القصص
Al-Qasas
The Stories
طسٓمٓ
tta-seen-meem
T. S̃. M̃.
تِلْكَ ءَايَـٰتُ ٱلْكِتَـٰبِ ٱلْمُبِينِ
til'ka āyātu l-kitābi l-mubīni
Waɗancan ãyõyin Littãfi ne bayyananne.
نَتْلُوا۟ عَلَيْكَ مِن نَّبَإِ مُوسَىٰ وَفِرْعَوْنَ بِٱلْحَقِّ لِقَوْمٍۢ يُؤْمِنُونَ
natlū ʿalayka min naba-i mūsā wafir'ʿawna bil-ḥaqi liqawmin yu'minūna
Munã karantãwa a kanka daga lãbarin Mũsã da Fir'auna da gaskiya dõmin mutãne waɗanda suke yin ĩmãni.
إِنَّ فِرْعَوْنَ عَلَا فِى ٱلْأَرْضِ وَجَعَلَ أَهْلَهَا شِيَعًۭا يَسْتَضْعِفُ طَآئِفَةًۭ مِّنْهُمْ يُذَبِّحُ أَبْنَآءَهُمْ وَيَسْتَحْىِۦ نِسَآءَهُمْ ۚ إِنَّهُۥ كَانَ مِنَ ٱلْمُفْسِدِينَ
inna fir'ʿawna ʿalā fī l-arḍi wajaʿala ahlahā shiyaʿan yastaḍʿifu ṭāifatan min'hum yudhabbiḥu abnāahum wayastaḥyī nisāahum innahu kāna mina l-muf'sidīna
Lalle ne Fir'auna ya ɗaukaka a cikin ƙasa, kuma ya sanya mutãnenta ƙungiya-ƙungiya, yanã raunanar da wata jama'a daga gare su; yanã yanyanka ɗiyansu maza kuma yanã rãyar da mãtan. Lalle shĩ ya kasance daga mãsu ɓarna.
وَنُرِيدُ أَن نَّمُنَّ عَلَى ٱلَّذِينَ ٱسْتُضْعِفُوا۟ فِى ٱلْأَرْضِ وَنَجْعَلَهُمْ أَئِمَّةًۭ وَنَجْعَلَهُمُ ٱلْوَٰرِثِينَ
wanurīdu an namunna ʿalā alladhīna us'tuḍ'ʿifū fī l-arḍi wanajʿalahum a-immatan wanajʿalahumu l-wārithīna
Kuma Munã nufin Mu yi falala ga waɗanda aka raunanar a cikin ƙasar, kuma Mu sanya su shugabanni, kuma Mu sanya su magãda.
وَنُمَكِّنَ لَهُمْ فِى ٱلْأَرْضِ وَنُرِىَ فِرْعَوْنَ وَهَـٰمَـٰنَ وَجُنُودَهُمَا مِنْهُم مَّا كَانُوا۟ يَحْذَرُونَ
wanumakkina lahum fī l-arḍi wanuriya fir'ʿawna wahāmāna wajunūdahumā min'hum mā kānū yaḥdharūna
Kuma Mu tabbatar da su a cikin ƙasar, kuma Mu nũna wa Fir'auna da Hãmãna da rundunõninsu abin da suka kasance sunã sauna daga gare su.
وَأَوْحَيْنَآ إِلَىٰٓ أُمِّ مُوسَىٰٓ أَنْ أَرْضِعِيهِ ۖ فَإِذَا خِفْتِ عَلَيْهِ فَأَلْقِيهِ فِى ٱلْيَمِّ وَلَا تَخَافِى وَلَا تَحْزَنِىٓ ۖ إِنَّا رَآدُّوهُ إِلَيْكِ وَجَاعِلُوهُ مِنَ ٱلْمُرْسَلِينَ
wa-awḥaynā ilā ummi mūsā an arḍiʿīhi fa-idhā khif'ti ʿalayhi fa-alqīhi fī l-yami walā takhāfī walā taḥzanī innā rāddūhu ilayki wajāʿilūhu mina l-mur'salīna
Kuma Muka yi wahayi zuwa ga uwar Mũsa, cẽwa ki shãyar da shi, sai idan kin ji tsõro game da shi, to, ki jẽfa shi a cikin kõgi, kuma kada ki ji tsõro, kuma kada ki yi baƙin ciki. Lalle ne Mũ, Mãsu mayar da shi ne zuwa gare ki, kuma Mãsu sanya shi ne a cikin Manzanni
فَٱلْتَقَطَهُۥٓ ءَالُ فِرْعَوْنَ لِيَكُونَ لَهُمْ عَدُوًّۭا وَحَزَنًا ۗ إِنَّ فِرْعَوْنَ وَهَـٰمَـٰنَ وَجُنُودَهُمَا كَانُوا۟ خَـٰطِـِٔينَ
fal-taqaṭahu ālu fir'ʿawna liyakūna lahum ʿaduwwan waḥazanan inna fir'ʿawna wahāmāna wajunūdahumā kānū khāṭiīna
Sai mutãnen Fir'auna suka tsince shi, dõmin ya kasance maƙiyi da baƙin ciki a gare su. Lalle ne Fir'auna da Hãmãna da rundunõninsu, sun kasance mãsu aikin ganganci.
وَقَالَتِ ٱمْرَأَتُ فِرْعَوْنَ قُرَّتُ عَيْنٍۢ لِّى وَلَكَ ۖ لَا تَقْتُلُوهُ عَسَىٰٓ أَن يَنفَعَنَآ أَوْ نَتَّخِذَهُۥ وَلَدًۭا وَهُمْ لَا يَشْعُرُونَ
waqālati im'ra-atu fir'ʿawna qurratu ʿaynin lī walaka lā taqtulūhu ʿasā an yanfaʿanā aw nattakhidhahu waladan wahum lā yashʿurūna
Kuma matar1 Fir'auna ta ce ("Ka bar shi yanã) sanyin ido a gare ni da gare ka! Kada ka kashe shi, akwai fatan ya amfane mu, kõ mu riƙe Shi ɗã," alhãli kuwa sũ ba su sansance ba.
وَأَصْبَحَ فُؤَادُ أُمِّ مُوسَىٰ فَـٰرِغًا ۖ إِن كَادَتْ لَتُبْدِى بِهِۦ لَوْلَآ أَن رَّبَطْنَا عَلَىٰ قَلْبِهَا لِتَكُونَ مِنَ ٱلْمُؤْمِنِينَ
wa-aṣbaḥa fuādu ummi mūsā fārighan in kādat latub'dī bihi lawlā an rabaṭnā ʿalā qalbihā litakūna mina l-mu'minīna
Kuma zuciyar uwar Mũsã ta wãyi gari yõfintatta.1 Lalle ne, haƙĩƙa, ta yi kusa ta bayyanar da shi, bã dõmin Mun ɗaure zũciyarta ba, dõmin ta kasance daga mũminai.
وَقَالَتْ لِأُخْتِهِۦ قُصِّيهِ ۖ فَبَصُرَتْ بِهِۦ عَن جُنُبٍۢ وَهُمْ لَا يَشْعُرُونَ
waqālat li-ukh'tihi quṣṣīhi fabaṣurat bihi ʿan junubin wahum lā yashʿurūna
Kuma ta ce wa 'yar'uwarsa,1 "Ki bĩ shi." Sabõda haka sai ta lẽƙe shi daga gẽfe, alhãli sũ ba Su sani ba.
۞ وَحَرَّمْنَا عَلَيْهِ ٱلْمَرَاضِعَ مِن قَبْلُ فَقَالَتْ هَلْ أَدُلُّكُمْ عَلَىٰٓ أَهْلِ بَيْتٍۢ يَكْفُلُونَهُۥ لَكُمْ وَهُمْ لَهُۥ نَـٰصِحُونَ
waḥarramnā ʿalayhi l-marāḍiʿa min qablu faqālat hal adullukum ʿalā ahli baytin yakfulūnahu lakum wahum lahu nāṣiḥūna
Kuma Muka hana masa mãsu shãyai da mãma, a gabãnin haka sai ta ce: "Kõ in nũnamuku mutãnen wani gida, su yi muku renonsa alhãli kuwa su mãsu nasĩha ne a, gare shi?"
فَرَدَدْنَـٰهُ إِلَىٰٓ أُمِّهِۦ كَىْ تَقَرَّ عَيْنُهَا وَلَا تَحْزَنَ وَلِتَعْلَمَ أَنَّ وَعْدَ ٱللَّهِ حَقٌّۭ وَلَـٰكِنَّ أَكْثَرَهُمْ لَا يَعْلَمُونَ
faradadnāhu ilā ummihi kay taqarra ʿaynuhā walā taḥzana walitaʿlama anna waʿda l-lahi ḥaqqun walākinna aktharahum lā yaʿlamūna
Sai Muka mayar da shi zuwa ga uwarsa dõmin idanunta su yi sanyi, kuma bã zã ta yi baƙin ciki ba, kuma dõmin ta san cẽwa lalle wa'adin Allah gaskiya ne, amma kuma mafi yawansu ba su sani ba.
