الحج
Al-Hajj
The Pilgrimage
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ ٱتَّقُوا۟ رَبَّكُمْ ۚ إِنَّ زَلْزَلَةَ ٱلسَّاعَةِ شَىْءٌ عَظِيمٌۭ
yāayyuhā l-nāsu ittaqū rabbakum inna zalzalata l-sāʿati shayon ʿaẓīmun
Yã ku mutãne! Ku bi Ubangijinku da taƙawa. Lalle ne girgizar1 ƙasa ta tsayuwar Sa'a wata aba ce mai girma.
يَوْمَ تَرَوْنَهَا تَذْهَلُ كُلُّ مُرْضِعَةٍ عَمَّآ أَرْضَعَتْ وَتَضَعُ كُلُّ ذَاتِ حَمْلٍ حَمْلَهَا وَتَرَى ٱلنَّاسَ سُكَـٰرَىٰ وَمَا هُم بِسُكَـٰرَىٰ وَلَـٰكِنَّ عَذَابَ ٱللَّهِ شَدِيدٌۭ
yawma tarawnahā tadhhalu kullu mur'ḍiʿatin ʿammā arḍaʿat wataḍaʿu kullu dhāti ḥamlin ḥamlahā watarā l-nāsa sukārā wamā hum bisukārā walākinna ʿadhāba l-lahi shadīdun
A rãnar da kuke ganin ta dukan mai shãyar da mãma tanã shagala daga abin da ta shãyar, kuma dukan mai ciki tanã haihuwar cikinta, kuma kanã ganin mutãne sunã mãsu mãyẽ alhãli kuwa su bã mãsu mãye ba, amma azãbar Allah ce mai tsanani.
وَمِنَ ٱلنَّاسِ مَن يُجَـٰدِلُ فِى ٱللَّهِ بِغَيْرِ عِلْمٍۢ وَيَتَّبِعُ كُلَّ شَيْطَـٰنٍۢ مَّرِيدٍۢ
wamina l-nāsi man yujādilu fī l-lahi bighayri ʿil'min wayattabiʿu kulla shayṭānin marīdin
Akwai daga mutãne1 wanda yake yin musũ ga sha'anin Allah bã da wani ilmi ba, kuma yanã biyar kõwane Shaiɗan mai taurin kai.
كُتِبَ عَلَيْهِ أَنَّهُۥ مَن تَوَلَّاهُ فَأَنَّهُۥ يُضِلُّهُۥ وَيَهْدِيهِ إِلَىٰ عَذَابِ ٱلسَّعِيرِ
kutiba ʿalayhi annahu man tawallāhu fa-annahu yuḍilluhu wayahdīhi ilā ʿadhābi l-saʿīri
An wajabta masa cẽwa wanda ya jiɓince shi, to, lalle ne sai ya ɓatar da shi, kuma ya shiryar da shi zuwa ga azãbar sa'ĩr.
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ إِن كُنتُمْ فِى رَيْبٍۢ مِّنَ ٱلْبَعْثِ فَإِنَّا خَلَقْنَـٰكُم مِّن تُرَابٍۢ ثُمَّ مِن نُّطْفَةٍۢ ثُمَّ مِنْ عَلَقَةٍۢ ثُمَّ مِن مُّضْغَةٍۢ مُّخَلَّقَةٍۢ وَغَيْرِ مُخَلَّقَةٍۢ لِّنُبَيِّنَ لَكُمْ ۚ وَنُقِرُّ فِى ٱلْأَرْحَامِ مَا نَشَآءُ إِلَىٰٓ أَجَلٍۢ مُّسَمًّۭى ثُمَّ نُخْرِجُكُمْ طِفْلًۭا ثُمَّ لِتَبْلُغُوٓا۟ أَشُدَّكُمْ ۖ وَمِنكُم مَّن يُتَوَفَّىٰ وَمِنكُم مَّن يُرَدُّ إِلَىٰٓ أَرْذَلِ ٱلْعُمُرِ لِكَيْلَا يَعْلَمَ مِنۢ بَعْدِ عِلْمٍۢ شَيْـًۭٔا ۚ وَتَرَى ٱلْأَرْضَ هَامِدَةًۭ فَإِذَآ أَنزَلْنَا عَلَيْهَا ٱلْمَآءَ ٱهْتَزَّتْ وَرَبَتْ وَأَنۢبَتَتْ مِن كُلِّ زَوْجٍۭ بَهِيجٍۢ
yāayyuhā l-nāsu in kuntum fī raybin mina l-baʿthi fa-innā khalaqnākum min turābin thumma min nuṭ'fatin thumma min ʿalaqatin thumma min muḍ'ghatin mukhallaqatin waghayri mukhallaqatin linubayyina lakum wanuqirru fī l-arḥāmi mā nashāu ilā ajalin musamman thumma nukh'rijukum ṭif'lan thumma litablughū ashuddakum waminkum man yutawaffā waminkum man yuraddu ilā ardhali l-ʿumuri likaylā yaʿlama min baʿdi ʿil'min shayan watarā l-arḍa hāmidatan fa-idhā anzalnā ʿalayhā l-māa ih'tazzat warabat wa-anbatat min kulli zawjin bahījin
Ya ku mutãne! Idan kun kasance a cikin shakka a Tãshin ¡iyãma, to, lalle ne Mũ, Man halittaku daga turɓaya, sa'an nan kuma daga gudãjin jini, sa'an nan kuma daga taõka wadda ake halittãwa da wadda ba a halittawa dõmin, Mu bayyana muku. Kuma Munã tab batar da abin da Muke so a cikin mahaifa zuwa ga wani ajali ambatacce, sa'an nan kuma Munã fitar da ku kunã jãrĩri, sa'an nan kuma dõmin ku kai ga cikar ƙarfinku. Kuma daga cikin ku akwai wanda ke mutuwa, kuma daga gare ku akwai wanda ake mayarwa zuwa ga mafi ƙasƙancin rãyuwa dõmin kada ya san kõme a bãyan ya sani. Kuma kanã ganin ƙasa shiru, sa'an nan idan Muka saukar da ruwa a kanta, sai ta girgiza kuma ta kumbura, kuma ta tsirar da tsirrai daga kõwane nau'i mai ban sha'awa.
ذَٰلِكَ بِأَنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلْحَقُّ وَأَنَّهُۥ يُحْىِ ٱلْمَوْتَىٰ وَأَنَّهُۥ عَلَىٰ كُلِّ شَىْءٍۢ قَدِيرٌۭ
dhālika bi-anna l-laha huwa l-ḥaqu wa-annahu yuḥ'yī l-mawtā wa-annahu ʿalā kulli shayin qadīrun
Wancan ne dõmin lalle Allah Shi ne Gaskiya, kuma lalle ne shi Yake rãyar da matattu, kuma lalle Shi Mai ikon yi ne a kan kõme.
وَأَنَّ ٱلسَّاعَةَ ءَاتِيَةٌۭ لَّا رَيْبَ فِيهَا وَأَنَّ ٱللَّهَ يَبْعَثُ مَن فِى ٱلْقُبُورِ
wa-anna l-sāʿata ātiyatun lā rayba fīhā wa-anna l-laha yabʿathu man fī l-qubūri
Kuma lalle ne Sa'ar Tãshin alkiiyãma mai zuwa ce, bãbu shakka a cikinta kuma lalle ne Allah Yanã tãyar da waɗanda suke a cikin ƙaburbura.
وَمِنَ ٱلنَّاسِ مَن يُجَـٰدِلُ فِى ٱللَّهِ بِغَيْرِ عِلْمٍۢ وَلَا هُدًۭى وَلَا كِتَـٰبٍۢ مُّنِيرٍۢ
wamina l-nāsi man yujādilu fī l-lahi bighayri ʿil'min walā hudan walā kitābin munīrin
Kuma daga mutãne akwai mai yin musu1 ga Allah bã da wani ilmi ba kuma bã da wata shiriya ba, kuma bã da wani littãfi mai haskakãwa ba.
