٰرِهِم مِّنۢ بَعْدِ مَا تَبَيَّنَ لَهُمُ ٱلْهُدَى ۙ ٱلشَّيْطَـٰنُ سَوَّلَ لَهُمْ وَأَمْلَىٰ لَهُمْ
inna alladhīna ir'taddū ʿalā adbārihim min baʿdi mā tabayyana lahumu l-hudā l-shayṭānu sawwala lahum wa-amlā lahum
lalle ne, waɗanda suka kõma bãya a kan dugãdugansu a bãyan shiryuwa tã bayyana a gare su, Shaiɗan ne ya ƙawãta 1musu (haka), kuma ya yi musu shibta.
ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمْ قَالُوا۟ لِلَّذِينَ كَرِهُوا۟ مَا نَزَّلَ ٱللَّهُ سَنُطِيعُكُمْ فِى بَعْضِ ٱلْأَمْرِ ۖ وَٱللَّهُ يَعْلَمُ إِسْرَارَهُمْ
dhālika bi-annahum qālū lilladhīna karihū mā nazzala l-lahu sanuṭīʿukum fī baʿḍi l-amri wal-lahu yaʿlamu is'rārahum
Wancan, dõmin lalle sũ sun ce wa waɗanda suka ƙi abin da Allah Ya saukar: "Za mu yi muku ɗã'ã ga sãshen al'amarin," alhãli kuwa Allah Yanã sane da gãnawarsu ta asĩri.
فَكَيْفَ إِذَا تَوَفَّتْهُمُ ٱلْمَلَـٰٓئِكَةُ يَضْرِبُونَ وُجُوهَهُمْ وَأَدْبَـٰرَهُمْ
fakayfa idhā tawaffathumu l-malāikatu yaḍribūna wujūhahum wa-adbārahum
To, yãya hãlinsu yake a lõkacin da malã'iku ke karɓar rãyukansu, sunã dũkan fuskõkinsu da ɗuwaiwansu?
ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمُ ٱتَّبَعُوا۟ مَآ أَسْخَطَ ٱللَّهَ وَكَرِهُوا۟ رِضْوَٰنَهُۥ فَأَحْبَطَ أَعْمَـٰلَهُمْ
dhālika bi-annahumu ittabaʿū mā askhaṭa l-laha wakarihū riḍ'wānahu fa-aḥbaṭa aʿmālahum
Wannan, dõmin lalle sũ sun bi abin da ya, fusãtar da Allah kuma sun ƙi yardarSa, sabõda haka Ya ɓãta ayyukansu.
أَمْ حَسِبَ ٱلَّذِينَ فِى قُلُوبِهِم مَّرَضٌ أَن لَّن يُخْرِجَ ٱللَّهُ أَضْغَـٰنَهُمْ
am ḥasiba alladhīna fī qulūbihim maraḍun an lan yukh'rija l-lahu aḍghānahum
Ko kuwa waɗanda ke da wata cũta a cikin zukatansu suna zaton cẽwa Allah ba zai fitar da mugun ƙulle-ƙullen su (ga Musulunci) ba?
وَلَوْ نَشَآءُ لَأَرَيْنَـٰكَهُمْ فَلَعَرَفْتَهُم بِسِيمَـٰهُمْ ۚ وَلَتَعْرِفَنَّهُمْ فِى لَحْنِ ٱلْقَوْلِ ۚ وَٱللَّهُ يَعْلَمُ أَعْمَـٰلَكُمْ
walaw nashāu la-araynākahum falaʿaraftahum bisīmāhum walataʿrifannahum fī laḥni l-qawli wal-lahu yaʿlamu aʿmālakum
Kuma dã Munã so, dã lalle Mun nũna maka su. To, lalle kanã sanin su game da alãmarsu. Kuma lalle kanã sanin su ga shaguɓen magana, alhali kuwa Allah Yanã sanin ayyukanku.
وَلَنَبْلُوَنَّكُمْ حَتَّىٰ نَعْلَمَ ٱلْمُجَـٰهِدِينَ مِنكُمْ وَٱلصَّـٰبِرِينَ وَنَبْلُوَا۟ أَخْبَارَكُمْ
walanabluwannakum ḥattā naʿlama l-mujāhidīna minkum wal-ṣābirīna wanabluwā akhbārakum
Kuma lalle ne, Munã jarraba ku, har Mu san mãsu jihãdi daga cikinku da mãsu haƙuri kuma Muna jbrraba lãbãran ku.
إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ وَصَدُّوا۟ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ وَشَآقُّوا۟ ٱلرَّسُولَ مِنۢ بَعْدِ مَا تَبَيَّنَ لَهُمُ ٱلْهُدَىٰ لَن يَضُرُّوا۟ ٱللَّهَ شَيْـًۭٔا وَسَيُحْبِطُ أَعْمَـٰلَهُمْ
inna alladhīna kafarū waṣaddū ʿan sabīli l-lahi washāqqū l-rasūla min baʿdi mā tabayyana lahumu l-hudā lan yaḍurrū l-laha shayan wasayuḥ'biṭu aʿmālahum
Lalle ne, waɗanda suka kãfirta, kuma suka kange daga tafarkin Allah, kuma suka saɓa wa Manzon sa a bãyan shiriyar ta bayyana a gare su, bã za su cũci Allah da kõme ba, kuma zã Ya ɓãta ayyukansu.