وَلَمَّا بَلَغَ أَشُدَّهُۥ وَٱسْتَوَىٰٓ ءَاتَيْنَـٰهُ حُكْمًۭا وَعِلْمًۭا ۚ وَكَذَٰلِكَ نَجْزِى ٱلْمُحْسِنِينَ
walammā balagha ashuddahu wa-is'tawā ātaynāhu ḥuk'man waʿil'man wakadhālika najzī l-muḥ'sinīna
Kuma a lõkacin da ya kai ƙarfinsa, kuma ya daidaita, Mun bã shi hukunci1 da ilmi kuma kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
وَدَخَلَ ٱلْمَدِينَةَ عَلَىٰ حِينِ غَفْلَةٍۢ مِّنْ أَهْلِهَا فَوَجَدَ فِيهَا رَجُلَيْنِ يَقْتَتِلَانِ هَـٰذَا مِن شِيعَتِهِۦ وَهَـٰذَا مِنْ عَدُوِّهِۦ ۖ فَٱسْتَغَـٰثَهُ ٱلَّذِى مِن شِيعَتِهِۦ عَلَى ٱلَّذِى مِنْ عَدُوِّهِۦ فَوَكَزَهُۥ مُوسَىٰ فَقَضَىٰ عَلَيْهِ ۖ قَالَ هَـٰذَا مِنْ عَمَلِ ٱلشَّيْطَـٰنِ ۖ إِنَّهُۥ عَدُوٌّۭ مُّضِلٌّۭ مُّبِينٌۭ
wadakhala l-madīnata ʿalā ḥīni ghaflatin min ahlihā fawajada fīhā rajulayni yaqtatilāni hādhā min shīʿatihi wahādhā min ʿaduwwihi fa-is'taghāthahu alladhī min shīʿatihi ʿalā alladhī min ʿaduwwihi fawakazahu mūsā faqaḍā ʿalayhi qāla hādhā min ʿamali l-shayṭāni innahu ʿaduwwun muḍillun mubīnun
Kuma sai ya shiga garin a lõkacin da mutãnen garin suka shagala, sai ya sãmu, a cikin garin, waɗansu maza biyu sunã faɗa, wannan daga ƙungiyarsa, kuma ɗayan daga maƙiyansa, sai wannann da yake daga ƙungiyarsa ya nẽmi ãgajinsa, sai Mũsã ya yi masa ƙulli, ya kashe shi. Ya ce: "Wannan aikin Shaiɗan ne, dõmin shi maƙiyi ne mai ɓatarwa, bayyananne!"
قَالَ رَبِّ إِنِّى ظَلَمْتُ نَفْسِى فَٱغْفِرْ لِى فَغَفَرَ لَهُۥٓ ۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلْغَفُورُ ٱلرَّحِيمُ
qāla rabbi innī ẓalamtu nafsī fa-igh'fir lī faghafara lahu innahu huwa l-ghafūru l-raḥīmu
Ya ce: "Ya Ubangijĩna! Lalle na zãlunci kaina, sai Ka yi mini gãfara." Sai Ya gãfarta masa, dõmin Shĩ ne Mai yawan gãfara, Mai jin ƙai.
قَالَ رَبِّ بِمَآ أَنْعَمْتَ عَلَىَّ فَلَنْ أَكُونَ ظَهِيرًۭا لِّلْمُجْرِمِينَ
qāla rabbi bimā anʿamta ʿalayya falan akūna ẓahīran lil'muj'rimīna
Ya ce: "Yã Ubangijĩna! Dõmin abin da Ka ni'imta shi a kaina, sahõda haka bã zan kasance mai taimako ga mãsu laifi ba."
فَأَصْبَحَ فِى ٱلْمَدِينَةِ خَآئِفًۭا يَتَرَقَّبُ فَإِذَا ٱلَّذِى ٱسْتَنصَرَهُۥ بِٱلْأَمْسِ يَسْتَصْرِخُهُۥ ۚ قَالَ لَهُۥ مُوسَىٰٓ إِنَّكَ لَغَوِىٌّۭ مُّبِينٌۭ
fa-aṣbaḥa fī l-madīnati khāifan yataraqqabu fa-idhā alladhī is'tanṣarahu bil-amsi yastaṣrikhuhu qāla lahu mūsā innaka laghawiyyun mubīnun
Sai ya wãyi gari a cikin birnin yanã mai tsõro, yanã sauna. Sai ga wanda ya nẽmi taimako daga gare shi a jiya, yanã nẽman ãgajinsa. Mũsã ya ce masa, "Lalle kai ɓatacce ne, bayyananne."
فَلَمَّآ أَنْ أَرَادَ أَن يَبْطِشَ بِٱلَّذِى هُوَ عَدُوٌّۭ لَّهُمَا قَالَ يَـٰمُوسَىٰٓ أَتُرِيدُ أَن تَقْتُلَنِى كَمَا قَتَلْتَ نَفْسًۢا بِٱلْأَمْسِ ۖ إِن تُرِيدُ إِلَّآ أَن تَكُونَ جَبَّارًۭا فِى ٱلْأَرْضِ وَمَا تُرِيدُ أَن تَكُونَ مِنَ ٱلْمُصْلِحِينَ
falammā an arāda an yabṭisha bi-alladhī huwa ʿaduwwun lahumā qāla yāmūsā aturīdu an taqtulanī kamā qatalta nafsan bil-amsi in turīdu illā an takūna jabbāran fī l-arḍi wamā turīdu an takūna mina l-muṣ'liḥīna
To, a lõkacin da Mũsã ya yi nufin ya damƙi wanda yake maƙiyi ne a gare su, (mai nẽman ãgajin) ya ce,1 "Ya Mũsã! Shin kanãnufin ka kashe ni ne kamar yadda ka kashe wani rai jiya? Ba ka son kõme fãce ka kasance mai tanƙwasawa11 a cikin ƙasa kuma bã ka nufin ka kasance daga mãsu kyautatãwa."
وَجَآءَ رَجُلٌۭ مِّنْ أَقْصَا ٱلْمَدِينَةِ يَسْعَىٰ قَالَ يَـٰمُوسَىٰٓ إِنَّ ٱلْمَلَأَ يَأْتَمِرُونَ بِكَ لِيَقْتُلُوكَ فَٱخْرُجْ إِنِّى لَكَ مِنَ ٱلنَّـٰصِحِينَ
wajāa rajulun min aqṣā l-madīnati yasʿā qāla yāmūsā inna l-mala-a yatamirūna bika liyaqtulūka fa-ukh'ruj innī laka mina l-nāṣiḥīna
Kuma wani mutum ya zo daga mafi nĩsan birnin yanã taliya da gaggãwa, ya ce: "Ya Mũsã! Lalle mashãwarta sunã shãwara game da kai dõmin su kashe ka sabõda haka ka fita. Lalle nĩ, mai nasĩha ne a gare ka."
فَخَرَجَ مِنْهَا خَآئِفًۭا يَتَرَقَّبُ ۖ قَالَ رَبِّ نَجِّنِى مِنَ ٱلْقَوْمِ ٱلظَّـٰلِمِينَ
fakharaja min'hā khāifan yataraqqabu qāla rabbi najjinī mina l-qawmi l-ẓālimīna
Sai ya fita daga gare ta,1 yanã mai jin tsõro yanã sauna. Ya ce: "Ya Ubangijĩna! Kã tsẽrar da ni daga mutãne azzãlumai."
وَلَمَّا تَوَجَّهَ تِلْقَآءَ مَدْيَنَ قَالَ عَسَىٰ رَبِّىٓ أَن يَهْدِيَنِى سَوَآءَ ٱلسَّبِيلِ
walammā tawajjaha til'qāa madyana qāla ʿasā rabbī an yahdiyanī sawāa l-sabīli
Kuma a lõkacin da ya fuskanci wajen Madyana, ya ce: "Inã fatan Ubangijĩna Ya shiryar da ni a kan madaidaiciyar hanya."
وَلَمَّا وَرَدَ مَآءَ مَدْيَنَ وَجَدَ عَلَيْهِ أُمَّةًۭ مِّنَ ٱلنَّاسِ يَسْقُونَ وَوَجَدَ مِن دُونِهِمُ ٱمْرَأَتَيْنِ تَذُودَانِ ۖ قَالَ مَا خَطْبُكُمَا ۖ قَالَتَا لَا نَسْقِى حَتَّىٰ يُصْدِرَ ٱلرِّعَآءُ ۖ وَأَبُونَا شَيْخٌۭ كَبِيرٌۭ
walammā warada māa madyana wajada ʿalayhi ummatan mina l-nāsi yasqūna wawajada min dūnihimu im'ra-atayni tadhūdāni qāla mā khaṭbukumā qālatā lā nasqī ḥattā yuṣ'dira l-riʿāu wa-abūnā shaykhun kabīrun
Kuma a lõkacin da ya isa mashãyar Madyana, ya sãmi wata jam'ar mutãne sunã shãyarwa, kuma a bãyansu ya sãmi waɗansu mãtã biyu sunã kõrar (tumãkinsu). Ya ce: "Mẽne ne shã'aninku?" Suka ce, "Bã zã mu iya shãyãrwa ba sai makiyãya sun fita, kuma ubanmu tsõho1 ne mai daraja."