ثَانِىَ عِطْفِهِۦ لِيُضِلَّ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ ۖ لَهُۥ فِى ٱلدُّنْيَا خِزْىٌۭ ۖ وَنُذِيقُهُۥ يَوْمَ ٱلْقِيَـٰمَةِ عَذَابَ ٱلْحَرِيقِ
thāniya ʿiṭ'fihi liyuḍilla ʿan sabīli l-lahi lahu fī l-dun'yā khiz'yun wanudhīquhu yawma l-qiyāmati ʿadhāba l-ḥarīqi
Yanã mai karkatar da sãshensa dõmin ya ɓatar (da wasu) daga tafarkin Allah! Yanã da wani wulãkanci a dũniya, kuma Munã ɗanɗana masa azãbar gõbara a Rãnar ¡iyãma.
ذَٰلِكَ بِمَا قَدَّمَتْ يَدَاكَ وَأَنَّ ٱللَّهَ لَيْسَ بِظَلَّـٰمٍۢ لِّلْعَبِيدِ
dhālika bimā qaddamat yadāka wa-anna l-laha laysa biẓallāmin lil'ʿabīdi
(A ce masa): "Wancan azaba sabõda abin da hannayenka biyu suka gabatar ne, kuma lalle ne Allah bai zama Mai zãlunci ga bãyinSa ba."
وَمِنَ ٱلنَّاسِ مَن يَعْبُدُ ٱللَّهَ عَلَىٰ حَرْفٍۢ ۖ فَإِنْ أَصَابَهُۥ خَيْرٌ ٱطْمَأَنَّ بِهِۦ ۖ وَإِنْ أَصَابَتْهُ فِتْنَةٌ ٱنقَلَبَ عَلَىٰ وَجْهِهِۦ خَسِرَ ٱلدُّنْيَا وَٱلْـَٔاخِرَةَ ۚ ذَٰلِكَ هُوَ ٱلْخُسْرَانُ ٱلْمُبِينُ
wamina l-nāsi man yaʿbudu l-laha ʿalā ḥarfin fa-in aṣābahu khayrun iṭ'ma-anna bihi wa-in aṣābathu fit'natun inqalaba ʿalā wajhihi khasira l-dun'yā wal-ākhirata dhālika huwa l-khus'rānu l-mubīnu
Kuma daga mutãne akwai mai bauta1 wa Allah a kan wani gefe. Sa'an nan idan wani alhẽri ya sãme shi, sai ya natsu da shi, kuma idan wata fitina ta sãme shi, sai ya jũya bãya a kan fuskarsa. Yã yi hasãrar dũniya da Lãhira. Waccan ita ce hasãra bayyananna.
يَدْعُوا۟ مِن دُونِ ٱللَّهِ مَا لَا يَضُرُّهُۥ وَمَا لَا يَنفَعُهُۥ ۚ ذَٰلِكَ هُوَ ٱلضَّلَـٰلُ ٱلْبَعِيدُ
yadʿū min dūni l-lahi mā lā yaḍurruhu wamā lā yanfaʿuhu dhālika huwa l-ḍalālu l-baʿīdu
Yanã kiran baicin Allah, abin da bã ya cũtarsa da abin da bã ya amfãninsa! waccan ita ce ɓata mai nĩsa.
يَدْعُوا۟ لَمَن ضَرُّهُۥٓ أَقْرَبُ مِن نَّفْعِهِۦ ۚ لَبِئْسَ ٱلْمَوْلَىٰ وَلَبِئْسَ ٱلْعَشِيرُ
yadʿū laman ḍarruhu aqrabu min nafʿihi labi'sa l-mawlā walabi'sa l-ʿashīru
Yanã kiran wanda yake lalle cũtarwarsa ce mafi kusa daga amfãninsa! Lalle ne, tir da shi ya zama majiɓinci, kuma tir da ya zama abõkin zama!
إِنَّ ٱللَّهَ يُدْخِلُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَعَمِلُوا۟ ٱلصَّـٰلِحَـٰتِ جَنَّـٰتٍۢ تَجْرِى مِن تَحْتِهَا ٱلْأَنْهَـٰرُ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ يَفْعَلُ مَا يُرِيدُ
inna l-laha yud'khilu alladhīna āmanū waʿamilū l-ṣāliḥāti jannātin tajrī min taḥtihā l-anhāru inna l-laha yafʿalu mā yurīdu
Lalle ne Allah Yanã shigar da waɗanda suka yi ĩmãni1 kuma suka aikata ayyukan ƙwarai a cikin gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashinsu. Lalle ne Allah Yanã aikata abin da Yake nufi.
مَن كَانَ يَظُنُّ أَن لَّن يَنصُرَهُ ٱللَّهُ فِى ٱلدُّنْيَا وَٱلْـَٔاخِرَةِ فَلْيَمْدُدْ بِسَبَبٍ إِلَى ٱلسَّمَآءِ ثُمَّ لْيَقْطَعْ فَلْيَنظُرْ هَلْ يُذْهِبَنَّ كَيْدُهُۥ مَا يَغِيظُ
man kāna yaẓunnu an lan yanṣurahu l-lahu fī l-dun'yā wal-ākhirati falyamdud bisababin ilā l-samāi thumma l'yaqṭaʿ falyanẓur hal yudh'hibanna kayduhu mā yaghīẓu
Wanda ya kasance yanã zaton cẽwa Allah bã zai taimake shi ba a cikin dũniya da Lãhira to sai ya mĩƙa wata igiya zuwa sama, sa'an nan kuma ya yanke ta, sa'an nan ya dũba. Shin, ko lalle kaidinsa zai gusar da abin da yake ji na takaici? 1
وَكَذَٰلِكَ أَنزَلْنَـٰهُ ءَايَـٰتٍۭ بَيِّنَـٰتٍۢ وَأَنَّ ٱللَّهَ يَهْدِى مَن يُرِيدُ
wakadhālika anzalnāhu āyātin bayyinātin wa-anna l-laha yahdī man yurīdu
Kuma kamar haka Muka saukar da shi (Alƙur'ãni) yanã ãyõyi bayyanannu. Kuma lalle ne Allah Yanã shiryar da wanda Yake nufi.
إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَٱلَّذِينَ هَادُوا۟ وَٱلصَّـٰبِـِٔينَ وَٱلنَّصَـٰرَىٰ وَٱلْمَجُوسَ وَٱلَّذِينَ أَشْرَكُوٓا۟ إِنَّ ٱللَّهَ يَفْصِلُ بَيْنَهُمْ يَوْمَ ٱلْقِيَـٰمَةِ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ كُلِّ شَىْءٍۢ شَهِيدٌ
inna alladhīna āmanū wa-alladhīna hādū wal-ṣābiīna wal-naṣārā wal-majūsa wa-alladhīna ashrakū inna l-laha yafṣilu baynahum yawma l-qiyāmati inna l-laha ʿalā kulli shayin shahīdun
Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni da waɗanda suka tũba (Yahũdu) da waɗanda suka karkace (Saba'ãwa) da Nasãra da Majũsãwa da waɗanda suka yi shirka, lalle ne Allah Yanã yin hukunci a tsakãninsu a Ranãr ¡iyãma. Lalle ne Allah Mahalarci ne a kan dukkan kõme. 1
أَلَمْ تَرَ أَنَّ ٱللَّهَ يَسْجُدُ لَهُۥ مَن فِى ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَمَن فِى ٱلْأَرْضِ وَٱلشَّمْسُ وَٱلْقَمَرُ وَٱلنُّجُومُ وَٱلْجِبَالُ وَٱلشَّجَرُ وَٱلدَّوَآبُّ وَكَثِيرٌۭ مِّنَ ٱلنَّاسِ ۖ وَكَثِيرٌ حَقَّ عَلَيْهِ ٱلْعَذَابُ ۗ وَمَن يُهِنِ ٱللَّهُ فَمَا لَهُۥ مِن مُّكْرِمٍ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ يَفْعَلُ مَا يَشَآءُ ۩
alam tara anna l-laha yasjudu lahu man fī l-samāwāti waman fī l-arḍi wal-shamsu wal-qamaru wal-nujūmu wal-jibālu wal-shajaru wal-dawābu wakathīrun mina l-nāsi wakathīrun ḥaqqa ʿalayhi l-ʿadhābu waman yuhini l-lahu famā lahu min muk'rimin inna l-laha yafʿalu mā yashāu
Ashe, ba ka gani ba, lalle Allah, wanda yake a cikin sammai da wanda yake a cikin ƙasa yanã yin sujada a gare shi, da kuma rãna da watã da taurãri da duwãtsu da itãce da dabbõbi, da kuma mãsu yawa daga mutãne? Kuma waɗansu mãsu yawa azãba tã tabbata a kansu. Kuma wanda Allah Ya wulãkantar, to, bã ya da wani mai girmamãwa. Kuma Lalle ne Allah Yanã aikata abin da Yake so.