۞ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓا۟ أَطِيعُوا۟ ٱللَّهَ وَأَطِيعُوا۟ ٱلرَّسُولَ وَلَا تُبْطِلُوٓا۟ أَعْمَـٰلَكُمْ
yāayyuhā alladhīna āmanū aṭīʿū l-laha wa-aṭīʿū l-rasūla walā tub'ṭilū aʿmālakum
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi ɗã'a ga Allah, kuma ku yi ɗa'a ga Manzon Sa, kuma kada 1ku ɓãta ayyukanku.
إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ وَصَدُّوا۟ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ ثُمَّ مَاتُوا۟ وَهُمْ كُفَّارٌۭ فَلَن يَغْفِرَ ٱللَّهُ لَهُمْ
inna alladhīna kafarū waṣaddū ʿan sabīli l-lahi thumma mātū wahum kuffārun falan yaghfira l-lahu lahum
Lalle ne waɗanda suka kãfirta sa'an nan kuma suka kange (mutãne) daga tafarkin Allah, sa'an nan suka mutu, alhãli kuwa sunã kãfirai, to, Allah bã zai yi gãfara ba a gare su.
فَلَا تَهِنُوا۟ وَتَدْعُوٓا۟ إِلَى ٱلسَّلْمِ وَأَنتُمُ ٱلْأَعْلَوْنَ وَٱللَّهُ مَعَكُمْ وَلَن يَتِرَكُمْ أَعْمَـٰلَكُمْ
falā tahinū watadʿū ilā l-salmi wa-antumu l-aʿlawna wal-lahu maʿakum walan yatirakum aʿmālakum
Sabõda haka kada ku yi rauni, kuma (kada) ku yi kira zũwaga sulhi alhãli kuwa kũ ne mafiɗaukaka kuma Allah na tãre da ku, kuma bã, zai naƙasa muku ayyukanku ba.
إِنَّمَا ٱلْحَيَوٰةُ ٱلدُّنْيَا لَعِبٌۭ وَلَهْوٌۭ ۚ وَإِن تُؤْمِنُوا۟ وَتَتَّقُوا۟ يُؤْتِكُمْ أُجُورَكُمْ وَلَا يَسْـَٔلْكُمْ أَمْوَٰلَكُمْ
innamā l-ḥayatu l-dun'yā laʿibun walahwun wa-in tu'minū watattaqū yu'tikum ujūrakum walā yasalkum amwālakum
Rãyuwar dũniya, wãsã da abin shagala kawai1 ce, kuma idan kun yi ĩmãni, kuma kun yi taƙawa, Allah zai kãwo muku ijarõrinku, kuma bã zai tambaye ku dũkiyarku ba.
إِن يَسْـَٔلْكُمُوهَا فَيُحْفِكُمْ تَبْخَلُوا۟ وَيُخْرِجْ أَضْغَـٰنَكُمْ
in yasalkumūhā fayuḥ'fikum tabkhalū wayukh'rij aḍghānakum
Dã Allah zai tambaye ku su (dũkiyõyin) har Ya wajabta muku bãyarwa, zã ku yi rõwa kuma Ya fitar da miyãgun ƙulle-ƙullenku.
هَـٰٓأَنتُمْ هَـٰٓؤُلَآءِ تُدْعَوْنَ لِتُنفِقُوا۟ فِى سَبِيلِ ٱللَّهِ فَمِنكُم مَّن يَبْخَلُ ۖ وَمَن يَبْخَلْ فَإِنَّمَا يَبْخَلُ عَن نَّفْسِهِۦ ۚ وَٱللَّهُ ٱلْغَنِىُّ وَأَنتُمُ ٱلْفُقَرَآءُ ۚ وَإِن تَتَوَلَّوْا۟ يَسْتَبْدِلْ قَوْمًا غَيْرَكُمْ ثُمَّ لَا يَكُونُوٓا۟ أَمْثَـٰلَكُم
hāantum hāulāi tud'ʿawna litunfiqū fī sabīli l-lahi faminkum man yabkhalu waman yabkhal fa-innamā yabkhalu ʿan nafsihi wal-lahu l-ghaniyu wa-antumu l-fuqarāu wa-in tatawallaw yastabdil qawman ghayrakum thumma lā yakūnū amthālakum
Ga ku, ya ku waɗannan! Anã kiran ku dõmin ku ciyar ga tafarkin Allah, sa'an nan daga cikinku akwai mai yin rõwa. Kuma wanda ke yin rõwa, to, yanã yin rõwar ne ga kansa. Kuma Allah ne wadãtacce alhãli kuwa kũ fãƙĩrai ne. Kuma idan kuka jũya (daga yi Masa ɗã'a), zai musanya waɗansu mutãne waɗansunku sa'an nan bã zã su kasance kwatankwacinku ba.