فَسَقَىٰ لَهُمَا ثُمَّ تَوَلَّىٰٓ إِلَى ٱلظِّلِّ فَقَالَ رَبِّ إِنِّى لِمَآ أَنزَلْتَ إِلَىَّ مِنْ خَيْرٍۢ فَقِيرٌۭ
fasaqā lahumā thumma tawallā ilā l-ẓili faqāla rabbi innī limā anzalta ilayya min khayrin faqīrun
Sai ya shãyar musu, sa'an nan kuma ya jũya zuwa ga inuwa, sa'an nan ya ce: "Yã Ubangijĩna! Lalle ne, ga abin da Ka saukar zuwa gare ni na alhẽri ni mai bukãta ne."
فَجَآءَتْهُ إِحْدَىٰهُمَا تَمْشِى عَلَى ٱسْتِحْيَآءٍۢ قَالَتْ إِنَّ أَبِى يَدْعُوكَ لِيَجْزِيَكَ أَجْرَ مَا سَقَيْتَ لَنَا ۚ فَلَمَّا جَآءَهُۥ وَقَصَّ عَلَيْهِ ٱلْقَصَصَ قَالَ لَا تَخَفْ ۖ نَجَوْتَ مِنَ ٱلْقَوْمِ ٱلظَّـٰلِمِينَ
fajāathu iḥ'dāhumā tamshī ʿalā is'tiḥ'yāin qālat inna abī yadʿūka liyajziyaka ajra mā saqayta lanā falammā jāahu waqaṣṣa ʿalayhi l-qaṣaṣa qāla lā takhaf najawta mina l-qawmi l-ẓālimīna
Sai ɗayansu ta je masa, tanã tafiya a kan jin kunya, ta ce, "Ubãna yanã kiran ka, dõmin ya sãka maka ijãrar abin da ka shãyar sabõda mu." To, a lõkacin da ya je masa, ya gaya masa lãbãrinsa, ya ce: "Kada ka ji tsõro, kã tsĩra daga mutãne azzãlumai."
قَالَتْ إِحْدَىٰهُمَا يَـٰٓأَبَتِ ٱسْتَـْٔجِرْهُ ۖ إِنَّ خَيْرَ مَنِ ٱسْتَـْٔجَرْتَ ٱلْقَوِىُّ ٱلْأَمِينُ
qālat iḥ'dāhumā yāabati is'tajir'hu inna khayra mani is'tajarta l-qawiyu l-amīnu
¦ayarsu ta ce, "Yã Bãba! Ka bã shi aikin ijãra, lalle ne mafi alhẽrin wanda ka bai wa aikin ijãra shi ne mai ƙarfi1 amintacce."
قَالَ إِنِّىٓ أُرِيدُ أَنْ أُنكِحَكَ إِحْدَى ٱبْنَتَىَّ هَـٰتَيْنِ عَلَىٰٓ أَن تَأْجُرَنِى ثَمَـٰنِىَ حِجَجٍۢ ۖ فَإِنْ أَتْمَمْتَ عَشْرًۭا فَمِنْ عِندِكَ ۖ وَمَآ أُرِيدُ أَنْ أَشُقَّ عَلَيْكَ ۚ سَتَجِدُنِىٓ إِن شَآءَ ٱللَّهُ مِنَ ٱلصَّـٰلِحِينَ
qāla innī urīdu an unkiḥaka iḥ'dā ib'natayya hātayni ʿalā an tajuranī thamāniya ḥijajin fa-in atmamta ʿashran famin ʿindika wamā urīdu an ashuqqa ʿalayka satajidunī in shāa l-lahu mina l-ṣāliḥīna
Ya ce: "Lalle ne inã nufin in aurar da kai ɗayan 'yã'yãna biyu, waɗannan, a kan ka yi mini aikin ijãra shẽkara takwas to, idan ka cika gõma, to, daga, gare ka yake. Ba ni so in tsanantã maka, zã ka sãme ni, in Allah Ya so, daga sãlihai."
قَالَ ذَٰلِكَ بَيْنِى وَبَيْنَكَ ۖ أَيَّمَا ٱلْأَجَلَيْنِ قَضَيْتُ فَلَا عُدْوَٰنَ عَلَىَّ ۖ وَٱللَّهُ عَلَىٰ مَا نَقُولُ وَكِيلٌۭ
qāla dhālika baynī wabaynaka ayyamā l-ajalayni qaḍaytu falā ʿud'wāna ʿalayya wal-lahu ʿalā mā naqūlu wakīlun
Ya ce: "Wannan yanã a tsakanina da tsakãninka kõwane ɗayan adadin biyun na ƙãre, to, bãbu wani zãlunci a kaina. Kuma Allah ne Wakili ga abin da muke faɗa."
۞ فَلَمَّا قَضَىٰ مُوسَى ٱلْأَجَلَ وَسَارَ بِأَهْلِهِۦٓ ءَانَسَ مِن جَانِبِ ٱلطُّورِ نَارًۭا قَالَ لِأَهْلِهِ ٱمْكُثُوٓا۟ إِنِّىٓ ءَانَسْتُ نَارًۭا لَّعَلِّىٓ ءَاتِيكُم مِّنْهَا بِخَبَرٍ أَوْ جَذْوَةٍۢ مِّنَ ٱلنَّارِ لَعَلَّكُمْ تَصْطَلُونَ
falammā qaḍā mūsā l-ajala wasāra bi-ahlihi ānasa min jānibi l-ṭūri nāran qāla li-ahlihi um'kuthū innī ānastu nāran laʿallī ātīkum min'hā bikhabarin aw jadhwatin mina l-nāri laʿallakum taṣṭalūna
To, a lokacin da Mũsã ya ƙãre adadin kuma yanã tafiya da iyãlinsa, sai ya tsinkãyi wata Wutã daga gẽfen dũtse (¦ũr). Ya cewa iyãlinsa, "Ku dãkata, lalle ne nĩ, na tsinkãyi wata wutã, tsammãnĩna ni, mai zo muku ne daga gare ta da wani lãbãrĩ, kõ kuwa da guntun makãmashi daga Wutar don kõ ku ji ɗimi."
فَلَمَّآ أَتَىٰهَا نُودِىَ مِن شَـٰطِئِ ٱلْوَادِ ٱلْأَيْمَنِ فِى ٱلْبُقْعَةِ ٱلْمُبَـٰرَكَةِ مِنَ ٱلشَّجَرَةِ أَن يَـٰمُوسَىٰٓ إِنِّىٓ أَنَا ٱللَّهُ رَبُّ ٱلْعَـٰلَمِينَ
falammā atāhā nūdiya min shāṭi-i l-wādi l-aymani fī l-buq'ʿati l-mubārakati mina l-shajarati an yāmūsā innī anā l-lahu rabbu l-ʿālamīna
To, a lõkacin da ya jẽ wurinta (Wutar) aka kirã shi, daga gẽfen rãfin na dãma, a cikin wurin nan mai albarka, daga itãciyar (cẽwa) "Ya Mũsã! Lalle Nĩ ne Allah Ubangijin halittu."
وَأَنْ أَلْقِ عَصَاكَ ۖ فَلَمَّا رَءَاهَا تَهْتَزُّ كَأَنَّهَا جَآنٌّۭ وَلَّىٰ مُدْبِرًۭا وَلَمْ يُعَقِّبْ ۚ يَـٰمُوسَىٰٓ أَقْبِلْ وَلَا تَخَفْ ۖ إِنَّكَ مِنَ ٱلْـَٔامِنِينَ
wa-an alqi ʿaṣāka falammā raāhā tahtazzu ka-annahā jānnun wallā mud'biran walam yuʿaqqib yāmūsā aqbil walā takhaf innaka mina l-āminīna
"Kuma ka jẽfa sandarka." To, a lõkacin da ya gan ta, tanã girgiza kamar ƙaramar macijiya, ya jũya yanã mai bãyar da bãya, bai kõma ba. "Ya Mũsã! Ka fuskanto, kuma kada ka ji tsõro lalle ne kanã daga waɗanda ke amintattu."
ٱسْلُكْ يَدَكَ فِى جَيْبِكَ تَخْرُجْ بَيْضَآءَ مِنْ غَيْرِ سُوٓءٍۢ وَٱضْمُمْ إِلَيْكَ جَنَاحَكَ مِنَ ٱلرَّهْبِ ۖ فَذَٰنِكَ بُرْهَـٰنَانِ مِن رَّبِّكَ إِلَىٰ فِرْعَوْنَ وَمَلَإِي۟هِۦٓ ۚ إِنَّهُمْ كَانُوا۟ قَوْمًۭا فَـٰسِقِينَ
us'luk yadaka fī jaybika takhruj bayḍāa min ghayri sūin wa-uḍ'mum ilayka janāḥaka mina l-rahbi fadhānika bur'hānāni min rabbika ilā fir'ʿawna wamala-ihi innahum kānū qawman fāsiqīna
"Ka shigar da hannunka a cikin wuyan rĩgarka, ya fita fari, ba da wata cũta ba, kuma ka haɗa hannuwanka ga kãfaɗunka, dõmin tsõro (ya gushe daga gare ka). To, waɗannan abũbuwa dalĩlai biyu ne daga Ubangijinka zuwa ga Fir'auna da 'yan Majalisarsa. Lalle sun kasance mutãne ne fãsiƙai."