۞ هَـٰذَانِ خَصْمَانِ ٱخْتَصَمُوا۟ فِى رَبِّهِمْ ۖ فَٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ قُطِّعَتْ لَهُمْ ثِيَابٌۭ مِّن نَّارٍۢ يُصَبُّ مِن فَوْقِ رُءُوسِهِمُ ٱلْحَمِيمُ
hādhāni khaṣmāni ikh'taṣamū fī rabbihim fa-alladhīna kafarū quṭṭiʿat lahum thiyābun min nārin yuṣabbu min fawqi ruūsihimu l-ḥamīmu
waɗannan ƙungiyõyi biyu1 ne mãsu husũma, sun yi husũma ga sha'anin Ubangijinsu. To, waɗanda suka kãfirta an yanka musu waɗansu tufafi daga wata irin wuta, anã zuba tafasasshen ruwa daga bisa kãwunansu.
يُصْهَرُ بِهِۦ مَا فِى بُطُونِهِمْ وَٱلْجُلُودُ
yuṣ'haru bihi mā fī buṭūnihim wal-julūdu
Da shĩ ake narkar da abin da yake a cikin cikunansu da fãtun jikinsu.
وَلَهُم مَّقَـٰمِعُ مِنْ حَدِيدٍۢ
walahum maqāmiʿu min ḥadīdin
Kuma sunã da waɗansu gwalmõmin dũka na baƙin ƙarfe.
كُلَّمَآ أَرَادُوٓا۟ أَن يَخْرُجُوا۟ مِنْهَا مِنْ غَمٍّ أُعِيدُوا۟ فِيهَا وَذُوقُوا۟ عَذَابَ ٱلْحَرِيقِ
kullamā arādū an yakhrujū min'hā min ghammin uʿīdū fīhā wadhūqū ʿadhāba l-ḥarīqi
A kõyaushe suka yi nufin fita daga gare ta, daga baƙin ciki, sai a mayar da su a cikinta, (a ce musu) "Ku ɗanɗani azãbar gõbara."
إِنَّ ٱللَّهَ يُدْخِلُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَعَمِلُوا۟ ٱلصَّـٰلِحَـٰتِ جَنَّـٰتٍۢ تَجْرِى مِن تَحْتِهَا ٱلْأَنْهَـٰرُ يُحَلَّوْنَ فِيهَا مِنْ أَسَاوِرَ مِن ذَهَبٍۢ وَلُؤْلُؤًۭا ۖ وَلِبَاسُهُمْ فِيهَا حَرِيرٌۭ
inna l-laha yud'khilu alladhīna āmanū waʿamilū l-ṣāliḥāti jannātin tajrī min taḥtihā l-anhāru yuḥallawna fīhā min asāwira min dhahabin walu'lu-an walibāsuhum fīhā ḥarīrun
Lalle ne, Allah Yana shigar da waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai a cikin gidãjen Aljanna, ƙoramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, anã ƙawãta su, a cikinsu, da waɗansu mundãye na zĩnãri da lu'u-lu'u. Kuma tufãfinsu a cikinsu alharĩni ne.1
وَهُدُوٓا۟ إِلَى ٱلطَّيِّبِ مِنَ ٱلْقَوْلِ وَهُدُوٓا۟ إِلَىٰ صِرَٰطِ ٱلْحَمِيدِ
wahudū ilā l-ṭayibi mina l-qawli wahudū ilā ṣirāṭi l-ḥamīdi
Kuma an shiryar da su zuwa ga mai kyau na zance kuma an shiryar da su zuwa ga, hanyar wanda ake gode wa.
إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ وَيَصُدُّونَ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ وَٱلْمَسْجِدِ ٱلْحَرَامِ ٱلَّذِى جَعَلْنَـٰهُ لِلنَّاسِ سَوَآءً ٱلْعَـٰكِفُ فِيهِ وَٱلْبَادِ ۚ وَمَن يُرِدْ فِيهِ بِإِلْحَادٍۭ بِظُلْمٍۢ نُّذِقْهُ مِنْ عَذَابٍ أَلِيمٍۢ
inna alladhīna kafarū wayaṣuddūna ʿan sabīli l-lahi wal-masjidi l-ḥarāmi alladhī jaʿalnāhu lilnnāsi sawāan l-ʿākifu fīhi wal-bādi waman yurid fīhi bi-il'ḥādin biẓul'min nudhiq'hu min ʿadhābin alīmin
Lalle ne waɗanda suka kãfirta kuma suka taushe (mutãne) daga hanyar Allah da masallaci mai alfarma wanda Muka sanya shi ga mutãne alhãli kuwa mazauni a ciki da baƙauye daidai suke kuma wanda ya yi nufin karkatar1 da gaskiya a cikinsa da zãlunci zã Mu ɗanɗana masa daga wata azãba mai raɗadi.
وَإِذْ بَوَّأْنَا لِإِبْرَٰهِيمَ مَكَانَ ٱلْبَيْتِ أَن لَّا تُشْرِكْ بِى شَيْـًۭٔا وَطَهِّرْ بَيْتِىَ لِلطَّآئِفِينَ وَٱلْقَآئِمِينَ وَٱلرُّكَّعِ ٱلسُّجُودِ
wa-idh bawwanā li-ib'rāhīma makāna l-bayti an lā tush'rik bī shayan waṭahhir baytiya lilṭṭāifīna wal-qāimīna wal-rukaʿi l-sujūdi
Kuma a lõkacin da Muka iyãkance1 wa Ibrãhim wurin ¦akin (Muka ce masa), "Kada ka haɗa kõme da Ni ga bauta, kuma ka tsarkake daki Na dõmin mãsu ɗawãfi da mãsu tsayuwa da mãsu ruku'u da mãsu sujada.
وَأَذِّن فِى ٱلنَّاسِ بِٱلْحَجِّ يَأْتُوكَ رِجَالًۭا وَعَلَىٰ كُلِّ ضَامِرٍۢ يَأْتِينَ مِن كُلِّ فَجٍّ عَمِيقٍۢ
wa-adhin fī l-nāsi bil-ḥaji yatūka rijālan waʿalā kulli ḍāmirin yatīna min kulli fajjin ʿamīqin
"Kuma ka yi yẽkuwa ga mutãne da wajabcin Hajji su je maka suna mãsu tafiya da ƙafãfu da kuma a kan kõwane maɗankwarin rãƙumi mãsu zuwa daga kõwane rango mai zurfi."
لِّيَشْهَدُوا۟ مَنَـٰفِعَ لَهُمْ وَيَذْكُرُوا۟ ٱسْمَ ٱللَّهِ فِىٓ أَيَّامٍۢ مَّعْلُومَـٰتٍ عَلَىٰ مَا رَزَقَهُم مِّنۢ بَهِيمَةِ ٱلْأَنْعَـٰمِ ۖ فَكُلُوا۟ مِنْهَا وَأَطْعِمُوا۟ ٱلْبَآئِسَ ٱلْفَقِيرَ
liyashhadū manāfiʿa lahum wayadhkurū is'ma l-lahi fī ayyāmin maʿlūmātin ʿalā mā razaqahum min bahīmati l-anʿāmi fakulū min'hā wa-aṭʿimū l-bāisa l-faqīra
"Dõmin su halarci abũbuwan amfãni a gare su, kuma su ambãci sunan Allah a cikin 'yan kwãnuka sanannu sabõda abin da Ya azurta su da shĩ daga dabbõbin jin dãɗi. Sai ku ci daga gare su, kuma ku ciyar da matsattse matalauci."
ثُمَّ لْيَقْضُوا۟ تَفَثَهُمْ وَلْيُوفُوا۟ نُذُورَهُمْ وَلْيَطَّوَّفُوا۟ بِٱلْبَيْتِ ٱلْعَتِيقِ
thumma l'yaqḍū tafathahum walyūfū nudhūrahum walyaṭṭawwafū bil-bayti l-ʿatīqi
"Sa'an nan kuma sai su ƙãre ibãdarsu da gusar da ƙazanta, knma sai su cika alkawuransu kuma sai su yi ɗawãfi (sunã gẽwaya) ga ¦ãkin nin 'yantacce."