قَالَ رَبِّ إِنِّى قَتَلْتُ مِنْهُمْ نَفْسًۭا فَأَخَافُ أَن يَقْتُلُونِ
qāla rabbi innī qataltu min'hum nafsan fa-akhāfu an yaqtulūni
Ya ce: "Yã Ubangijĩna! Lalle nã kashe wani rai daga gare su, dõmin haka inã tsõron kada su kashe ni."
وَأَخِى هَـٰرُونُ هُوَ أَفْصَحُ مِنِّى لِسَانًۭا فَأَرْسِلْهُ مَعِىَ رِدْءًۭا يُصَدِّقُنِىٓ ۖ إِنِّىٓ أَخَافُ أَن يُكَذِّبُونِ
wa-akhī hārūnu huwa afṣaḥu minnī lisānan fa-arsil'hu maʿiya rid'an yuṣaddiqunī innī akhāfu an yukadhibūni
"Kuma ɗan'uwana Hãrũna shĩ ne mafi fasãha daga gareni, ga harshe, sabõda haka Ka aika shi tãre da ni, yanã mai taimako, yanã gaskata ni, lalle ne inã tsõron su ƙaryata ni."
قَالَ سَنَشُدُّ عَضُدَكَ بِأَخِيكَ وَنَجْعَلُ لَكُمَا سُلْطَـٰنًۭا فَلَا يَصِلُونَ إِلَيْكُمَا ۚ بِـَٔايَـٰتِنَآ أَنتُمَا وَمَنِ ٱتَّبَعَكُمَا ٱلْغَـٰلِبُونَ
qāla sanashuddu ʿaḍudaka bi-akhīka wanajʿalu lakumā sul'ṭānan falā yaṣilūna ilaykumā biāyātinā antumā wamani ittabaʿakumā l-ghālibūna
Ya ce: "Zã Mu ƙarfafa damtsenka game da ɗan'uwanka kuma Mu sanya muku wani dalĩli, sabõda haka bã zã su sãdu zuwa gareku ba, tãre da ãyõyinMu, kũ da waɗanda suka bĩ ku ne marinjãya."
فَلَمَّا جَآءَهُم مُّوسَىٰ بِـَٔايَـٰتِنَا بَيِّنَـٰتٍۢ قَالُوا۟ مَا هَـٰذَآ إِلَّا سِحْرٌۭ مُّفْتَرًۭى وَمَا سَمِعْنَا بِهَـٰذَا فِىٓ ءَابَآئِنَا ٱلْأَوَّلِينَ
falammā jāahum mūsā biāyātinā bayyinātin qālū mā hādhā illā siḥ'run muf'taran wamā samiʿ'nā bihādhā fī ābāinā l-awalīna
To, a lõkacin da Mũsã ya jẽ musu da ãyõyinMu bayyanannu, suka ce: "Wannan ba kõme ba sai sihiri, wanda aka ƙãga, kuma ba mu ji wannan ba daga wajen ubanninmu na farko."
وَقَالَ مُوسَىٰ رَبِّىٓ أَعْلَمُ بِمَن جَآءَ بِٱلْهُدَىٰ مِنْ عِندِهِۦ وَمَن تَكُونُ لَهُۥ عَـٰقِبَةُ ٱلدَّارِ ۖ إِنَّهُۥ لَا يُفْلِحُ ٱلظَّـٰلِمُونَ
waqāla mūsā rabbī aʿlamu biman jāa bil-hudā min ʿindihi waman takūnu lahu ʿāqibatu l-dāri innahu lā yuf'liḥu l-ẓālimūna
Kuma Mũsã ya ce: "Ubangijĩna ne Mafi sanin wanda ya zo da shiriya daga gare Shi, da wanda ãƙibar gida take kasancẽwa agare shi. Lalle ne mãsu zãlunci bã su cin nasara."
وَقَالَ فِرْعَوْنُ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلْمَلَأُ مَا عَلِمْتُ لَكُم مِّنْ إِلَـٰهٍ غَيْرِى فَأَوْقِدْ لِى يَـٰهَـٰمَـٰنُ عَلَى ٱلطِّينِ فَٱجْعَل لِّى صَرْحًۭا لَّعَلِّىٓ أَطَّلِعُ إِلَىٰٓ إِلَـٰهِ مُوسَىٰ وَإِنِّى لَأَظُنُّهُۥ مِنَ ٱلْكَـٰذِبِينَ
waqāla fir'ʿawnu yāayyuhā l-mala-u mā ʿalim'tu lakum min ilāhin ghayrī fa-awqid lī yāhāmānu ʿalā l-ṭīni fa-ij'ʿal lī ṣarḥan laʿallī aṭṭaliʿu ilā ilāhi mūsā wa-innī la-aẓunnuhu mina l-kādhibīna
Kuma Fir'auna ya ce: "Yã ku mashãwarta! Ban san kunã da wani abin bautãwa baicina ba, sabõda haka ka hũra mini wuta, ya Hãmãnu! a kan lãka1 (dõmin a yi tũbali), sa'an nan ka sanya mini bẽne tsammãnĩna zan ninƙãya zuwa ga Ubangijin Mũsã kuma lalle ne ni, haƙĩƙa, inã zaton sa daga maƙaryata."
وَٱسْتَكْبَرَ هُوَ وَجُنُودُهُۥ فِى ٱلْأَرْضِ بِغَيْرِ ٱلْحَقِّ وَظَنُّوٓا۟ أَنَّهُمْ إِلَيْنَا لَا يُرْجَعُونَ
wa-is'takbara huwa wajunūduhu fī l-arḍi bighayri l-ḥaqi waẓannū annahum ilaynā lā yur'jaʿūna
Kuma ya kangare, shi da rundunõninsa a cikin ƙasa, bã da haƙƙi ba kuma suka zaci cẽwa sũ, bã zã a mayar da su zuwa gare Mu ba.
فَأَخَذْنَـٰهُ وَجُنُودَهُۥ فَنَبَذْنَـٰهُمْ فِى ٱلْيَمِّ ۖ فَٱنظُرْ كَيْفَ كَانَ عَـٰقِبَةُ ٱلظَّـٰلِمِينَ
fa-akhadhnāhu wajunūdahu fanabadhnāhum fī l-yami fa-unẓur kayfa kāna ʿāqibatu l-ẓālimīna
Sai Muka kãma shi, shĩ da rundunõninsa sai Muka jẽfa su a cikin kõgi. Sai ka dũbi yaddaãƙibar azzãlumai ta kasance.
وَجَعَلْنَـٰهُمْ أَئِمَّةًۭ يَدْعُونَ إِلَى ٱلنَّارِ ۖ وَيَوْمَ ٱلْقِيَـٰمَةِ لَا يُنصَرُونَ
wajaʿalnāhum a-immatan yadʿūna ilā l-nāri wayawma l-qiyāmati lā yunṣarūna
Kuma Muka sanya su shũgabanni, sunã kira zuwa ga wuta, kuma a Rãnar ¡iyãma bã zã a taimake su ba.
وَأَتْبَعْنَـٰهُمْ فِى هَـٰذِهِ ٱلدُّنْيَا لَعْنَةًۭ ۖ وَيَوْمَ ٱلْقِيَـٰمَةِ هُم مِّنَ ٱلْمَقْبُوحِينَ
wa-atbaʿnāhum fī hādhihi l-dun'yā laʿnatan wayawma l-qiyāmati hum mina l-maqbūḥīna
Kuma Muka biyar musu da la'ana a cikin wannan dũniyakuma a Rãnar ¡iyãma sunã daga waɗanda aka mũnana halittarsu.
وَلَقَدْ ءَاتَيْنَا مُوسَى ٱلْكِتَـٰبَ مِنۢ بَعْدِ مَآ أَهْلَكْنَا ٱلْقُرُونَ ٱلْأُولَىٰ بَصَآئِرَ لِلنَّاسِ وَهُدًۭى وَرَحْمَةًۭ لَّعَلَّهُمْ يَتَذَكَّرُونَ
walaqad ātaynā mūsā l-kitāba min baʿdi mā ahlaknā l-qurūna l-ūlā baṣāira lilnnāsi wahudan waraḥmatan laʿallahum yatadhakkarūna
Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun bai wa Mũsã Littãfi daga bãyan Mun halakar da ƙarnõnin farko, dõmin su zama abũbuwan kula ga mutãne, da shiriya da rahama, tsammãninsu sunã tunãwa.
وَمَا كُنتَ بِجَانِبِ ٱلْغَرْبِىِّ إِذْ قَضَيْنَآ إِلَىٰ مُوسَى ٱلْأَمْرَ وَمَا كُنتَ مِنَ ٱلشَّـٰهِدِينَ
wamā kunta bijānibi l-gharbiyi idh qaḍaynā ilā mūsā l-amra wamā kunta mina l-shāhidīna
Kuma ba ka kasance ba ga gẽfen rãfi na yamma a lõkacin da Muka hukunta al'amaru zuwa ga Mũsã, kuma ba ka kasance daga halartattu ba.
وَلَـٰكِنَّآ أَنشَأْنَا قُرُونًۭا فَتَطَاوَلَ عَلَيْهِمُ ٱلْعُمُرُ ۚ وَمَا كُنتَ ثَاوِيًۭا فِىٓ أَهْلِ مَدْيَنَ تَتْلُوا۟ عَلَيْهِمْ ءَايَـٰتِنَا وَلَـٰكِنَّا كُنَّا مُرْسِلِينَ
walākinnā anshanā qurūnan fataṭāwala ʿalayhimu l-ʿumuru wamā kunta thāwiyan fī ahli madyana tatlū ʿalayhim āyātinā walākinnā kunnā mur'silīna
Kuma amma Mũ, Mun ƙãga halittawar wasu ƙarnõni har lõkatan rãyuwa suka yi tsawo a kansu. Kuma ba ka kasance mazauni ba a cikin mutãnen Madyana, kanã karanta musu ãyõyinMu, amma Mũ Mun kasãnce mãsu aikãwa (da kai game1 da waɗancan lãbarai).
وَمَا كُنتَ بِجَانِبِ ٱلطُّورِ إِذْ نَادَيْنَا وَلَـٰكِن رَّحْمَةًۭ مِّن رَّبِّكَ لِتُنذِرَ قَوْمًۭا مَّآ أَتَىٰهُم مِّن نَّذِيرٍۢ مِّن قَبْلِكَ لَعَلَّهُمْ يَتَذَكَّرُونَ
wamā kunta bijānibi l-ṭūri idh nādaynā walākin raḥmatan min rabbika litundhira qawman mā atāhum min nadhīrin min qablika laʿallahum yatadhakkarūna
Kuma ba ka kasance ga gẽfen dũtse ba a lõkacin da Muka yi kira, kuma amma dõmin rahama daga Ubangijinka, dõmin ka yi gargaɗi ga mutãne waɗanda suke wani mai gargaɗi a gabãninka bai je musu ba, tsammãninsu sunã tunãwa.
وَلَوْلَآ أَن تُصِيبَهُم مُّصِيبَةٌۢ بِمَا قَدَّمَتْ أَيْدِيهِمْ فَيَقُولُوا۟ رَبَّنَا لَوْلَآ أَرْسَلْتَ إِلَيْنَا رَسُولًۭا فَنَتَّبِعَ ءَايَـٰتِكَ وَنَكُونَ مِنَ ٱلْمُؤْمِنِينَ
walawlā an tuṣībahum muṣībatun bimā qaddamat aydīhim fayaqūlū rabbanā lawlā arsalta ilaynā rasūlan fanattabiʿa āyātika wanakūna mina l-mu'minīna
Kuma bã dõmin wata masĩfa ta sãme su ba sabõda abin da hannayensu suka gabãtar, su ce: "Yã Ubangijinmu! Don me ba Ka aiko wani Manzo zuwa gare mu ba, har mu dinga bĩn ãyõyinKa, kuma mu kasance daga mũminai?"
فَلَمَّا جَآءَهُمُ ٱلْحَقُّ مِنْ عِندِنَا قَالُوا۟ لَوْلَآ أُوتِىَ مِثْلَ مَآ أُوتِىَ مُوسَىٰٓ ۚ أَوَلَمْ يَكْفُرُوا۟ بِمَآ أُوتِىَ مُوسَىٰ مِن قَبْلُ ۖ قَالُوا۟ سِحْرَانِ تَظَـٰهَرَا وَقَالُوٓا۟ إِنَّا بِكُلٍّۢ كَـٰفِرُونَ
falammā jāahumu l-ḥaqu min ʿindinā qālū lawlā ūtiya mith'la mā ūtiya mūsā awalam yakfurū bimā ūtiya mūsā min qablu qālū siḥ'rāni taẓāharā waqālū innā bikullin kāfirūna
Sa'an nan a lõkacin da gaskiya ta jẽ musu daga wurin Mu, suka ce: "Don me ba a bã shi kamar abin da aka bai wa Mũsã ba?" Shin kuma ba su kãfirta ba da abin da aka bai wa Mũsã a gabãnin (wannan)? suka ce: "Sihirõri biyu ne suka taimaki jũna," kuma suka ce: "Lalle ne mũ, mãsu kãfirta ne ga dukansu?"
قُلْ فَأْتُوا۟ بِكِتَـٰبٍۢ مِّنْ عِندِ ٱللَّهِ هُوَ أَهْدَىٰ مِنْهُمَآ أَتَّبِعْهُ إِن كُنتُمْ صَـٰدِقِينَ
qul fatū bikitābin min ʿindi l-lahi huwa ahdā min'humā attabiʿ'hu in kuntum ṣādiqīna
Ka ce: "To ku zo da wani littãfi daga, wurin Allah, wanda yake shi ne mafi shiryarwa daga gare su, in bĩ shi, idan kunkasance mãsu gaskiya."
فَإِن لَّمْ يَسْتَجِيبُوا۟ لَكَ فَٱعْلَمْ أَنَّمَا يَتَّبِعُونَ أَهْوَآءَهُمْ ۚ وَمَنْ أَضَلُّ مِمَّنِ ٱتَّبَعَ هَوَىٰهُ بِغَيْرِ هُدًۭى مِّنَ ٱللَّهِ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَهْدِى ٱلْقَوْمَ ٱلظَّـٰلِمِينَ
fa-in lam yastajībū laka fa-iʿ'lam annamā yattabiʿūna ahwāahum waman aḍallu mimmani ittabaʿa hawāhu bighayri hudan mina l-lahi inna l-laha lā yahdī l-qawma l-ẓālimīna
To, idan ba su karɓa maka ba to sai ka sani sunã bin son zuciyarsu ne kawai, kuma wãne ne mafi ɓata daga wanda ya bi son zuciyarsa, bã tãre da wata shiriya daga Allah ba? Lalle ne, Allah bã ya shiryar da mutãne azzãlumai.
۞ وَلَقَدْ وَصَّلْنَا لَهُمُ ٱلْقَوْلَ لَعَلَّهُمْ يَتَذَكَّرُونَ
walaqad waṣṣalnā lahumu l-qawla laʿallahum yatadhakkarūna
Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun sãdar1 da magana sabõda su, tsammãninsu, suna tunãni.
ٱلَّذِينَ ءَاتَيْنَـٰهُمُ ٱلْكِتَـٰبَ مِن قَبْلِهِۦ هُم بِهِۦ يُؤْمِنُونَ
alladhīna ātaynāhumu l-kitāba min qablihi hum bihi yu'minūna
Waɗanda Muka bã su littãfi daga gabãninsa (Alƙur'ãni), su mãsu ĩmãni ne da shi.1
وَإِذَا يُتْلَىٰ عَلَيْهِمْ قَالُوٓا۟ ءَامَنَّا بِهِۦٓ إِنَّهُ ٱلْحَقُّ مِن رَّبِّنَآ إِنَّا كُنَّا مِن قَبْلِهِۦ مُسْلِمِينَ
wa-idhā yut'lā ʿalayhim qālū āmannā bihi innahu l-ḥaqu min rabbinā innā kunnā min qablihi mus'limīna
Kuma idan anã karanta shi a kansu, sai su ce: "Mun yi ĩmãni da shi, lalle shi ne gaskiya daga Ubangijinmu. Lalle mũ, mun kasance a gabãninsa masu sallamãwa."
أُو۟لَـٰٓئِكَ يُؤْتَوْنَ أَجْرَهُم مَّرَّتَيْنِ بِمَا صَبَرُوا۟ وَيَدْرَءُونَ بِٱلْحَسَنَةِ ٱلسَّيِّئَةَ وَمِمَّا رَزَقْنَـٰهُمْ يُنفِقُونَ
ulāika yu'tawna ajrahum marratayni bimā ṣabarū wayadraūna bil-ḥasanati l-sayi-ata wamimmā razaqnāhum yunfiqūna
Waɗancan anã ba su lãdansu sau biyu, sabõda haƙurin da suka yi, kuma da kyautatãwa suna tunkuɗewar mũnanãwa kuma daga abin da Muka azũrtã susunã ciyarwa.
وَإِذَا سَمِعُوا۟ ٱللَّغْوَ أَعْرَضُوا۟ عَنْهُ وَقَالُوا۟ لَنَآ أَعْمَـٰلُنَا وَلَكُمْ أَعْمَـٰلُكُمْ سَلَـٰمٌ عَلَيْكُمْ لَا نَبْتَغِى ٱلْجَـٰهِلِينَ
wa-idhā samiʿū l-laghwa aʿraḍū ʿanhu waqālū lanā aʿmālunā walakum aʿmālukum salāmun ʿalaykum lā nabtaghī l-jāhilīna
Kuma idan sun ji yãsassar magana sukan kau da kai daga barinta, kuma sukan ce, "Ayyukanmu sunã a gare mu, kuma ayyukanku sunã a gare ku, aminci ya tabbata a kanmu bã mu nẽman jãhilai (da husũma)."1
إِنَّكَ لَا تَهْدِى مَنْ أَحْبَبْتَ وَلَـٰكِنَّ ٱللَّهَ يَهْدِى مَن يَشَآءُ ۚ وَهُوَ أَعْلَمُ بِٱلْمُهْتَدِينَ
innaka lā tahdī man aḥbabta walākinna l-laha yahdī man yashāu wahuwa aʿlamu bil-muh'tadīna
Lalle ne kai bã ka shiryar1 da wanda ka so, amma kuma Allah Yanã shiryar da wanda Yake so, kuma Shi ne Mafi sani daga mãsu shiryuwa.