ذَٰلِكَ وَمَن يُعَظِّمْ حُرُمَـٰتِ ٱللَّهِ فَهُوَ خَيْرٌۭ لَّهُۥ عِندَ رَبِّهِۦ ۗ وَأُحِلَّتْ لَكُمُ ٱلْأَنْعَـٰمُ إِلَّا مَا يُتْلَىٰ عَلَيْكُمْ ۖ فَٱجْتَنِبُوا۟ ٱلرِّجْسَ مِنَ ٱلْأَوْثَـٰنِ وَٱجْتَنِبُوا۟ قَوْلَ ٱلزُّورِ
dhālika waman yuʿaẓẓim ḥurumāti l-lahi fahuwa khayrun lahu ʿinda rabbihi wa-uḥillat lakumu l-anʿāmu illā mā yut'lā ʿalaykum fa-ij'tanibū l-rij'sa mina l-awthāni wa-ij'tanibū qawla l-zūri
Wancan ne. Kuma wanda ya girmama hukunce-hukuncen Allah to shĩ ne mafĩfĩci a gare shi, a wurin Ubangijinsa. Kuma an halatta muku dabbõbin ni'ima1 fãce abin da ake karantãwa a kanku. Sabõda haka ku nĩsanci ƙazanta daga gumãka kuma ku nĩsanci ƙazanta daga shaidar zur.
حُنَفَآءَ لِلَّهِ غَيْرَ مُشْرِكِينَ بِهِۦ ۚ وَمَن يُشْرِكْ بِٱللَّهِ فَكَأَنَّمَا خَرَّ مِنَ ٱلسَّمَآءِ فَتَخْطَفُهُ ٱلطَّيْرُ أَوْ تَهْوِى بِهِ ٱلرِّيحُ فِى مَكَانٍۢ سَحِيقٍۢ
ḥunafāa lillahi ghayra mush'rikīna bihi waman yush'rik bil-lahi faka-annamā kharra mina l-samāi fatakhṭafuhu l-ṭayru aw tahwī bihi l-rīḥu fī makānin saḥīqin
Kuna mãsu tsayuwa ga gaskiya dõmin Allah, ba masu yin shirka da Shi ba. Kuma wanda ya yi shirka da Allah, to, yanã kamar abin da ya fãɗo daga sama, sa'an nan tsuntsãye su cafe shi, ko iska ta fãɗa da shi a cikin wani wuri mai nisa.
ذَٰلِكَ وَمَن يُعَظِّمْ شَعَـٰٓئِرَ ٱللَّهِ فَإِنَّهَا مِن تَقْوَى ٱلْقُلُوبِ
dhālika waman yuʿaẓẓim shaʿāira l-lahi fa-innahā min taqwā l-qulūbi
Wancan ne. Kuma wanda ya girmama ibãdõdin Allah, to, lalle ne ita (girmamãwar) tanã daga ayyukan zukãta na ibãda.
لَكُمْ فِيهَا مَنَـٰفِعُ إِلَىٰٓ أَجَلٍۢ مُّسَمًّۭى ثُمَّ مَحِلُّهَآ إِلَى ٱلْبَيْتِ ٱلْعَتِيقِ
lakum fīhā manāfiʿu ilā ajalin musamman thumma maḥilluhā ilā l-bayti l-ʿatīqi
Kuna da waɗansu abũbuwan amfãni1 a cikinta (dabbar hadaya) har ya zuwa ga wani ajali ambatacce, sa'an nan kuma wurin halattãta zuwa ga ¦ãkin 'yantacce ne.
وَلِكُلِّ أُمَّةٍۢ جَعَلْنَا مَنسَكًۭا لِّيَذْكُرُوا۟ ٱسْمَ ٱللَّهِ عَلَىٰ مَا رَزَقَهُم مِّنۢ بَهِيمَةِ ٱلْأَنْعَـٰمِ ۗ فَإِلَـٰهُكُمْ إِلَـٰهٌۭ وَٰحِدٌۭ فَلَهُۥٓ أَسْلِمُوا۟ ۗ وَبَشِّرِ ٱلْمُخْبِتِينَ
walikulli ummatin jaʿalnā mansakan liyadhkurū is'ma l-lahi ʿalā mā razaqahum min bahīmati l-anʿāmi fa-ilāhukum ilāhun wāḥidun falahu aslimū wabashiri l-mukh'bitīna
Kuma ga kõwace al'umma Mun sanya ibãdar yanka, dõmin su ambaci sũnan Allah a kan abin da Ya azurta su da shi daga dabbõbin ni'ima. Sa'an nan kuma Abin bautawarku Abin bautawa ne Guda, sai ku sallama Masa. Kuma ka yi bushãra ga mãsu ƙanƙantar da kai.
ٱلَّذِينَ إِذَا ذُكِرَ ٱللَّهُ وَجِلَتْ قُلُوبُهُمْ وَٱلصَّـٰبِرِينَ عَلَىٰ مَآ أَصَابَهُمْ وَٱلْمُقِيمِى ٱلصَّلَوٰةِ وَمِمَّا رَزَقْنَـٰهُمْ يُنفِقُونَ
alladhīna idhā dhukira l-lahu wajilat qulūbuhum wal-ṣābirīna ʿalā mā aṣābahum wal-muqīmī l-ṣalati wamimmā razaqnāhum yunfiqūna
Waɗanda suke idan an ambaci Allah sai zukãtansu su firgita, da mãsu haƙuri a kan abin da ya sãme su, da mãsu tsayar da salla, kuma sunã ciyarwa daga abin da Muka azurta su.1
وَٱلْبُدْنَ جَعَلْنَـٰهَا لَكُم مِّن شَعَـٰٓئِرِ ٱللَّهِ لَكُمْ فِيهَا خَيْرٌۭ ۖ فَٱذْكُرُوا۟ ٱسْمَ ٱللَّهِ عَلَيْهَا صَوَآفَّ ۖ فَإِذَا وَجَبَتْ جُنُوبُهَا فَكُلُوا۟ مِنْهَا وَأَطْعِمُوا۟ ٱلْقَانِعَ وَٱلْمُعْتَرَّ ۚ كَذَٰلِكَ سَخَّرْنَـٰهَا لَكُمْ لَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ
wal-bud'na jaʿalnāhā lakum min shaʿāiri l-lahi lakum fīhā khayrun fa-udh'kurū is'ma l-lahi ʿalayhā ṣawāffa fa-idhā wajabat junūbuhā fakulū min'hā wa-aṭʿimū l-qāniʿa wal-muʿ'tara kadhālika sakharnāhā lakum laʿallakum tashkurūna
Kuma rãƙuman, Mun sanya su a gare ku, a ibãdõjin Allah. Kunã da wani alhẽri babba a cikinsu. Sai ku ambaci sũnan Allah a kansu sunã tsaye1 a kan ƙafãfu uku. Sa'an nan idan sãsanninsu suka fãɗi, to, ku ci daga gare su, kuma ku ciyar da mai wadar zũci da mai bara. Kamar haka Muka hõre muku su, tsammãninku kunã gõdẽwa.
لَن يَنَالَ ٱللَّهَ لُحُومُهَا وَلَا دِمَآؤُهَا وَلَـٰكِن يَنَالُهُ ٱلتَّقْوَىٰ مِنكُمْ ۚ كَذَٰلِكَ سَخَّرَهَا لَكُمْ لِتُكَبِّرُوا۟ ٱللَّهَ عَلَىٰ مَا هَدَىٰكُمْ ۗ وَبَشِّرِ ٱلْمُحْسِنِينَ
lan yanāla l-laha luḥūmuhā walā dimāuhā walākin yanāluhu l-taqwā minkum kadhālika sakharahā lakum litukabbirū l-laha ʿalā mā hadākum wabashiri l-muḥ'sinīna
Nãmõminsu bã za su sãmi Allah ba haka jinainansu amma taƙawa daga gare ku tanã, sãmun Sa. Kamar haka Ya hõre su sabõda ku dõmin ku girmama Allah sabõda shiriyar da Ya yi muku. Kuma ka yi bushãra ga mãsu kyautata yi.