وَقَالُوٓا۟ إِن نَّتَّبِعِ ٱلْهُدَىٰ مَعَكَ نُتَخَطَّفْ مِنْ أَرْضِنَآ ۚ أَوَلَمْ نُمَكِّن لَّهُمْ حَرَمًا ءَامِنًۭا يُجْبَىٰٓ إِلَيْهِ ثَمَرَٰتُ كُلِّ شَىْءٍۢ رِّزْقًۭا مِّن لَّدُنَّا وَلَـٰكِنَّ أَكْثَرَهُمْ لَا يَعْلَمُونَ
waqālū in nattabiʿi l-hudā maʿaka nutakhaṭṭaf min arḍinā awalam numakkin lahum ḥaraman āminan yuj'bā ilayhi thamarātu kulli shayin riz'qan min ladunnā walākinna aktharahum lā yaʿlamūna
Kuma suka ce: "Idan mun bi shiriya tãre da kai anã fizge mu1 daga ƙasamiu." Shin, ba Mu tabbatar musu da mallakar Hurumi ba, ya zama amintacce, anã jãwõwa zuwa gare shi, 'ya'yan itãcen kõwane iri, bisa ga azurtãwa daga gare Mu? Amma kuma mafi yawansu ba su sani ba.
وَكَمْ أَهْلَكْنَا مِن قَرْيَةٍۭ بَطِرَتْ مَعِيشَتَهَا ۖ فَتِلْكَ مَسَـٰكِنُهُمْ لَمْ تُسْكَن مِّنۢ بَعْدِهِمْ إِلَّا قَلِيلًۭا ۖ وَكُنَّا نَحْنُ ٱلْوَٰرِثِينَ
wakam ahlaknā min qaryatin baṭirat maʿīshatahā fatil'ka masākinuhum lam tus'kan min baʿdihim illā qalīlan wakunnā naḥnu l-wārithīna
Kuma da yawa Muka halakar da wata alƙarya wadda ta yi butulci ga rãyuwarta. To, waɗancan gidãjensu ne, ba a zaune su ba, a bãyansu, fãce kaɗan. Kuma mun kasance Mũ ne Magãda.
وَمَا كَانَ رَبُّكَ مُهْلِكَ ٱلْقُرَىٰ حَتَّىٰ يَبْعَثَ فِىٓ أُمِّهَا رَسُولًۭا يَتْلُوا۟ عَلَيْهِمْ ءَايَـٰتِنَا ۚ وَمَا كُنَّا مُهْلِكِى ٱلْقُرَىٰٓ إِلَّا وَأَهْلُهَا ظَـٰلِمُونَ
wamā kāna rabbuka muh'lika l-qurā ḥattā yabʿatha fī ummihā rasūlan yatlū ʿalayhim āyātinā wamā kunnā muh'likī l-qurā illā wa-ahluhā ẓālimūna
Kuma Ubangijinka bai kasance Mai halaka alƙaryu ba, sai Ya aika a cikin hedkwatarsu da wani Manzo yanã karanta ãyõyinMu a kansu. Kuma ba Mu kasance Mãsu halaka alƙaryu ba, fãce mutanensu sun kasance mãsu zãlunci.
وَمَآ أُوتِيتُم مِّن شَىْءٍۢ فَمَتَـٰعُ ٱلْحَيَوٰةِ ٱلدُّنْيَا وَزِينَتُهَا ۚ وَمَا عِندَ ٱللَّهِ خَيْرٌۭ وَأَبْقَىٰٓ ۚ أَفَلَا تَعْقِلُونَ
wamā ūtītum min shayin famatāʿu l-ḥayati l-dun'yā wazīnatuhā wamā ʿinda l-lahi khayrun wa-abqā afalā taʿqilūna
Kuma abin da aka bã su daga kõme, to, jin dãɗin rayuwar dũniya ne da ƙawarta. Kuma abin da ke wurin Allah, shĩ ne mafi alhẽri, knma mafi wanzuwa. Shin bã ku hankalta?
أَفَمَن وَعَدْنَـٰهُ وَعْدًا حَسَنًۭا فَهُوَ لَـٰقِيهِ كَمَن مَّتَّعْنَـٰهُ مَتَـٰعَ ٱلْحَيَوٰةِ ٱلدُّنْيَا ثُمَّ هُوَ يَوْمَ ٱلْقِيَـٰمَةِ مِنَ ٱلْمُحْضَرِينَ
afaman waʿadnāhu waʿdan ḥasanan fahuwa lāqīhi kaman mattaʿnāhu matāʿa l-ḥayati l-dun'yā thumma huwa yawma l-qiyāmati mina l-muḥ'ḍarīna
Shin fa, wanda Muka yi wa wa'adi, wa'adi mai kyau, sa'an nan shĩ mai haɗuwa da shi ne, yanã zama kamar wanda Muka jiyar da shi ɗan dãɗi, dãɗin rãyuwar dũniya, sa'an nan shi a Rãnar ¡iyãma yanã daga mãsu shiga wuta?
وَيَوْمَ يُنَادِيهِمْ فَيَقُولُ أَيْنَ شُرَكَآءِىَ ٱلَّذِينَ كُنتُمْ تَزْعُمُونَ
wayawma yunādīhim fayaqūlu ayna shurakāiya alladhīna kuntum tazʿumūna
Kuma rãnar da (Allah) Yake kiran su sa'an nan Ya ce: "Inã abõkan tãrayyaTa, waɗanda kuka kasance kunã rayãwa?"
قَالَ ٱلَّذِينَ حَقَّ عَلَيْهِمُ ٱلْقَوْلُ رَبَّنَا هَـٰٓؤُلَآءِ ٱلَّذِينَ أَغْوَيْنَآ أَغْوَيْنَـٰهُمْ كَمَا غَوَيْنَا ۖ تَبَرَّأْنَآ إِلَيْكَ ۖ مَا كَانُوٓا۟ إِيَّانَا يَعْبُدُونَ
qāla alladhīna ḥaqqa ʿalayhimu l-qawlu rabbanā hāulāi alladhīna aghwaynā aghwaynāhum kamā ghawaynā tabarranā ilayka mā kānū iyyānā yaʿbudūna
Waɗanda magana ta wajaba a kansu, su ce: "Yã Ubangijinmu! Waɗannan sũ ne waɗanda muka halakar mun halakar da su kamar yadda muka halaka. Mun barranta zuwa gare Ka, ba su kasance mũ suke bautã wa ba."
وَقِيلَ ٱدْعُوا۟ شُرَكَآءَكُمْ فَدَعَوْهُمْ فَلَمْ يَسْتَجِيبُوا۟ لَهُمْ وَرَأَوُا۟ ٱلْعَذَابَ ۚ لَوْ أَنَّهُمْ كَانُوا۟ يَهْتَدُونَ
waqīla id'ʿū shurakāakum fadaʿawhum falam yastajībū lahum wara-awū l-ʿadhāba law annahum kānū yahtadūna
Kuma a ce ku kirãwo abõkan tãrayyar ɗinku, sai su kira su, sai ba su amsa ba, kuma su ga azãbar. Dã dai lalle su sun kasance snnã shiryuwa1!
وَيَوْمَ يُنَادِيهِمْ فَيَقُولُ مَاذَآ أَجَبْتُمُ ٱلْمُرْسَلِينَ
wayawma yunādīhim fayaqūlu mādhā ajabtumu l-mur'salīna
Kuma rãnar da Yake kiran su, sa'an nan Ya ce: "Mẽne nekuka karɓa wa Mananni?"
فَعَمِيَتْ عَلَيْهِمُ ٱلْأَنۢبَآءُ يَوْمَئِذٍۢ فَهُمْ لَا يَتَسَآءَلُونَ
faʿamiyat ʿalayhimu l-anbāu yawma-idhin fahum lā yatasāalūna
Sai lãbãru su ɓace musu a rãnar nan sa'an nan bã zã su tambayi jũnansu ba.
فَأَمَّا مَن تَابَ وَءَامَنَ وَعَمِلَ صَـٰلِحًۭا فَعَسَىٰٓ أَن يَكُونَ مِنَ ٱلْمُفْلِحِينَ
fa-ammā man tāba waāmana waʿamila ṣāliḥan faʿasā an yakūna mina l-muf'liḥīna
To, amma wanda ya tũba, kuma ya yi ĩmãni' ya aikata aiki na ƙwarai, to, akwai fãtan su kasance daga mãsu cin nasara.
وَرَبُّكَ يَخْلُقُ مَا يَشَآءُ وَيَخْتَارُ ۗ مَا كَانَ لَهُمُ ٱلْخِيَرَةُ ۚ سُبْحَـٰنَ ٱللَّهِ وَتَعَـٰلَىٰ عَمَّا يُشْرِكُونَ
warabbuka yakhluqu mā yashāu wayakhtāru mā kāna lahumu l-khiyaratu sub'ḥāna l-lahi wataʿālā ʿammā yush'rikūna
Kuma Ubangijinka Yanã halitta abin da Yake so kuma Yake zãɓi. Zãɓi bai kasance a gare su ba. Tsarki ya tabbata ga Allah, kuma (Allah) Ya ɗaukaka daga barin abin da suke yi na shirka.
وَرَبُّكَ يَعْلَمُ مَا تُكِنُّ صُدُورُهُمْ وَمَا يُعْلِنُونَ
warabbuka yaʿlamu mā tukinnu ṣudūruhum wamā yuʿ'linūna
Kuma Ubangijinka Yanã sanin abin da zukãtansu ke ɓõyẽwa, da abin da suke bayyanãwa.
وَهُوَ ٱللَّهُ لَآ إِلَـٰهَ إِلَّا هُوَ ۖ لَهُ ٱلْحَمْدُ فِى ٱلْأُولَىٰ وَٱلْـَٔاخِرَةِ ۖ وَلَهُ ٱلْحُكْمُ وَإِلَيْهِ تُرْجَعُونَ
wahuwa l-lahu lā ilāha illā huwa lahu l-ḥamdu fī l-ūlā wal-ākhirati walahu l-ḥuk'mu wa-ilayhi tur'jaʿūna
Kuma Shĩ ne Allah, bãbu abin bautãwa fãce Shi. Kuma Shi ne abin gõdiya a cikin ta farko (dũniya), da ta ƙarshe (Lãhira). Kuma Shi ne da hukunci, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku.
قُلْ أَرَءَيْتُمْ إِن جَعَلَ ٱللَّهُ عَلَيْكُمُ ٱلَّيْلَ سَرْمَدًا إِلَىٰ يَوْمِ ٱلْقِيَـٰمَةِ مَنْ إِلَـٰهٌ غَيْرُ ٱللَّهِ يَأْتِيكُم بِضِيَآءٍ ۖ أَفَلَا تَسْمَعُونَ
qul ara-aytum in jaʿala l-lahu ʿalaykumu al-layla sarmadan ilā yawmi l-qiyāmati man ilāhun ghayru l-lahi yatīkum biḍiyāin afalā tasmaʿūna
Ka ce: "Shin, kun gani, idan Allah Ya sanya dare tutur a kanku har zuwa Rãnar ¡iyãma, wane abin bautãwa wanin Allah zai zo muku da haske? Shin, bã ku ji?"
قُلْ أَرَءَيْتُمْ إِن جَعَلَ ٱللَّهُ عَلَيْكُمُ ٱلنَّهَارَ سَرْمَدًا إِلَىٰ يَوْمِ ٱلْقِيَـٰمَةِ مَنْ إِلَـٰهٌ غَيْرُ ٱللَّهِ يَأْتِيكُم بِلَيْلٍۢ تَسْكُنُونَ فِيهِ ۖ أَفَلَا تُبْصِرُونَ
qul ara-aytum in jaʿala l-lahu ʿalaykumu l-nahāra sarmadan ilā yawmi l-qiyāmati man ilāhun ghayru l-lahi yatīkum bilaylin taskunūna fīhi afalā tub'ṣirūna
Ka ce: "Shin, kun gani, idan Allah Ya sanya yini a kanku tutur zuwa Rãnar ¡iyãma, wane abin bautãwa, wanin Allah, zai zo muku da dare wanda kunã natsuwa a cikinsa? Shin fa, bã ku gani?"
وَمِن رَّحْمَتِهِۦ جَعَلَ لَكُمُ ٱلَّيْلَ وَٱلنَّهَارَ لِتَسْكُنُوا۟ فِيهِ وَلِتَبْتَغُوا۟ مِن فَضْلِهِۦ وَلَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ
wamin raḥmatihi jaʿala lakumu al-layla wal-nahāra litaskunū fīhi walitabtaghū min faḍlihi walaʿallakum tashkurūna
"Kuma daga rahamarSa Ya sanya muku dare da yini dõmin ku natsu a cikinsa, kuma dõmin ku nẽma daga falalar Sa, kuma tsammãninku zã ku gõde."
وَيَوْمَ يُنَادِيهِمْ فَيَقُولُ أَيْنَ شُرَكَآءِىَ ٱلَّذِينَ كُنتُمْ تَزْعُمُونَ
wayawma yunādīhim fayaqūlu ayna shurakāiya alladhīna kuntum tazʿumūna
Kuma a rãnar da Yake kiran su ya ce: "Inã abõkan tarayya Ta, waɗanda kuka kasance kunã riyãwa"1
وَنَزَعْنَا مِن كُلِّ أُمَّةٍۢ شَهِيدًۭا فَقُلْنَا هَاتُوا۟ بُرْهَـٰنَكُمْ فَعَلِمُوٓا۟ أَنَّ ٱلْحَقَّ لِلَّهِ وَضَلَّ عَنْهُم مَّا كَانُوا۟ يَفْتَرُونَ
wanazaʿnā min kulli ummatin shahīdan faqul'nā hātū bur'hānakum faʿalimū anna l-ḥaqa lillahi waḍalla ʿanhum mā kānū yaftarūna
Kuma Muka zãre mai shaida daga kõwace al'umma, sa'an nan Muka ce: "Ku kãwo dalilinku." Sai suka san cẽwa lalle gaskiya ga Allah take. Kuma abin da suka kasance sunã ƙirƙirãwa na ƙarya ya ɓace daga barinsu.
۞ إِنَّ قَـٰرُونَ كَانَ مِن قَوْمِ مُوسَىٰ فَبَغَىٰ عَلَيْهِمْ ۖ وَءَاتَيْنَـٰهُ مِنَ ٱلْكُنُوزِ مَآ إِنَّ مَفَاتِحَهُۥ لَتَنُوٓأُ بِٱلْعُصْبَةِ أُو۟لِى ٱلْقُوَّةِ إِذْ قَالَ لَهُۥ قَوْمُهُۥ لَا تَفْرَحْ ۖ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُحِبُّ ٱلْفَرِحِينَ
inna qārūna kāna min qawmi mūsā fabaghā ʿalayhim waātaynāhu mina l-kunūzi mā inna mafātiḥahu latanūu bil-ʿuṣ'bati ulī l-quwati idh qāla lahu qawmuhu lā tafraḥ inna l-laha lā yuḥibbu l-fariḥīna
Lalle ne ¡ãrũna ya kasance daga mutãnen Mũsã, sai ya fita1 daga tsãrinsu alhãli Mun bã shi taskõkin abin da yake mabũɗansa sunã nauyi ga jama'a11 ma'abũta ƙarfi a lõkacin da mutãnensa suka ce masa, "Kada ka yi annashuwa, lalle ne Allah bã Ya son mãsu annashuwa."
وَٱبْتَغِ فِيمَآ ءَاتَىٰكَ ٱللَّهُ ٱلدَّارَ ٱلْـَٔاخِرَةَ ۖ وَلَا تَنسَ نَصِيبَكَ مِنَ ٱلدُّنْيَا ۖ وَأَحْسِن كَمَآ أَحْسَنَ ٱللَّهُ إِلَيْكَ ۖ وَلَا تَبْغِ ٱلْفَسَادَ فِى ٱلْأَرْضِ ۖ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُحِبُّ ٱلْمُفْسِدِينَ
wa-ib'taghi fīmā ātāka l-lahu l-dāra l-ākhirata walā tansa naṣībaka mina l-dun'yā wa-aḥsin kamā aḥsana l-lahu ilayka walā tabghi l-fasāda fī l-arḍi inna l-laha lā yuḥibbu l-muf'sidīna
"Kuma ka biɗã a cikin abin da Allah Ya bã ka, gidan Lãhira, kuma kada ka manta da rabonka daga dũniya. Kuma ka kyautata, kamar yadda Allah Ya kyautata zuwa gare ka, kuma kada ka nẽmi ɓarna a cikin ƙasa,1 lalle ne Allah bã Ya son mãsu barna."