۞ إِنَّ ٱللَّهَ يُدَٰفِعُ عَنِ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓا۟ ۗ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُحِبُّ كُلَّ خَوَّانٍۢ كَفُورٍ
inna l-laha yudāfiʿu ʿani alladhīna āmanū inna l-laha lā yuḥibbu kulla khawwānin kafūrin
Lalle ne, Allah Yanã yin faɗa1 sabõda waɗanda suka yi ĩmãni. Lalle ne Allah bã Ya son dukkan mayaudari, mai yawan kãfirci.
أُذِنَ لِلَّذِينَ يُقَـٰتَلُونَ بِأَنَّهُمْ ظُلِمُوا۟ ۚ وَإِنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ نَصْرِهِمْ لَقَدِيرٌ
udhina lilladhīna yuqātalūna bi-annahum ẓulimū wa-inna l-laha ʿalā naṣrihim laqadīrun
An yi izni ga waɗanda ake yãƙar su da cẽwa lalle an zãlunce su, kuma lalle ne Allah, haƙĩƙa, Mai ĩkon yi ne a kan taimakonsu.
ٱلَّذِينَ أُخْرِجُوا۟ مِن دِيَـٰرِهِم بِغَيْرِ حَقٍّ إِلَّآ أَن يَقُولُوا۟ رَبُّنَا ٱللَّهُ ۗ وَلَوْلَا دَفْعُ ٱللَّهِ ٱلنَّاسَ بَعْضَهُم بِبَعْضٍۢ لَّهُدِّمَتْ صَوَٰمِعُ وَبِيَعٌۭ وَصَلَوَٰتٌۭ وَمَسَـٰجِدُ يُذْكَرُ فِيهَا ٱسْمُ ٱللَّهِ كَثِيرًۭا ۗ وَلَيَنصُرَنَّ ٱللَّهُ مَن يَنصُرُهُۥٓ ۗ إِنَّ ٱللَّهَ لَقَوِىٌّ عَزِيزٌ
alladhīna ukh'rijū min diyārihim bighayri ḥaqqin illā an yaqūlū rabbunā l-lahu walawlā dafʿu l-lahi l-nāsa baʿḍahum bibaʿḍin lahuddimat ṣawāmiʿu wabiyaʿun waṣalawātun wamasājidu yudh'karu fīhā us'mu l-lahi kathīran walayanṣuranna l-lahu man yanṣuruhu inna l-laha laqawiyyun ʿazīzun
Waɗanda aka fitina daga gidajensu bã da wani hakki ba fãce sunã cẽwa, Ubangijinmu Allah ne."Kuma ba dõmin tunkuɗẽwar Allah ga mutãne ba, sãshensu da sãshe, haƙĩƙa, da an rũsa sauma'õ'in (Ruhbãnãwa) dã majãmi'õ'in Nasãra da gidãjen ibãdar Yahudu da masallatai waɗanda ake ambatar Allah a cikinsu da yawa. Kuma lalle, haƙĩƙa, Allah Yanã taimakon wanda yake taimakon Sa. Lalle Allah ne haƙĩƙa Mai ƙarfi Mabuwãyi.
ٱلَّذِينَ إِن مَّكَّنَّـٰهُمْ فِى ٱلْأَرْضِ أَقَامُوا۟ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتَوُا۟ ٱلزَّكَوٰةَ وَأَمَرُوا۟ بِٱلْمَعْرُوفِ وَنَهَوْا۟ عَنِ ٱلْمُنكَرِ ۗ وَلِلَّهِ عَـٰقِبَةُ ٱلْأُمُورِ
alladhīna in makkannāhum fī l-arḍi aqāmū l-ṣalata waātawū l-zakata wa-amarū bil-maʿrūfi wanahaw ʿani l-munkari walillahi ʿāqibatu l-umūri
Waɗanda suke idan Muka bã su ĩko a cikin ƙasa sai su tsai da salla, kuma su baybr da zakka kuma su yi umurni da abin da aka sani,1 kuma su hana daga abin da ba a sani ba. Kuma ãƙibar al'amura ga Allah take.
وَإِن يُكَذِّبُوكَ فَقَدْ كَذَّبَتْ قَبْلَهُمْ قَوْمُ نُوحٍۢ وَعَادٌۭ وَثَمُودُ
wa-in yukadhibūka faqad kadhabat qablahum qawmu nūḥin waʿādun wathamūdu
Kuma idan sun ƙaryata ka, to lalle haƙĩƙa, mutãnen Nũhu da Ãdãwa da Samũdawa, sun ƙaryata a gabaninsu.
وَقَوْمُ إِبْرَٰهِيمَ وَقَوْمُ لُوطٍۢ
waqawmu ib'rāhīma waqawmu lūṭin
Da mutãnen Ibrahim da mutãnen Lũɗu.
وَأَصْحَـٰبُ مَدْيَنَ ۖ وَكُذِّبَ مُوسَىٰ فَأَمْلَيْتُ لِلْكَـٰفِرِينَ ثُمَّ أَخَذْتُهُمْ ۖ فَكَيْفَ كَانَ نَكِيرِ
wa-aṣḥābu madyana wakudhiba mūsā fa-amlaytu lil'kāfirīna thumma akhadhtuhum fakayfa kāna nakīri
Da mãsu Madyana, kuma an ƙaryata Mũsã. Sai Na jinkirtawa kãfiran, sa'an nan kuma Na kãma su. To, yãya musũNa (gare su) ya kasance?
فَكَأَيِّن مِّن قَرْيَةٍ أَهْلَكْنَـٰهَا وَهِىَ ظَالِمَةٌۭ فَهِىَ خَاوِيَةٌ عَلَىٰ عُرُوشِهَا وَبِئْرٍۢ مُّعَطَّلَةٍۢ وَقَصْرٍۢ مَّشِيدٍ
faka-ayyin min qaryatin ahlaknāhā wahiya ẓālimatun fahiya khāwiyatun ʿalā ʿurūshihā wabi'rin muʿaṭṭalatin waqaṣrin mashīdin
Sa'an nan da yawa daga alƙarya, Muka halaka ta, alhãli kuwa tanã mai zalũnci sai ta zama fãɗaɗɗa a kan rassanta, da yawa daga rĩjiya wadda aka wõfintar, da kuma gidãjen sarauta maɗaukaka.
أَفَلَمْ يَسِيرُوا۟ فِى ٱلْأَرْضِ فَتَكُونَ لَهُمْ قُلُوبٌۭ يَعْقِلُونَ بِهَآ أَوْ ءَاذَانٌۭ يَسْمَعُونَ بِهَا ۖ فَإِنَّهَا لَا تَعْمَى ٱلْأَبْصَـٰرُ وَلَـٰكِن تَعْمَى ٱلْقُلُوبُ ٱلَّتِى فِى ٱلصُّدُورِ
afalam yasīrū fī l-arḍi fatakūna lahum qulūbun yaʿqilūna bihā aw ādhānun yasmaʿūna bihā fa-innahā lā taʿmā l-abṣāru walākin taʿmā l-qulūbu allatī fī l-ṣudūri
Shin, to, ba su yi tafiya ba a cikin ƙasa dõmin zukãta waɗanda zã su yi hankali da su da kunnuwa da za su yi saurãre da su su kasance a gare su? Dõmin lalle ne idãnun ba su makanta, amma zukãta waɗanda ke a cikin ƙirãza sũ ke makanta.
وَيَسْتَعْجِلُونَكَ بِٱلْعَذَابِ وَلَن يُخْلِفَ ٱللَّهُ وَعْدَهُۥ ۚ وَإِنَّ يَوْمًا عِندَ رَبِّكَ كَأَلْفِ سَنَةٍۢ مِّمَّا تَعُدُّونَ
wayastaʿjilūnaka bil-ʿadhābi walan yukh'lifa l-lahu waʿdahu wa-inna yawman ʿinda rabbika ka-alfi sanatin mimmā taʿuddūna
Kuma sunã nẽman ka yi gaggãwa da azãba, alhãli kuwa Allah bã zai sãɓa wa'adinSa ba kuma lalle ne, yini1 ɗaya a wurin Ubangijinka kamar shẽkara dubu yake daga abin da kuke ƙidãyãwa.