قَالَ إِنَّمَآ أُوتِيتُهُۥ عَلَىٰ عِلْمٍ عِندِىٓ ۚ أَوَلَمْ يَعْلَمْ أَنَّ ٱللَّهَ قَدْ أَهْلَكَ مِن قَبْلِهِۦ مِنَ ٱلْقُرُونِ مَنْ هُوَ أَشَدُّ مِنْهُ قُوَّةًۭ وَأَكْثَرُ جَمْعًۭا ۚ وَلَا يُسْـَٔلُ عَن ذُنُوبِهِمُ ٱلْمُجْرِمُونَ
qāla innamā ūtītuhu ʿalā ʿil'min ʿindī awalam yaʿlam anna l-laha qad ahlaka min qablihi mina l-qurūni man huwa ashaddu min'hu quwwatan wa-aktharu jamʿan walā yus'alu ʿan dhunūbihimu l-muj'rimūna
Ya ce: "An bã ni shi a kan wani ilmi wanda yake gare ni ne kawai." Shin, kuma bai sani ba cẽwa lalle Allah haƙiƙa Ya halakar a gabaninsa, daga ƙarnõni, wanda yake Shi ne mafi tsananin ƙarfi daga gare shi, kuma mafi yawan tãrawar dũkiya, kuma bã zã a tambayi mãsu laifi daga zunubansu ba?1
فَخَرَجَ عَلَىٰ قَوْمِهِۦ فِى زِينَتِهِۦ ۖ قَالَ ٱلَّذِينَ يُرِيدُونَ ٱلْحَيَوٰةَ ٱلدُّنْيَا يَـٰلَيْتَ لَنَا مِثْلَ مَآ أُوتِىَ قَـٰرُونُ إِنَّهُۥ لَذُو حَظٍّ عَظِيمٍۢ
fakharaja ʿalā qawmihi fī zīnatihi qāla alladhīna yurīdūna l-ḥayata l-dun'yā yālayta lanā mith'la mā ūtiya qārūnu innahu ladhū ḥaẓẓin ʿaẓīmin
Sai (¡ãrũna) ya fita a kan mutãnensa a cikin adonsa. Waɗanda suke nufin rãyuwar dũniya suka ce: "Inã dai munã da kwatancin abin da aka bai wa ¡ãrũna! Lalle shĩ haƙĩƙa ma'abũcin rabo babba ne."
وَقَالَ ٱلَّذِينَ أُوتُوا۟ ٱلْعِلْمَ وَيْلَكُمْ ثَوَابُ ٱللَّهِ خَيْرٌۭ لِّمَنْ ءَامَنَ وَعَمِلَ صَـٰلِحًۭا وَلَا يُلَقَّىٰهَآ إِلَّا ٱلصَّـٰبِرُونَ
waqāla alladhīna ūtū l-ʿil'ma waylakum thawābu l-lahi khayrun liman āmana waʿamila ṣāliḥan walā yulaqqāhā illā l-ṣābirūna
Kuma waɗanda aka bai wa ilmi suka ce: "Kaitonku! sakamakon Allah ne mafi alhẽri a wanda ya yi tunãni, kuma ya aikata aikin ƙwarai,1 kuma bãbu wanda ake haɗãwa da ita fãce mai haƙuri."
فَخَسَفْنَا بِهِۦ وَبِدَارِهِ ٱلْأَرْضَ فَمَا كَانَ لَهُۥ مِن فِئَةٍۢ يَنصُرُونَهُۥ مِن دُونِ ٱللَّهِ وَمَا كَانَ مِنَ ٱلْمُنتَصِرِينَ
fakhasafnā bihi wabidārihi l-arḍa famā kāna lahu min fi-atin yanṣurūnahu min dūni l-lahi wamā kāna mina l-muntaṣirīna
Sai Muka shãfe ƙasa1 da shi da kuma gidansa. To, waɗansu jama'a ba su kasance gare shi ba, waɗanda suke taimakon sa, baicin Allah, kuma shi bai kasance daga mãsu taimakon kansu ba.
وَأَصْبَحَ ٱلَّذِينَ تَمَنَّوْا۟ مَكَانَهُۥ بِٱلْأَمْسِ يَقُولُونَ وَيْكَأَنَّ ٱللَّهَ يَبْسُطُ ٱلرِّزْقَ لِمَن يَشَآءُ مِنْ عِبَادِهِۦ وَيَقْدِرُ ۖ لَوْلَآ أَن مَّنَّ ٱللَّهُ عَلَيْنَا لَخَسَفَ بِنَا ۖ وَيْكَأَنَّهُۥ لَا يُفْلِحُ ٱلْكَـٰفِرُونَ
wa-aṣbaḥa alladhīna tamannaw makānahu bil-amsi yaqūlūna wayka-anna l-laha yabsuṭu l-riz'qa liman yashāu min ʿibādihi wayaqdiru lawlā an manna l-lahu ʿalaynā lakhasafa binā wayka-annahu lā yuf'liḥu l-kāfirūna
Kuma waɗanda suka yi bũrin matsayinsa a jiya suka wãyi gari sunã cẽwa, "Wai! Allah Yanã shimfiɗa arziki, ga wanda Yake so daga bãyinsa, kuma Yanã ƙuntatãwa. Bã dõmin Allah Ya yi mana falala ba dã Yã shãfe ƙasa da mu. Wai! lalle ne shi, kãfirai bã su cin nasara."
تِلْكَ ٱلدَّارُ ٱلْـَٔاخِرَةُ نَجْعَلُهَا لِلَّذِينَ لَا يُرِيدُونَ عُلُوًّۭا فِى ٱلْأَرْضِ وَلَا فَسَادًۭا ۚ وَٱلْعَـٰقِبَةُ لِلْمُتَّقِينَ
til'ka l-dāru l-ākhiratu najʿaluhā lilladhīna lā yurīdūna ʿuluwwan fī l-arḍi walā fasādan wal-ʿāqibatu lil'muttaqīna
Wancan gidan Lãhira Munã sanya shi ga waɗanda suke bã su nufin ɗaukaka a cikin rãyuwar dũniya kuma bã su son ɓarna. Kuma ãkiba ga mãsu taƙawa take.
مَن جَآءَ بِٱلْحَسَنَةِ فَلَهُۥ خَيْرٌۭ مِّنْهَا ۖ وَمَن جَآءَ بِٱلسَّيِّئَةِ فَلَا يُجْزَى ٱلَّذِينَ عَمِلُوا۟ ٱلسَّيِّـَٔاتِ إِلَّا مَا كَانُوا۟ يَعْمَلُونَ
man jāa bil-ḥasanati falahu khayrun min'hā waman jāa bil-sayi-ati falā yuj'zā alladhīna ʿamilū l-sayiāti illā mā kānū yaʿmalūna
Wanda ya zo da abu mai kyau, to, yana da mafi alhẽri daga gare shi, kuma wanda ya zo da mũgun abu, to, bã zã a sãkawa waɗanda suka aikata miyãgun ayyuka ba, fãce da abin da suka kasance sunã aikatãwa.
إِنَّ ٱلَّذِى فَرَضَ عَلَيْكَ ٱلْقُرْءَانَ لَرَآدُّكَ إِلَىٰ مَعَادٍۢ ۚ قُل رَّبِّىٓ أَعْلَمُ مَن جَآءَ بِٱلْهُدَىٰ وَمَنْ هُوَ فِى ضَلَـٰلٍۢ مُّبِينٍۢ
inna alladhī faraḍa ʿalayka l-qur'āna larādduka ilā maʿādin qul rabbī aʿlamu man jāa bil-hudā waman huwa fī ḍalālin mubīnin
Lalle ne wanda Ya faralta Alƙur'ãni a kanka, haƙĩƙa, Mai Mayar da kai ne zuwa ga makõma. ka ce: "Ubangijĩna ne Mafi sani ga wanda ya zo da shiriya, da kuma wanda yake a cikin ɓata bayyananne"
وَمَا كُنتَ تَرْجُوٓا۟ أَن يُلْقَىٰٓ إِلَيْكَ ٱلْكِتَـٰبُ إِلَّا رَحْمَةًۭ مِّن رَّبِّكَ ۖ فَلَا تَكُونَنَّ ظَهِيرًۭا لِّلْكَـٰفِرِينَ
wamā kunta tarjū an yul'qā ilayka l-kitābu illā raḥmatan min rabbika falā takūnanna ẓahīran lil'kāfirīna
Kuma ba ka kasance kanã fãtan a jẽfa Littafin nan zuwa gare ka ba, fãce dai dõmin rahama daga Ubangijinka. Sabõda haka kada ka zama mai taimako1 ga kãfirai.
وَلَا يَصُدُّنَّكَ عَنْ ءَايَـٰتِ ٱللَّهِ بَعْدَ إِذْ أُنزِلَتْ إِلَيْكَ ۖ وَٱدْعُ إِلَىٰ رَبِّكَ ۖ وَلَا تَكُونَنَّ مِنَ ٱلْمُشْرِكِينَ
walā yaṣuddunnaka ʿan āyāti l-lahi baʿda idh unzilat ilayka wa-ud'ʿu ilā rabbika walā takūnanna mina l-mush'rikīna
Kuma kada lalle su karkatar da kai daga barin ãyõyin Allah, a bãyãn har an saukar da su uwa gare ka. Ka yi kira zuwa ga Ubangijinka, kuma kada lalle ka kasance daga mãsu shirka.
وَلَا تَدْعُ مَعَ ٱللَّهِ إِلَـٰهًا ءَاخَرَ ۘ لَآ إِلَـٰهَ إِلَّا هُوَ ۚ كُلُّ شَىْءٍ هَالِكٌ إِلَّا وَجْهَهُۥ ۚ لَهُ ٱلْحُكْمُ وَإِلَيْهِ تُرْجَعُونَ
walā tadʿu maʿa l-lahi ilāhan ākhara lā ilāha illā huwa kullu shayin hālikun illā wajhahu lahu l-ḥuk'mu wa-ilayhi tur'jaʿūna
Kada ka kira wani abin bautãwa na dabam tãre da Allah. Bãbu abin bautãwa fãce Shi. Kõwane abu mai halaka ne fãce fuskar Sa. Shi ne da hukunci kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku.1