وَكَأَيِّن مِّن قَرْيَةٍ أَمْلَيْتُ لَهَا وَهِىَ ظَالِمَةٌۭ ثُمَّ أَخَذْتُهَا وَإِلَىَّ ٱلْمَصِيرُ
waka-ayyin min qaryatin amlaytu lahā wahiya ẓālimatun thumma akhadhtuhā wa-ilayya l-maṣīru
Kuma da yawa daga alƙarya, Na yi jinkirin azãba gare ta (da laifinta) sa'an nan Na kãma ta, kuma zuwa gare Ni makõma take.
قُلْ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ إِنَّمَآ أَنَا۠ لَكُمْ نَذِيرٌۭ مُّبِينٌۭ
qul yāayyuhā l-nāsu innamā anā lakum nadhīrun mubīnun
Ka ce: "Ya ku mutãne! Nĩ wani mai gargaɗi ne kawai zuwa gare ku, mai bayyanawa."
فَٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَعَمِلُوا۟ ٱلصَّـٰلِحَـٰتِ لَهُم مَّغْفِرَةٌۭ وَرِزْقٌۭ كَرِيمٌۭ
fa-alladhīna āmanū waʿamilū l-ṣāliḥāti lahum maghfiratun wariz'qun karīmun
To, waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, sunã da gãfara da arziki na karimci.
وَٱلَّذِينَ سَعَوْا۟ فِىٓ ءَايَـٰتِنَا مُعَـٰجِزِينَ أُو۟لَـٰٓئِكَ أَصْحَـٰبُ ٱلْجَحِيمِ
wa-alladhīna saʿaw fī āyātinā muʿājizīna ulāika aṣḥābu l-jaḥīmi
Kuma waɗanda suka yi aikin ɓãtãwa a cikin ayõyinMu, sunã mãsu gajiyarwa, waɗancan 'yan Jahĩm ne.
وَمَآ أَرْسَلْنَا مِن قَبْلِكَ مِن رَّسُولٍۢ وَلَا نَبِىٍّ إِلَّآ إِذَا تَمَنَّىٰٓ أَلْقَى ٱلشَّيْطَـٰنُ فِىٓ أُمْنِيَّتِهِۦ فَيَنسَخُ ٱللَّهُ مَا يُلْقِى ٱلشَّيْطَـٰنُ ثُمَّ يُحْكِمُ ٱللَّهُ ءَايَـٰتِهِۦ ۗ وَٱللَّهُ عَلِيمٌ حَكِيمٌۭ
wamā arsalnā min qablika min rasūlin walā nabiyyin illā idhā tamannā alqā l-shayṭānu fī um'niyyatihi fayansakhu l-lahu mā yul'qī l-shayṭānu thumma yuḥ'kimu l-lahu āyātihi wal-lahu ʿalīmun ḥakīmun
Kuma ba Mu aika wani manzo ba a gabãninka, kuma ba Mu umurci wani Annabi ba fãce idan ya yi bũri,1 sai Shaiɗan ya jẽfa (wani abu) a cikin bũrinsa, sa'an nan Allah Ya shãfe abin da Shaiɗan ke jefãwa. Sa'an nan kuma Allah Ya kyautata ãyõyin Sa. Kuma Allah Masani ne, Mai hikima.
لِّيَجْعَلَ مَا يُلْقِى ٱلشَّيْطَـٰنُ فِتْنَةًۭ لِّلَّذِينَ فِى قُلُوبِهِم مَّرَضٌۭ وَٱلْقَاسِيَةِ قُلُوبُهُمْ ۗ وَإِنَّ ٱلظَّـٰلِمِينَ لَفِى شِقَاقٍۭ بَعِيدٍۢ
liyajʿala mā yul'qī l-shayṭānu fit'natan lilladhīna fī qulūbihim maraḍun wal-qāsiyati qulūbuhum wa-inna l-ẓālimīna lafī shiqāqin baʿīdin
Dõmin Ya sanya abin da Shaiɗan ke jẽfãwa ya zama fitina ga waɗanda a cikin zukãtansu akwai cũta, da mãsu ƙẽƙasassun zukãtansu. Kuma lalle ne azzãlumai haƙĩƙa, sunã a cikin sãɓãnimai nĩsa.
وَلِيَعْلَمَ ٱلَّذِينَ أُوتُوا۟ ٱلْعِلْمَ أَنَّهُ ٱلْحَقُّ مِن رَّبِّكَ فَيُؤْمِنُوا۟ بِهِۦ فَتُخْبِتَ لَهُۥ قُلُوبُهُمْ ۗ وَإِنَّ ٱللَّهَ لَهَادِ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓا۟ إِلَىٰ صِرَٰطٍۢ مُّسْتَقِيمٍۢ
waliyaʿlama alladhīna ūtū l-ʿil'ma annahu l-ḥaqu min rabbika fayu'minū bihi fatukh'bita lahu qulūbuhum wa-inna l-laha lahādi alladhīna āmanū ilā ṣirāṭin mus'taqīmin
Kuma dõmin waɗanda aka bai wa ilmi su sani lalle shi ne gaskiya daga Ubangijinka dõmin su yi ĩmãni da shi sabõda zukãtansu su natsu gare shi. Kuma lalle ne Allah, haƙĩƙa, Mai shiryar da waɗanda suka yi ĩmãni ne zuwa ga hanya madaidaiciya.
وَلَا يَزَالُ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ فِى مِرْيَةٍۢ مِّنْهُ حَتَّىٰ تَأْتِيَهُمُ ٱلسَّاعَةُ بَغْتَةً أَوْ يَأْتِيَهُمْ عَذَابُ يَوْمٍ عَقِيمٍ
walā yazālu alladhīna kafarū fī mir'yatin min'hu ḥattā tatiyahumu l-sāʿatu baghtatan aw yatiyahum ʿadhābu yawmin ʿaqīmin
Kuma waɗanda suka kãfirta bã zã su gushe ba sunã a cikin shakka daga gare shi, har Sa'a ta jẽ musu bisa ga abke, kõ kuwa azãbar wani yini bakarãre ta jẽ musu.
ٱلْمُلْكُ يَوْمَئِذٍۢ لِّلَّهِ يَحْكُمُ بَيْنَهُمْ ۚ فَٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَعَمِلُوا۟ ٱلصَّـٰلِحَـٰتِ فِى جَنَّـٰتِ ٱلنَّعِيمِ
al-mul'ku yawma-idhin lillahi yaḥkumu baynahum fa-alladhīna āmanū waʿamilū l-ṣāliḥāti fī jannāti l-naʿīmi
Mulki a rãnar nan ga Allah yake, Yanã hukunci a tsakãninsu. To, waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã a cikin gidãjen Aljannar ni'ima.
وَٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ وَكَذَّبُوا۟ بِـَٔايَـٰتِنَا فَأُو۟لَـٰٓئِكَ لَهُمْ عَذَابٌۭ مُّهِينٌۭ
wa-alladhīna kafarū wakadhabū biāyātinā fa-ulāika lahum ʿadhābun muhīnun
Kuma waɗandra suka kãfirta kuma suka ƙaryata, game da ãyõyin Mu, to, waɗannan sunã da azãba mai wulãkantarwa.
وَٱلَّذِينَ هَاجَرُوا۟ فِى سَبِيلِ ٱللَّهِ ثُمَّ قُتِلُوٓا۟ أَوْ مَاتُوا۟ لَيَرْزُقَنَّهُمُ ٱللَّهُ رِزْقًا حَسَنًۭا ۚ وَإِنَّ ٱللَّهَ لَهُوَ خَيْرُ ٱلرَّٰزِقِينَ
wa-alladhīna hājarū fī sabīli l-lahi thumma qutilū aw mātū layarzuqannahumu l-lahu riz'qan ḥasanan wa-inna l-laha lahuwa khayru l-rāziqīna
Kuma waɗanda suka yi hijira a cikin tafarkin Allah sa'an nan kuma aka kashe su, kõ suka mutu, lalle ne Allah Yanã azurta su da arziki mai kyau. Kuma lalle ne Allah, haƙĩƙa, Shĩ ne Mafi alhẽrin mãsu azurtãwa.
لَيُدْخِلَنَّهُم مُّدْخَلًۭا يَرْضَوْنَهُۥ ۗ وَإِنَّ ٱللَّهَ لَعَلِيمٌ حَلِيمٌۭ
layud'khilannahum mud'khalan yarḍawnahu wa-inna l-laha laʿalīmun ḥalīmun
Lalle ne, Yanã shigar da su a wata mashiga wadda zã su yarda da ita. Kuma lalle ne Allah, haƙĩƙa Masani ne, Mai haƙuri.
۞ ذَٰلِكَ وَمَنْ عَاقَبَ بِمِثْلِ مَا عُوقِبَ بِهِۦ ثُمَّ بُغِىَ عَلَيْهِ لَيَنصُرَنَّهُ ٱللَّهُ ۗ إِنَّ ٱللَّهَ لَعَفُوٌّ غَفُورٌۭ
dhālika waman ʿāqaba bimith'li mā ʿūqiba bihi thumma bughiya ʿalayhi layanṣurannahu l-lahu inna l-laha laʿafuwwun ghafūrun
Wancan! Kuma wanda ya rãma azãba da misãlin abin da aka yi masa, sa'an nan kuma aka zãlunce shi, lalle ne Allah Yanã taimakon sa. Lalle ne Allah haƙĩƙa Mai yãfẽwa ne, Mai gãfara.
ذَٰلِكَ بِأَنَّ ٱللَّهَ يُولِجُ ٱلَّيْلَ فِى ٱلنَّهَارِ وَيُولِجُ ٱلنَّهَارَ فِى ٱلَّيْلِ وَأَنَّ ٱللَّهَ سَمِيعٌۢ بَصِيرٌۭ
dhālika bi-anna l-laha yūliju al-layla fī l-nahāri wayūliju l-nahāra fī al-layli wa-anna l-laha samīʿun baṣīrun
Wancan! sabõda Allah Yanã shigar da dare a cikin yini, kuma Yanã shigar da yini a cikin dare, kuma lalle, Allah Mai jĩ ne, Mai gani.
ذَٰلِكَ بِأَنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلْحَقُّ وَأَنَّ مَا يَدْعُونَ مِن دُونِهِۦ هُوَ ٱلْبَـٰطِلُ وَأَنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلْعَلِىُّ ٱلْكَبِيرُ
dhālika bi-anna l-laha huwa l-ḥaqu wa-anna mā yadʿūna min dūnihi huwa l-bāṭilu wa-anna l-laha huwa l-ʿaliyu l-kabīru
Wancan! sabõda lalle ne Allah, shĩ ne Gaskiya, kuma lalle ne, abin da suke kira waninSa shi ne ƙarya. Kuma lalle ne Allah, Shĩ ne Maɗaukaki, Mai girma.
أَلَمْ تَرَ أَنَّ ٱللَّهَ أَنزَلَ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءًۭ فَتُصْبِحُ ٱلْأَرْضُ مُخْضَرَّةً ۗ إِنَّ ٱللَّهَ لَطِيفٌ خَبِيرٌۭ
alam tara anna l-laha anzala mina l-samāi māan fatuṣ'biḥu l-arḍu mukh'ḍarratan inna l-laha laṭīfun khabīrun
Ashe, ba ka gani ba, lalle ne, Allah Yã saukar da ruwa1 daga sama, sai ƙasa ta wãyi gari kõriya? Lalle Allah Mai tausasawa ne, Mai ƙididdigewa.
لَّهُۥ مَا فِى ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَمَا فِى ٱلْأَرْضِ ۗ وَإِنَّ ٱللَّهَ لَهُوَ ٱلْغَنِىُّ ٱلْحَمِيدُ
lahu mā fī l-samāwāti wamā fī l-arḍi wa-inna l-laha lahuwa l-ghaniyu l-ḥamīdu
Abin da ke a cikin sammai, da abin da ke a cikin ƙasa, Nasa ne, kuma lalle ne Allah, haƙĩƙa, Shi ne wadatacce, Gõdadde.
أَلَمْ تَرَ أَنَّ ٱللَّهَ سَخَّرَ لَكُم مَّا فِى ٱلْأَرْضِ وَٱلْفُلْكَ تَجْرِى فِى ٱلْبَحْرِ بِأَمْرِهِۦ وَيُمْسِكُ ٱلسَّمَآءَ أَن تَقَعَ عَلَى ٱلْأَرْضِ إِلَّا بِإِذْنِهِۦٓ ۗ إِنَّ ٱللَّهَ بِٱلنَّاسِ لَرَءُوفٌۭ رَّحِيمٌۭ
alam tara anna l-laha sakhara lakum mā fī l-arḍi wal-ful'ka tajrī fī l-baḥri bi-amrihi wayum'siku l-samāa an taqaʿa ʿalā l-arḍi illā bi-idh'nihi inna l-laha bil-nāsi laraūfun raḥīmun
Shin ba ka gani ba, lalle ne Allah Ya hõre muku abin da yake a cikin ƙasa, kuma jirãge sunã gudãna a cikin tẽku, da umurninSa kuma Yanã riƙe sama dõmin kada ta fãɗi a kan ƙasa fãce da izninsa? Lalle ne Allah ga mutãne haƙĩƙa, Mai tausayi ne, Mai jin ƙai.
وَهُوَ ٱلَّذِىٓ أَحْيَاكُمْ ثُمَّ يُمِيتُكُمْ ثُمَّ يُحْيِيكُمْ ۗ إِنَّ ٱلْإِنسَـٰنَ لَكَفُورٌۭ
wahuwa alladhī aḥyākum thumma yumītukum thumma yuḥ'yīkum inna l-insāna lakafūrun
Kuma shĩ ne wanda Ya rãya ku, sa'an nan kuma Yanã matar da ku, sa'an nan kuma Yanã rãyar da ku. Lalle mutum, haƙĩƙa, mai kãfirci ne.
لِّكُلِّ أُمَّةٍۢ جَعَلْنَا مَنسَكًا هُمْ نَاسِكُوهُ ۖ فَلَا يُنَـٰزِعُنَّكَ فِى ٱلْأَمْرِ ۚ وَٱدْعُ إِلَىٰ رَبِّكَ ۖ إِنَّكَ لَعَلَىٰ هُدًۭى مُّسْتَقِيمٍۢ
likulli ummatin jaʿalnā mansakan hum nāsikūhu falā yunāziʿunnaka fī l-amri wa-ud'ʿu ilā rabbika innaka laʿalā hudan mus'taqīmin
Ga kõwace al'umma Mun sanya wurin yanka, su ne masu yin baiko gare Shi, sabõda haka, kada su yi maka jãyayya a cikin al'amarin (hadaya). Kuma ka yi kira zuwa ga Ubangijinka lalle kai kana a kan shiriya madaidaiciya.
وَإِن جَـٰدَلُوكَ فَقُلِ ٱللَّهُ أَعْلَمُ بِمَا تَعْمَلُونَ
wa-in jādalūka faquli l-lahu aʿlamu bimā taʿmalūna
Kuma idan sun yi maka jidãli, sai ka ce: "Allah ne Mafi sani game da abin da kuke aikatãwa."
ٱللَّهُ يَحْكُمُ بَيْنَكُمْ يَوْمَ ٱلْقِيَـٰمَةِ فِيمَا كُنتُمْ فِيهِ تَخْتَلِفُونَ
al-lahu yaḥkumu baynakum yawma l-qiyāmati fīmā kuntum fīhi takhtalifūna
"Allah ne zai yi hukunci a tsakãninku, a Rãnar ¡iyãma a cikin abin da kuka kasance a cikinsa kunã sãɓawa jũna."
أَلَمْ تَعْلَمْ أَنَّ ٱللَّهَ يَعْلَمُ مَا فِى ٱلسَّمَآءِ وَٱلْأَرْضِ ۗ إِنَّ ذَٰلِكَ فِى كِتَـٰبٍ ۚ إِنَّ ذَٰلِكَ عَلَى ٱللَّهِ يَسِيرٌۭ
alam taʿlam anna l-laha yaʿlamu mā fī l-samāi wal-arḍi inna dhālika fī kitābin inna dhālika ʿalā l-lahi yasīrun
Ashe, ba ka sani ba, lalle ne Allah Yanã sanin abin da yake a cikin sama da ƙasa? Lalle ne wancan yanã cikin Littafi lalle wancan ga Allah mai sauƙi ne.
وَيَعْبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ مَا لَمْ يُنَزِّلْ بِهِۦ سُلْطَـٰنًۭا وَمَا لَيْسَ لَهُم بِهِۦ عِلْمٌۭ ۗ وَمَا لِلظَّـٰلِمِينَ مِن نَّصِيرٍۢ
wayaʿbudūna min dūni l-lahi mā lam yunazzil bihi sul'ṭānan wamā laysa lahum bihi ʿil'mun wamā lilẓẓālimīna min naṣīrin
Kuma sunã bautãwa baicin Allah, abin da (Allah) bai saukar da wani dalili ba game da shi, kuma abin da bã su da wani ilmi game da shi, kuma bãbu wani mai taimako ga azzãlumai.
وَإِذَا تُتْلَىٰ عَلَيْهِمْ ءَايَـٰتُنَا بَيِّنَـٰتٍۢ تَعْرِفُ فِى وُجُوهِ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ ٱلْمُنكَرَ ۖ يَكَادُونَ يَسْطُونَ بِٱلَّذِينَ يَتْلُونَ عَلَيْهِمْ ءَايَـٰتِنَا ۗ قُلْ أَفَأُنَبِّئُكُم بِشَرٍّۢ مِّن ذَٰلِكُمُ ۗ ٱلنَّارُ وَعَدَهَا ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ ۖ وَبِئْسَ ٱلْمَصِيرُ
wa-idhā tut'lā ʿalayhim āyātunā bayyinātin taʿrifu fī wujūhi alladhīna kafarū l-munkara yakādūna yasṭūna bi-alladhīna yatlūna ʿalayhim āyātinā qul afa-unabbi-ukum bisharrin min dhālikumu l-nāru waʿadahā l-lahu alladhīna kafarū wabi'sa l-maṣīru
Kuma idan anã karanta ãyõyin Mu bayyanannu a kansu kanã sanin abin ƙyãma a cikin fuskõkin waɗanda suka kãfirta sunã kusa su yi danƙa ga waɗanda ke karãtun ayõyinMu a kansu. Ka ce: "Shin to in gaya muku abin da yake mafi sharri daga wannan? (Ita ce) Wuta." Allah Yã yi alkawarinta ga waɗanda suka kãfirta. Kuma makõmarsu ta mũnana.
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ ضُرِبَ مَثَلٌۭ فَٱسْتَمِعُوا۟ لَهُۥٓ ۚ إِنَّ ٱلَّذِينَ تَدْعُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ لَن يَخْلُقُوا۟ ذُبَابًۭا وَلَوِ ٱجْتَمَعُوا۟ لَهُۥ ۖ وَإِن يَسْلُبْهُمُ ٱلذُّبَابُ شَيْـًۭٔا لَّا يَسْتَنقِذُوهُ مِنْهُ ۚ ضَعُفَ ٱلطَّالِبُ وَٱلْمَطْلُوبُ
yāayyuhā l-nāsu ḍuriba mathalun fa-is'tamiʿū lahu inna alladhīna tadʿūna min dūni l-lahi lan yakhluqū dhubāban walawi ij'tamaʿū lahu wa-in yaslub'humu l-dhubābu shayan lā yastanqidhūhu min'hu ḍaʿufa l-ṭālibu wal-maṭlūbu
"Ya ku mutãne! An buga wani misãli, sai ku saurãra zuwa gare shi. Lalle ne waɗanda kuke kira baicin Allah, bã zã su halitta ƙudã ba, kõ da sun tãru gare shi, kuma idan ƙudãn ya ƙwãce musu wani abu, bã zã su kuɓutar da shi ba daga gare shi. Mai nẽma da wanda ake nẽman gare shi sun raunana."
مَا قَدَرُوا۟ ٱللَّهَ حَقَّ قَدْرِهِۦٓ ۗ إِنَّ ٱللَّهَ لَقَوِىٌّ عَزِيزٌ
mā qadarū l-laha ḥaqqa qadrihi inna l-laha laqawiyyun ʿazīzun
Ba su ƙaddara wa Allah hakkin girmanSa ba. Lalle ne Allah, haƙĩƙa, Mai ƙarfi ne, Mabuwãyi.
ٱللَّهُ يَصْطَفِى مِنَ ٱلْمَلَـٰٓئِكَةِ رُسُلًۭا وَمِنَ ٱلنَّاسِ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ سَمِيعٌۢ بَصِيرٌۭ
al-lahu yaṣṭafī mina l-malāikati rusulan wamina l-nāsi inna l-laha samīʿun baṣīrun
Allah nã zãɓen Manzanni daga malã'iku kuma daga mutãne.1 Lalle Allah, Mai ji ne, Mai gani.
يَعْلَمُ مَا بَيْنَ أَيْدِيهِمْ وَمَا خَلْفَهُمْ ۗ وَإِلَى ٱللَّهِ تُرْجَعُ ٱلْأُمُورُ
yaʿlamu mā bayna aydīhim wamā khalfahum wa-ilā l-lahi tur'jaʿu l-umūru
Yanã sanin abin da ke gaba gare su da abin da ke bãyansu, kuma zuwa ga Allah ake mayar da al'amura.
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ ٱرْكَعُوا۟ وَٱسْجُدُوا۟ وَٱعْبُدُوا۟ رَبَّكُمْ وَٱفْعَلُوا۟ ٱلْخَيْرَ لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ ۩
yāayyuhā alladhīna āmanū ir'kaʿū wa-us'judū wa-uʿ'budū rabbakum wa-if'ʿalū l-khayra laʿallakum tuf'liḥūna
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi rukũ'i, kuma ku yi sujada, kuma ku bauta wa Ubangijinku, kuma ku aikata alhẽri, tsammãninku, ku sami babban rabo.
وَجَـٰهِدُوا۟ فِى ٱللَّهِ حَقَّ جِهَادِهِۦ ۚ هُوَ ٱجْتَبَىٰكُمْ وَمَا جَعَلَ عَلَيْكُمْ فِى ٱلدِّينِ مِنْ حَرَجٍۢ ۚ مِّلَّةَ أَبِيكُمْ إِبْرَٰهِيمَ ۚ هُوَ سَمَّىٰكُمُ ٱلْمُسْلِمِينَ مِن قَبْلُ وَفِى هَـٰذَا لِيَكُونَ ٱلرَّسُولُ شَهِيدًا عَلَيْكُمْ وَتَكُونُوا۟ شُهَدَآءَ عَلَى ٱلنَّاسِ ۚ فَأَقِيمُوا۟ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتُوا۟ ٱلزَّكَوٰةَ وَٱعْتَصِمُوا۟ بِٱللَّهِ هُوَ مَوْلَىٰكُمْ ۖ فَنِعْمَ ٱلْمَوْلَىٰ وَنِعْمَ ٱلنَّصِيرُ
wajāhidū fī l-lahi ḥaqqa jihādihi huwa ij'tabākum wamā jaʿala ʿalaykum fī l-dīni min ḥarajin millata abīkum ib'rāhīma huwa sammākumu l-mus'limīna min qablu wafī hādhā liyakūna l-rasūlu shahīdan ʿalaykum watakūnū shuhadāa ʿalā l-nāsi fa-aqīmū l-ṣalata waātū l-zakata wa-iʿ'taṣimū bil-lahi huwa mawlākum faniʿ'ma l-mawlā waniʿ'ma l-naṣīru
Kuma ku yi jihãdi a cikin (al'amarin) Allah, hakkin JihãdinSa. shĩ ne Ya zãɓe ku alhãli kuwa bai sanya wani ƙunci1 ba a kanku a cikin addĩni. Bisa ƙudurcẽwar ubanku Ibrãhĩm, shĩ ne ya yi muku sũna Musulmi11 daga gabãnin haka. Kuma a cikin wannan (Littãfi ya yi muku sũna Musulmi), dõmin Manzo ya kasance mai shaida a kanku, kũ kuma ku kasancemãsu shaida a kan mutãne. Sabõda haka ku tsayar da salla kuma ku bãyar da zakka kuma ku amince da Allah, Shi ne Majiɓincinku. Sãbõda haka mãdalla da Shi Ya zama Majiɓinci, mãdalla da Shi ya zama Mai taimako.